Page Fifty Three

40 1 0
                                    

🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert* 💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Fifty  Three

***
Salim tunda yaji Gogode tayi maganar aurar da Rukayya yaji hankalinshi ya matukar tashi,abunda yakara tada Masa hankali kuma shine accepting maganar da Abbansu yayi. what was he thinking?why will agry to get Rukayya married at this very young age? It's unlike him,he really can't believe it. Inma kuma zai yarda din toh tabbas mahaifin nasa yanada wani kwawaran dalili akasa,dalilin da babu wanda yasanshi seshi shi kadai. Yaso idan kowa yabar gurin Abban nasu yaje yasameshi yaji ta bakinsa,yanason yatabbatar bawai haka kawai Abban yayarda da maganar Gogoden ba,yanason ya tabbatar cewa akwai wannan kwakwaran dalilin dayake da yakinin Abban nada shi anma se besamu kebewa da Abban nasaba har yasaka shi yaje yamayar da Gogode gida. Harsuka Isa Babban buli gabadaya hankalinshi baya jikinshi,tunanin za'a aurar da yarinya kamar Rukayya yadameshi,yazatayi Rayuwar aure? wazata aura? Is he worthy of having her? Karatun ta Kuma fah?danya tabbatar bazai wuce wani Dan Kauye Gogoden tanema ma Rukayyan ta auraba. Bashida wani buri ayanzu daya wuce yayi dropping Gogode yakoma gida. Rabi'u natayi mishi hira a mota ma baisan meyake cewaba dayake tare suka sake komawa Babban bulin. ahanyarsu na dawowa ne bayan sun shigo gari Rabi'un yace "Kai Mallam it seems you're not in the mood today,inata maka surutu bakamasan menake cewaba. Toh nidai kasaukeni agida kawai dan nasan dakyar insamu kanka komun koma tare ma"

Araunane Salim yace "I'm sorry Bro, gabadaya wani tunanine yashige min kai" Rabi'u yayi murmushi yace "Bakomai,just drop me off,I understand" haka yakai Rabi'un gida yanasake bashi hakuri kafin yawuce nasu gidan. Yana parking motarsa a garage bezarce ko'inaba se sashin Kawu Sani,besameshi a parlour ba anma yajiyo muryarsa dagacan dakin yana amsa sallamarsa. zama yayi anan parlourn har Kawu Sanin yafito daga daki yace "A'a harka dawo daga Babban bulin?" Ahankali Salim yace "Eh Abba" akan daya daga cikin kujerun parlourn Kawu Sani yazauna sannan yace "Toh sannu da dawowa,Badai wata matsala Koh?" Kawu Sani yayi maganar yana zubama Salim din idanu ganin kamar akwai abunda ke tafe dashi.

Salim yace "Abba daman akan maganar auren Rukayya ne. I'm just curious, miyasa ka goyi bayan Kakarta?" Murmushin dayafi kuka ciwo Kawu Sani yasaki sannan yace "toh yazanyi Salim? Because that's the only solution. Innace zanyi objecting maganar toh definitely zata tafi gurin kakanku a Giyade,intaje can kuma babu tantama ko aranar takeson a daura auren Rukayya dawannan yaron Baba Mallam bazaiyi wata wata ba zai amince da uzurinta because shima abunda yakeso kenan" Salim yace "toh kai Abba yazakayi handling situation din daka yarda da maganar?" Kawu Sani yace "I'l see the guy first kafin inyanke duk wani decision. abunda yasa nima amince din sabida banason ayiwa Rukayya zabin mijin dabai dace da'ita bane Salim" Salim dabai gane inda maganar mahaifin nasa yadosa gabadaya ba yace "kenan in yaron baiyi maka ba zakasan yanda zakayi kacanza maganar?" Girgizakai Kawu Sani yayi alamar a'a sannan yace "Hakan bazai taba yuyuwa ba,tunda Gogode tadauko maganar nan hankalinta bazai taba kwanciya ba setaga Rukayya a gidan mijinta. So in yaron baiyimin ba nizan nema ma Rukayya mijin danake da tabbacin zai kulada ita in aura Mata akan su suyi Mata zabi marar kyau" Salim baisan sanda yadago yakalli mahaifinnasaba.
Kawu Sani yayi murmushi yace "Yes son,that's the only solution and be rest assured nidin maizaba ma Rukayya miji nagari ne insha Allah" ahankali Salim yace "Allah yazabi abunda yafi alkhairi Abba" Kawu Sani yace "Amin" sannan yakarada "Thanks for caring for Rukayya son. It really means alot and it shows cewa ko bayan raina Rukayya bazata taba wulakanta ba sabida ahalina, at least I've you and Fahad dakuke kokarin son abunda nakeso,kuke kokarin cika min burina na rike amanar tilon Yar kanina" Salim yace "bakomai Abba, Rukayya ai kanwar muce yanda su Aisha suke agurin mu haka Itama muka dauketa" jinjinakai Kawu Sanin yayi cikeda Jin dadi sannan Salim yamasa sallama yatafi bayan Kawu Sanin yace su jirayi zuwan yaron ranar Saturday.

QADRWhere stories live. Discover now