Page Thirty Five

60 4 0
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Thirty Five

Najima tsaye Ina kuka kafin naja akwatina nakoma jikin wata bishiya dakenan gaban gate din makarantar na ajiye akwatin nahau kai nazauna narabza uban tagumi with the hope cewa may be Yaya Zunnurain yajuyo motarsa yadawo yadaukeni,may be tozarta kawai sukeson suyi shiyasa sukayimin haka. Inba haka ba wani marar imanin ne za'aturoshi daukan kannensa a makaranta yabar daya agurin Kuma bawai Dan ya manta ba.

Haka nacigaba dazaman jira inayi Ina leken takowani angle kozanga motar gidan Kawu Sani anma sede babu shi babu labarinsa gashi har anfara watsewa,tsirarrun student ne suka rage agurin Kuma Suma anata zuwa daya bayan daya ana daukarsu,gashi Naga Rana yafito kwatsa kwatsa da alama dai Sadiya tawuce sosai. Banida agoge inakuma so insan lokaci don innemi stand dina danhaka senatashi daga kan akwatina Dana zauna nakarasa can wurin wasu group din students dake zaune suna hirarrakin su na tambayesu kosuna da agogo. Senayi sa'a daya daga cikin su tanadashi,tambayar ta lokaci nayi inda tace min ai shabiyu da rabi ne lokacin. Zuciyana seda yabuga,shabiyu harda rabi,Awa na nawa anan kenan Ina jira? dan tun after nine aka sakemu daga assembly ground. daurewa nayi namusu godiya kafin nakoma kusa da kayana natsaya Ina tunanin abunyi. Ayanzu Kam nasan insu Yaya Zunnurain Basu Isa gida ba toh sauransu kiris. Wasu irin hawayene suka tahomin lokaci guda,niwana sani yanzu dazai taimakamin?

Take kuma se commercial car yafado min arai,nafara ayyanawa ko inbi commercial car ne? anma Sena tuna banida kudi,bankarbi kudina agurin Uncle Adam ba dukdama tun shekaranjiya ya kiramu duka kan zai raba mana yabamu namu ninaki karba. Nace Masa ya ajiyemin kawai se andawo hutu nacigaba da amfani dashi dankuwa alokacin gani nikeyi kudin bazaimin amfanin komai agidaba tunda bawani abun zance zansaya ba Kuma konace zansaya din ai sede inci aboye kowani abudai haka. Regret din rashin karban kudin seyahau kaina dankuwa dana karba dayanzu zaiyimin amfani.

Take kuma sewata zuciyar tashiga rayamin kode inje cikin makarantar induba office din Uncle Adam dinne inkarbi kudi yanzu may be inyi sa'ar samunshi. At first naji tsoron zuwa sabida kada yayi questioning dina dalilin dayasa aka tafi aka barni amma danaga banida wani mafita daya wuce wannan sekawai nayi deciding inje din. Harda akwatina nadauka nanufi cikin makarantar dashi dankuwa banason wahalar dawowa nan indai har nasamu nakarbi kudin tunda commercial cars dinda makaranta take kawowa acikin makaranta suke diban dalibai,masu gadi seda sukayimin tambayar dalilin dayasa zan mayar da kayana cikin makaranta sekawai nace musu staff quarters zankai.

Koda na'isa gaban admin block sebanga commercial car ko daya ba,duk sun tafi dajimawa. daman Naga sanda suke fita a gate din makarantar anma ai banyi tunanin duka suka tafiba. Anan gaban admin block na ajiye kayana sannan nashiga cikin admin block din nanufi office din uncle Adam Ina addu'ar Allah yasa insameshi inyaso Inna karbi kudin basai inhau napep intafi Tasha in hau motaba. Anma sede banyi sa'a ba dankuwa office dinma agarke take gabadaya gashi admin block dinma shiru duk yawanci malaman suntafi. Tashi hankalina yakumayi ayayinda nakoma gurin kayana,najima zaune gurin Ina ganin yanda ake zuwa daukan wasu dake cikin makarantar Basu fita gate ba sunajiran azo adaukesu harya rage saura Mutum biyu. Ananne tsoro yakara kamani,Sena fara tunanin insuka tafi suka barni anan akazo akasaceni fah? Kokuma in Allah yahadani da mugayen mutane fah? Dankuwa naji ance maza nayima Mata fyade most especially agurin da babu crowdness,agurin da kikayi ihu babu Mai taimakonka. Wannan tunanin danayi ne yasani tashi dasauri nadauki akwatina nanufi wurin masallaci. Acan tambayan masallaci inda baza'a ganni ba na ajiye akwatina sannan naje nadauro alwala nazo natada sallah sanin cewa azahar tawuce.

Koda na'idar da sallahn anan cikin masallacin nacigaba da zama Ina kuka na tareda neman dauki gurin Allah anma har la'asar tayi tawuce babu wanda yazo to my rescue. Infact makarantar tayi shiru sosai,sallah ma ba'a zuwa Yi a masallacin danake ciki dayake masallacim student ne se in sunanan ake Jam'i aciki ayayinda lokacin hutu Kuma malaman dake zama a staff quarter's sesukeyin sallarsu acan masallacin dake kusa da staff quarters din. Allah yataimakeni ma ba'akai ga rufe wannan masallacin ba anma nasan may be zuwa dare ko gobe dasafe zasu rufe danbazasu taba barinshi haka Kara zube ba.

QADRWhere stories live. Discover now