Page Thirty Six

51 1 0
                                    

🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert* 💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Thirty Six

Suna isa security office ɗin guard ɗin ya ƙarasa ciki yaɗauko akwatin daya ɗauka abakin masallacin yafito musu dashi. Fahad nagani yace "Shine! Akwatintane wallahi. A Ina kasamu?" dankuwa bai manta kalar akwatin ba tunsanda yakawo su ranar da akayi admitting ɗinsu a cikin makarantar.

Security Guard ɗin seyace "Acan kusa da masallacin hostel ɗin Mata nasamu a ajiye kusa da varendern masallacin. ni duk a tunani nama wata daga cikin Ɗaliban ne tamanta dayake wasu sukanyi misplacing kayansu ranar hutu kokuma sumanta shi inda mukuma inmuka gani semu ɗauko mu ajiyeshi agurin mu yanda in andawo masu shi sunzo sunyi claiming semu basu" Fahad yace "wannan kam akwatin Kanwata ce,muje muduba gurin may be musameta" jinjina kai sauran sukayi sannan suka nufi masallacin ayayinda security guard ɗinda ya tsinci kayan yake faɗin "Nidai banga alamar akwai Ɗaliba agurin ba" wani acikin su yace "kasani ko tana cikin masallacin? mujedai muduba anything can happen".

***
Zama na cigaba dayi anan cikin masallacin har aka fara kiraye kirayen sallar maghriba duk a kunnena. tashi nayi nafita daniyar yin alwala inzo inyi sallah,anan bakin tap na tsuguna na ɗaura alwalana,natashi kenan zankoma cikin masallacin senaji kamar motsin mutum. Hakan ba ƙaramin tsorata ni yayi ba,lungu nasamu na buya cikin sauri ayayinda zuciyana ke bugu,seda nadaina Jin foot steps ɗin dana dinga ji sannan nafito daga lungun dana buyan,nashiga leken hanyar dazanbi inshiga masallacin inda annanne nahango ɗaya daga cikin Security man ɗinmu ɗaukeda akwatina ya nufi security office dashi. zare idona nayi cikin sauri ayayinda nadaga kafana daniyar infito fili in tsaida shi ince mishi nawane anma take sewata zuciyar ta haneni dayin hakan dana tuna cewa "No one is to be trusted and Some Men take this kind of advantages suyi ruining rayuwar Ya'ya Mata,yanzu a tsakiyar makarantar nan da duhu yafarayi innace zanmishi magana yazo yamin wani abunfah? Wazai zo yayi rescuing dina? don haka sena hakura dayi masa maganar nayi sauri nashige masallaci Ina addu'ar Allah yasa baijuyo yaganni ba kokuma Allah yasa baiji karar rufe kofar masallacin danayiba dukdama i was very careful wurin rufewan.  I badly wanted my Box back sabida akwai abubuwa da dama dazan bukata aciki kafin gobe anma na gwammace in yita zama ahaka akan inbi bayanshi,na gwammace inzauna a duhu batareda nayi using lantern dinaba don ganin haske dankuwa babu hasken koda security light ne acikin makarantar kasancewar daman lokacin hutu yanke wutar akeyi harsai Ɗalibai sundawo sannan adawo musu dashi.

Gaba ɗaya a tsorace nayi sallan maghriba,inayi zuciya ta na bugawa hakanan inaji kamar security ɗin zaidawo yayimin wani abu,bayan na idar da sallah can dungun gini nakoma na rakube agurin kamar wata meshirin shiga ginin ayayinda zuciyana ke dukan uku uku. Nafi mintuna talatin acikin wannan fear ɗin,fear ɗinda bana tunanin zan iya mantashi a rayuwata. Surutun mutane danaji dakuma footsteps dana keji suna tahowa towards masallacin ne yasa nasake mugun tsorata,bugun zuciyana yakaru gashi kuma muryar maza nikeji,hawaye nafarayi babu kakkautawa ayayinda nake kokarin holding kukana dan kada yafito fili har su jini,addu'a kuwa babu wanda banyishi ba alokacin,harda na shiga banɗaki seda nadinga yi tsabar kidima.

Inaji sukazo kofar masallacin,senaji wani acikinsu na faɗin "Aikuwa ga takalmin ta nan" wani irin danasani ne yashigeni lokaci guda,Sena fara danasanin barin takalmina awaje. Cusa kaina nayi cikin cinyoyina dasauri ayayinda zuciyana kecigava da bugu,nikam nasan yau tawa yakare shine abunda nake ayyanawa araina ayayinda naji ambude kofar masallacin. Haska Torchlight ɗinda aka shigayi acikin masallacin takowani angle har ya iso kaina babu wanda hakan yasani ɗago da kaina daga cusashi danayi cikin cinyana.

Inaji suna faɗin gatacan,muryar Yaya Fahad danaji Yana faɗin "Rukayya" ne yasani ɗagowa dasauri cikeda mamaki and there I saw him coming towards me. Dasauri natashi Ina hawaye nakarasa inda yake nafaɗa jikinshi se kuka. Tsugunawa yayi agabana ya rungume ni dakyau yana shafa gadon bayana batareda ya iya ya ce komai ba.

QADRWhere stories live. Discover now