Page Forty Eight

50 3 0
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Forty Eight

Cemasa nayi "Toh" sannan mukayi sallama natafi gida. Koda na'isa gida babu wanda yanemi ba'asin rashin dawowana da wuri barema har inyi tunanin koda ace wataran zan bata za'asamu mai nuna min irin wannan gatan.

Tundaga ranar kullum naje Islamiya sena hadu da Yaya Sajeed mungaisa,either alokacin break kokuma kafin inshiga islamiyar sabida naki yarda ma  muna haduwa bayan antashi kasancewar Ina tsoron kada azo daukarmu aganni dashi ko kar garin tsayawa gaisawa dashi Yaya Zunnurain yatafi yabarni.
Daman Wednesday yakamata muyi resuming school anma sai Ummi taroka mana Kawu Sani kan mubari se Friday koh Saturday kawai mu koma dan ballallai damun koma din ace za'ana mana serious lesson ba. Dole se wata satin tazagayo kafin akoma normal activities fully,dayake yan rashin strictness din Kawu Sanin suna kusa seya yarda wanda wannan dalilin yasa muka cigaba dazuwa islamiyar dandama sauran daliban dasuke boarding suma duk se cikin weekend dinne zasu koma makarantar su sannan dayake gajeren hutune har Thursdays and Fridays ma zuwa islamiyar mukeyi.

Ranar Friday nayi rashin sa'a asirina yatonu. during break naje mungaisa da Yaya Sajeed yabani ledar chocolates da kayan makulashe munyi sallama kenan nafita daga motarsa daniyar tafiya idanuna suka sauka kan motar Yaya Salim dayake kokarin parking motarsa agurin. Yakawo wa Sule lunch box dinsa daya manta agida,zare idanuna nayi atsorace sannan najuya nashiga tafiya dasauri zuciyana tana dukan uku anma abanza dankuwa Yaya Salim already yaganni,cikin sauri yafito daga cikin motar ransa a matukar bace yana kwala kiran sunana.

Dole natsaya sabida tsoron kada attention din masu gadin islamiyar daketa cikin makarantar yadawo kanmu harsu fito suce zasu hukunta ni. Juyawa nayi Ina kallonsa anma memakon inga yanufoni senaga yanufi motar Yaya Sajeed,baiyi wata wata ba yabude motar yacakuma wuyan Yaya Sajeed din dakarfi. Seda yayi Jim sanda yaganshi hakanan anger dinsa yakaru. Yana huci yace "What were you doing in the car with my sister? Banace karabu da'ita ba?" Yaya Sajeed dayagama rudewa yashiga cewa "Calm down Salim! Calm down please. It's not what you're thinking" bamu ankara ba kawai seji mukayi Yaya Salim din yakaiwa Yaya Sajeed punch a fuska.

Yace "Dan ubanka it's not what I'm thinking kakecewa? Tambayarka nakeyi mekayiwa kanwata!! why on Earth will you ask her to come and meet you outside islamiya?" Sekuma yasaki Yaya Sajeed din yayo kaina rai bace,jinadingayi kamar insaki fitsari a wando because bantaba ganin wannan side din Yaya Salim dinba.

Fizgana yayi yajuya dani daniyar zuwa gun Yaya Sajeed din anma da mamakinsa seyaga harya shige mota yayi reverse. Sakina yayi yashiga yabisa da gudu yana kwala masa kira tareda auna masa duk zagin dayazo bakinsa anma dayake bazaka hada gudun mota dana Mutum ba tuni Yaya Sajeed din yabar gurin bakidaya. Seda yabace masa dagani sannan yajuyo yanamin wani irin kallon tuhuma,idanun sa gabadaya sun canza launi harya iso inda nake.

Strictly yace "Meya miki?" Kawai sejikina yacigaba da rawa nakasa furta komai. Cikin wata irin tsawa dahar seda jijiyoyin wuyar satatashi yace "ba tammbayar ki nakeyi ba Rukayya?meya miki?" bakina narawa cikin kuka nace "Allah Babu abunda yamin" Yaya Salim yace "meyakaiki cikin motarsa toh?" cikin firgici nace "gaisawa mukayi Allah" Yaya Salim yace "Anma menace miki ranar? Banace Kar insake ganinki tareda shiba?yama akayi yasan islamiyar dakike?" harlokacin jikina baibar rawa ba nashiga bashi labarin yanda yasan islamiyar mu dakuma taimakona dayayi ranar da Kare yabiyoni harnakai aya sekuma nafashe da kuka maisauti...

Nace "Wallahi Yaya Salim cewa yayi yanason yazama Yayana and nothing else" Rai bace Yaya Salim yace "Dan bakida hankali Yayun tsintar su ake akan titi? Duk yayundakike dasu basu ishekiba sekin jajubo wani?" Yafurzar da wani iska mai zafi yace "Rukayya miyasa wani sa'in kike abu kamar ba mai ilimi ba? why are you trusting people so easily? Kinsan halin wasu mazan kuwa? bama mazaba harda Matan ma you can't just meet someone and trust him out of blue for goodness sake!!!! inkika cigaba da yin hakan you'll only ruin your life....." Yayi maganar murya a raunane dayake nuna tsantsar damuwarsa akaina.

QADROnde histórias criam vida. Descubra agora