Suya(Tsire)

19 1 0
                                    


INGREDIENTS:
Nama, borkono, kuli-kuli, citta, kimba, kanunfari, masoro, thyme, curry, busashen tafarnuwa da sauran spices. Mangyada, gishiri, maggi sai tsinkin tsire.

PROCEDURE: Ki daka dukkanin spices naki tare da kuli, amma kulin ya ďan fi yawa, kuma ki sanya maggi da gishiri. A zabi nama mai kyau wanda babu kitse sosai a jiki, sai ki yanka shi sirara ta kwance da dan tsayi kadan sai ki ďauko tsinken tseren ki jera wannan naman a jiki. Wato in kin huda ta ciki sai ki fitar da shi ta waje.
Daga nan sai ki sami kwano ki zuba mangyada dai-dai misali tare da gishiri da maggi kaďan ki shafe jikin naman duka. Kina yi kina sanya shi cikin haďin kulin ya kama jikinsa da kyau. Daga nan in a oven ne sai ki yi ta jera su suna gasuwa. In ma a rushi ne duka ba damuwa.

Perfect Kitchen Recipe BookWhere stories live. Discover now