Peppered Chicken

18 1 0
                                    

Kayan hadi:-
•Kaza
•Attaruhu
•Koran tattasai
•Albasa
•Maggi/Gishiri
•Mai
•Citta
•Curry

YADDA AKE HADAWA
Dafa kaza da Maggi/Gishiri,citta, tafarnuwa da albasa.idan kazar ta dahu sauke ajiye gefe guda.
Zuba mai a kasko idan yayi zafi sai a soya wannan kazar amma kada ta soyu sosai,idan angama kara zuba mai dan kadan a kasko,zuba albasa idan tayi laushi, zuba attaruhu idan ya dan soyu, sai a juye wannan kazar ana juyawa zuba ruwan dahuwar kazar da Koran tattasai,curry ci gaba da juyawa zuwa dan mintina,sauke idan ruwan  ya dan tsotse.

Perfect Kitchen Recipe BookWhere stories live. Discover now