Sinasir

39 4 0
                                    


Abubuwan hadawa

Shinkafar tuwo kofi biyu
Daffafiyar shinkafa ludayi biyu
Suga
Baking powder cokali biyu
Yeast rabin cokali
Kindirmo rabin cup

Yadda ake hadawa
Ki wanke shikafarki ta tuwo kijikata kamar akalla awa shida.

Sai ki tsame daga ruwan, ki kawo dafaffiyar shinkafa ludayi biyu ki zuba, bi ma'ana ko wani kofi daya ludayi daya za ki sa na shinkafa dafaffiya. A kai a niqa a kawo.

Sai ki sa yeast da kindirmo, da suga, ki juye ko ina yaji. Sai ki kai kullin rana ki ajiye kokuma wuri mai dumi.

Ki jira har sai ya taso sannan ki sa baking powder ko kanwa ki juya sosai.

Ki sami kaskon suyanki, ki rika zuba mai kadan-kadan, ki na zuba kullin da ludayi, ki rufe da murfi kar ki cika wuta ki bari har sai ya gasu.  Shi ba a juyawa kamar yadda ake juya qwai. In ki ka rufe ki ka sa wutan dai dai za ki ga ya yi dai dai. Sannan za ki ga ya yi huji huji huji. ‘Yar uwa wannan shine sinasir.

Perfect Kitchen Recipe BookWhere stories live. Discover now