KHAIRAT-21

1.5K 76 24
                                    

A daren haka suka fito neman kaza a yanda ya ce ama dama yunwa suke ji dan khairat kam tun abincin da taci kafin yan kawo amarya su tafi tun shi bata kai ruwa bakin ta ba. Driving yake a hankali bin wakar da ke playing a motar yake jikin shi na bashi kallon shi take, da gefen ido ya jiwo ya kalleta sanan yace koh in juyo ne gaba ki daya yanda zaki ji dadin kallo na, maida kallon ta tayi daya side din shi kuma ya riko hannun ta daya yana shafawa a hankali yace seriously this is not the khairat I proposed to and i got married to another khairat that is entirely different from the other haba mana babe pls talk to me kinsan kwa yanda zuciya ta ke zumudin taji kin yi magana pls where did you leave my fun loving and talkative khairat inje in dauko abuna, wait what did you just say am I a talkative ta tambaya tana kallon shi, yauwa yanzu na san ke din ce dai khairee na, parking yayi a wani wurin joint yayi horn da gudu wani ya karaso yana sannu oga, kaza muke so yace guda nawa, kamar 20 yayi koh khairee ido ta bude tana kallon shi sanan tace ama kai kadai zaka cinye 20 koh, noo ke zaki ci 19 ni kuma 1 so nake kiyi kiba kafin gobe, wanda ya karaso karban order yayi dan gyaran murya sanan yace ashirin din za a kawo, murmushi Mubarak yayi sanan yace 10 zaka kawo biyu kasa a leda daban sauran Kuma ka hada wuri daya' bayan minti da basu fi goma Sha biyar ba aka kawo musu ya bude kofar baya ya ajiye ledojin, suka wuce wani mini market suka tsaya shi kadai ya shiga ya barta a mota tabi bayan shi da kallo drinks da yogurt ya siyo da yawa har tana mamaki duk ina zasu kai wanan killa na sati ne koh wata ta fada a zuciyar ta 'sorry I left you alone' no problem ta fada, motar ya tada suka tafi bai tsaya ko Ina ba sai kofar wani gida yayi horn mai gadi har zai bude ya kara horn ya mai alama da hannu yazo, fita yayi daga motar ya dauki rabin abunda suka siyo yace ya kai cikin gida wurin su umma sanan ya dawo suka wuce nasu gidan.

Bayan dawo war su gida kofar da dazun ta gwada bude wa nan taga ya sa key yace mata bara nayi wanka nazo, yafi more than 30 minutes yana wanka ( ni dai nace wankan baki asarar sabula mai yake wanke wa har ya fi tabin awa ). Towel daure a kugun shi ya fito ya bude wardrobe ya dauko wata farar jallabiya ya sa, inda yake ajiye perfumes dinshi ya tsaya yana kallo yana tunanin wanne zai fesa sai da ya shin shina ko wanane sanan ya dauko creed aventus ' ahh this will do for the night.mubarak irin jovial mutanen ne da basu da matsala shiyasa da kowa ma yana shiri, amma in ka ganshi a cikin uniform dinshi zaka rantse bai taba dariya ba balle murmushi, captain Mubarak kenan.

Har ya zo fita ya tuna wani abu ya dawo ya dauka yana dariyar mugunta ' I'm going to make you talk kairi'

Daga ita sai towel ta fito ta tsaya gaban wodrobe zata dauko night gown dinta ya fado dakin sanye da farar jallabiya da white mask wani irin ihu ta saki tana neman shiga cikin wardrobe din, shima ihun yayi sanan ya kamo ta suka fada kan gado, dariya ya fara saboda yanda ya ga tsantar tsoro a fuskar, ' haba kina matar captain ama kin jin tsoro' bige shi tayi tana kokarin tashi, kara rike ta yayi yanda ko motsi ta kasa, jikin ta ta kalla ta ga daka ita sai towel tace em em bara na sa kaya, no I like it this way yace yana kallon cikin idon ta a hankali ya fara kissing dinta...... Asuba ta gari mukhair.

Bayan kwana biyu.....

Kusan kullum sai sunje chan cikin gidan su dan yanda mubarak ke san yan uwan shi itama sai take taya shi sonsu kuma har ga Allah suma suna son ta saboda koh sau daya basu taba nuna mata ban banci ba harta umma da ba son auren take ba ta hakura balle yanda taga khairat din na mata lada bi da biyayya, ya wanci tun safe suke xuwa gidan sai dare zasu dawo nasu gidan. Kamar kullum yau ma suna gidan sai ga hajiya ma an kawo ta,oyo yo suka mata sanan suka gaishe ta bayan ta amsa, ta kalli khairat tace kishiya ta kamar har yau baki gama sakewa ba, murmushi ta dan yi ' kar ki damu nasan mai zanyi ki daina jin kunyar mu, nabila akwai wasu food warmers din dana zo dasu karaso min dasu nan. Tuwon ne da miyar kubewa ne a cikin food warmers din da aka bude miyar kubewar kwa kada duka aka mata ga taji nama tunda aka bude kamashi ko ina ( better soup na money kill am ), ni na dafa abincin nan da kike gani da kaina ba dan kowa nayi shi ba sai dan ke da mai gida na, hajiya banda mu khadija ta tambaya ' wa ke ta ku ai ku kun tsufa, wani wasa za ayi tsakanin ango da amarya ' nabila mai ma kuke Kiran abun da turanci, competition nabila tace ' yes competition haka shi nake nufi, salim je ka kitchen ka dauko min babbar roba kaga.

Yauwa, tuwo ta dauko malmala hudu tasa a robar tace toh ango da amarya wanan shine, yama akace cewa em competition dinku, wanda yafi ci shine winner sanan amarya zaki fadi abubuwan da nayi amfani na dafa kuma da wanne irin tuwo ne kai kuma ango bayan ta gama lissafawa zaka fadamin yanda ake girka wa.

Bismillah.....

Hajiya ai kin hada su da aiki taya mubarak zai fada miki yanda ake girki mutumin da arayuwar shi nake ji koh ruwan zafi bai taba dafa wa ba balle ya fada miki yanda ake tuwo da miyar kuka ya Maryam ta fada bayan ta zauna gefen hajiya, ke dai ki min shiru ki gani....

Amma hajiya tuwon ya mana yawa koh zamu iya rage wa mu bar malmala daya, khairat ta tambaya ' a'a ba maganar ragi sai dai kari hajiya ta fada ' khairee let's prove them wrong we can do this. Hannu suka sa har sun fara ci khairat ta dan tabo shi ' barik ka manta bakayi bismillah ' oh thank you, da ker ta iya cinye malmala daya, dai dai yanda zai ji tace wlh na koshi in har na kara amai zanyi, kina cin miyar yanda ba mai gane wa daga nan zaki gane ingredients din da ta yi amfani dashi, kai ta dan daga taga hira ma suke a hankali ta ce mai ka iya yanda ake dafa wa, ba ki ji mai ya Maryam tace ba koh ruwa ban iya dafawa ba well sorry to disappoint you love ama ban iya ba, ohk we need to win let's confuse your grandma she can't pick a winner, wait my grandma or our grandma ' oh sorry hajiyar mu, kasan ya za ayi let me type it on my fone then I will forward it to you sai ka karanta while eating dan kar su gane ' yeah nice idea. Yanda ake tuwo ta rubuta mai sanan ta yi na miyar kubewa ta tura mai as text message sanan ta cigaba kamar tana cin tuwon koh ince shan miya, ya naga kamar bakya ci khairat ' a'a hajiya inaci,

Da ker suka samu suka cinye koh in ce mubarak ya cinye dan ita khairat malmala daya taci sauran shi ya cinye.
Hajiya let's move to the next round, I just want to see if bro is going to be the winner or Yaya amarya, nabila ta fada tana dariyar mugunta. Toh khairat fara lissafo mana abinda nayi amfani dashi wurin hada miyar nan hajiya ta fada tana kallon khairat, dan ajiyar zuciya tayi sanan tace kin san attarugu, red oil, crayfish, iru ( daddawar yarbawa ), tomato, girlic, shitta khairat ta fada ' shikenan koh da saura, shiru ta dan yi sanan tace na manta kubewar kanta da nama' dariya duk sukayi 🤣 😂 sanan umma tace baki fada mana wanne irin nama bane, tunani take wanne irin nama ne saboda da laushi kuma da zaki tabbas wannan ba naman saniya bane, nake ji naman rago ne, dariya suka suka ce kike ji baki tabbatar ba kenan, na rago ne ta fada am sure of it. Sai tuwon Kuma wanne iri ne, tace na dawa ne.

An gama dake sauran mai gidan nawa......



KHAIRAT Where stories live. Discover now