KHAIRAT -17

3.5K 368 42
                                    

Wurin amarya kwa gida ya gama ciki da yan uwa da abokan arziki
Kyan da khairat tayi tun kafin amata makeup ma kenan dan falmata ta iya gyara jiki , kowa sai ya ba yanda ta gyara amarya take
Kawayen ta sai tsokanar ta suke wacce bata son sojoji ta kare da auren soja, nabila na gefen ta ko ina suna tare , ba wani events zasuyi ba saboda sunce albarka suke nema ba hayaniya ba

Ranar kunshi/kamu

Kar ku so kuga khairat masha allah tayi kyau , a silver sand aka shirya yin komai in kunga yanda aka gyara wurin tsayawa fadan yanda gurin yayi kyau bata lokaci ne...

Karfe hudu na rana wuri ya ciki ana jiran isowar amarya  , sauti kurum ke tashi a cikin hall din, nusaiba na hango sai shiga da fice take gown dinta kurum ya tafi da hankali na..

Mc ce ta fara bayani a shirya ga amarya nan shigo wa nan kowa ya shirya ,wakar ado gawanja kujerar tsakar gida aka sa a hankali amarya da take ta ko wa a hankali take tafiya kamar bata son taka kasa ga mama ta riku hanun ta fuskar ta a rufe nan aka hau tafi amarya da mahaifiyar ta sun iso masha allah sunyi kyau khairat sanyi da light brown asoebi wanda asoebiafrica ta mata mama kuma ta sa green asoebi sanan bayan su kawayen amarya su siyama da nabila wacce yanzu ita ma ta zama Kawar amarya duk kansu sanye da brown and golden atampa gaskiya sai kunga yanda shigowar su tayi kyau

Tun kafin amarya ta karasa wurin zamanta mutane suka zagaye ta sai lika mata kudi aka ga kawayen mama ma sun taso dan goyawa yar su baya

Sai da Mc tayi ta dan allah abar amarya ta zauna tukun ga yan paparazzi sai daukan hoto suke nima nace bara dai in daukar muku

Sai da Mc tayi ta dan allah abar amarya ta zauna tukun ga yan paparazzi sai daukan hoto suke nima nace bara dai in daukar muku

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Daker aka samu suka bar amarya ta wuce wurin da aka tana da mata dan ta zauna gefen ta kuma kawayen ta ne zaune...

Yanzu dai muna jiran dangin ango da ango su iso kafin su zo bara a bude taro da addua aunty hussaina aka ba mic ta yi addua kawo ya amsa da ameen..

Wai ina dangin ango suke ne amarya mu na jira fa..

Tunda muna jiran su bara muje wurin iyayen amarya su mana nasiha

Aunty sadiya wacce ke zaune kusa da mama mc ta mai ka mata mic tace yarki na jiran nasihar ki ni dai nace ba yarta kurum ba muma ma karu da wani abun

Amarya ni dai abinda zance miki na farko shine hakuri hakuri hakuri ina ba hakuri ba za ki iya zaman gidan miji ba yata kiyi hakuri da duk wani abinda zaki fuskanta kowa kika gani a wurin nan hakuri yake a gidan auren shi...

Abu na biyu ba ruwan ki da wayar shi in dai kina sin kwanciyar hankalin ki kin dai san matsalar waya sanan ki zama mai kawaici

Nan kowa ya fara dariya

Mc tace hajiya Mun gode bara mu kara gaba wa zamu ba wa

Ga babbar auntyn mu , aunty amarya na bukatar shawarar ki , gaskiya khairat bansan abinda zance miki ba saboda abubuwan suna da yawa , aunty ki fadi ko da kadan ne

KHAIRAT Where stories live. Discover now