KHAIRAT -13

3.5K 265 17
                                    

3:00am.....

Sai ihun Jama'a ku taimake mu yake , ramla zauna tanan kar ki tashi bara naga in zan iya samun taimako a dare nan, shiru ba wanda ya fito sai daga baya suka fara isowa domin kawo agaji tundaga nesa suke ganin hayaki ,gidan su malam ya kama da wuta , nan suka fara kawo agaji dan daker suka samu ruwa dan rijiyar da ake samo ruwan nada nisa wasu nasa ruwa sauran kuma nasa kasa...

Daker aka samu wutar ta daina ci sai dai gobarar tayi bar na dan ba abinda malam da ramla suka fitar daga gidan sanadiyar komai ya kone kayan jikin su kurum suka tsira dashi...

Nasan zaku so sanin ya akayi gidan ya kama da wuta...🙄🙄

Karfe biyu da rabi nayi inna ta tashi indo ki tashi lokaci yayi

Ba shiri indo ta tashi,tasa kayanta suka fito ko tsoron dare basu yi ba .

Da fetur da ashana suka taho dan tun rana suka siya dan ma kar da daddare su rasa..

Suna isowa gidan suka shigo yanda inna da indo ke tafiya kwace barayi ne , ni dai kallon su nake ina tunanin to mai zai faru..

Nan naga indo ta fara watsa wa gidan fetur din hannun ta ita kwa inna abu ta samu ta toshe kofar dasu malam zasu iya fitowa tayi sanan suna fitowa bakin kofar inna ta kare ma gidan kallo sanan tace malam sai mun hadu a lahira sanan in kaje can ma ka kalli matan aljanna ka ga...

Inna mai kike tunanin kyasta ashanar mu , addu'a nake ma malam kinsan hakki nane ina matar shi , har da dan gun tun hawayen ta san nan tace allah ya jikan ka da rahma masoyina na asali ba wanda akamin kwace ba...

Nan ta kyasta ashanar suka wuce

Baza mu kwana a garin nan ba , dan haka mu fara takawa da kafar mu zuwa wani kauyen dan ni bazan iya barci yanzu ba inna tace..

Sai hakuri inna ba ke kadai wanan mutuwar ta shafa ba kar ki manta mahaifina ne nan ta fashe da kuka shikenan mun zama marayu..

Suna tafi ko gajiya babu har allah ya
Hada su da wani bawan allah yana tuka babbar motar sa , nan indo tayi saurin tsayar dashi ,har ya wuce sai kuma yaga bai kamata nan ya tsaya har suka karaso

Ina zuwa a daren , rimi indo tace , ku shigo zan ajiye ku dan zan wace ta garin

Mun gode dan nan allah ya saka da alkairi. ...

Inda gari ya waye har sun iso rimi
Nan suka mai godiya suka kara sa gida...

A tsakar gida suka zauna rukaiya datake autar inna wacce bata fi shekara goma a duniya ba amma sai wayo da hankali dan batayi halin inna halimare ba...tafito daga daki

Inna ina kika shiga kwana biyu kuma ni nasan bakiyi mana sallama ba kin bar mu mukadai

Auta wlh rasuwa aka mana acan kauye shiyasa kika ga mun tafi ba shiri
Allah sarki allah ya jikin mai rai

Ta dai fada ne dan bata yarda da inna da indo ba inna wacce ta manta da dangin ta a rayuwar ta itace zata ce an musu rasuwa..

Inna waya rasu , auta kin fara tambayoyin ki ko , samo mana abincin dan kafurar muke ji...

Auta bata gama karaso wa da abinci ba malam ya shigo

Inna da indo basu san yanda suka mike ba suna salati nan jikin inna ya fara karkarwa rasa mai zata ce ma tayi

Malam ka da..
Bata karasa ba taga shigowar abunda taki gani a duniya

Mai ka kawo min gidana malama mai nake gani

Gidanki ko gidana...
Bismillah ramla

Auta kaita dakin dake kusa da nawa

Kai kurum auta ta daga alamar toh ďan ita abun ya daure mata kai..

Wayece wanan matar da take gani

Har daki ta kai ta sanan ta debo ruwan sha ta ba dan taga alamar a gajiye take

Agurguje fans...

Tun bayan dawowar ramla da malam rimi , ramla bata samu kwanciyar hankali ba gidan ya bata zafi koh tsakar gida bata fita sai in malam na nan in baya nan kwa tana daki auta ce kurum ke tayata hira dan jinnin su ya hadu dana ta kullum sai ta mata aduar allah ya sauke ta lfy ta samu kani ko kanwa a daina ce mata auta..

Bayan wata biyu ramla ta haifi dan ta mai rai da lfy inda ran suna yaro yaci sunan mukhtar

Ba abinda ya raba malam da mukhtar wurin kama

Wani abun mamaki tunda ramla ta haihu inna bata leko tace bata ko sannu ba

Ranar dai ramla ta sa auta kaima inna yaron ta sa mai albarka ka zo kuga matsifa wurin halimare, ke fitar min da yaron nan daga nan , auta ta bata rai tace inna kanina ne fa mukhtar, sannu mai kani da yake akanki akafara ko tun kafin in bata miki rai fitar min dashi...

Haka rayuwa ya cigaba wurin su ramla ina da take jin dadin abun rukaiya na taya ta raino dan wani sa in a dakin take kwana wai baza ta rabu da kanin ta ba dan yanda take son shi ko yayyan bata musu wanan son dan ashirye take tayi yaki da duk wanda zai taba dan kanin ta

Wanan kenan....
Ranar da mukhtar ya cika shekara daya da sati, ramla ta hadu da bugun zuciya da bai yi ko minute talatin ba tace ga garin ku...

Malam da auta ne kurum rasuwa ya shafa in kaga rukaiya kace inna halimare ce ta mutu , tana kuka tana tausayin mukhtar....

Bayan shekara bakwai...
Muktar ya soma girma a yanzu kuma ya fahimta cewa inna halimare ba itace mahaifiyar shi ba dan tun bayan rasuwar ramla ba irin azabar da bata bashi abinci ma sai in an ba auta rabonta shine yake samu yaci...

Yanzu ya shiga cikin wani kuncin rayuwa dan rukaiya tayi aure ga allah ya dau ran malam...

Ko da akazo rabon gado inna cewa tayi wai ba dan malam bane da rukaiya taga za a cuce shi nan tasa baki aka raba gado dashi ina ya fisu komai

Bayan masu rabon gado sun wuce inna tace wa rukaiya ta tattaro duk wani abinda tasan an bashi da tazo kawo gardama nan tace zata tsine mata....

Haka rayuwa tacigaba da yiwa muktar da ci bai da wani gata sai in yaje gidan rukaiya nan zata yi ta bashi hakuri tace mai komai mai wuce wa watarana sai lbr...

Inda ya kai shekara goma shadaya nan ya fara zuwa kasuwa daukan kaya har watarana allah ya hada shi da sanusi

Yaro ya kamata ace kana makaranta
Ko baka son karatu

Nan hawaye yafa zubowa mukhtar ya fara kuka ya ce ina so inyi karatu sai dai banda kudin biyan makaranta aikin nan da nake ina kawai yayata kudin ne tana tara min dan in samu inyi karatu

Sosai ya ba sanusi tausayi , ya kalli muktar wanda hawaye ke kwance kan fuskar shi yace za ka zama dana...

Da sauri muktar ya fara jan baya dan ya saba ji an cewa musu dauke yara na yawo a garin kar aje shima wanan wayo yake so ya mai ya tafi dashi...

Da sanusi ya lura da haka sai yace ba cutar dakai zanyi ba muktar illa taimakon ka dana ke so nayi.

Masu cewa ina ja musu rai sai dai kuyi hakuri dani saboda ba laifi na bane

Banga ana voting da commenting ba shiyasa ban updating


Rema kay 💋

KHAIRAT Where stories live. Discover now