KHAIRAT -4

4.4K 193 6
                                    

                               

Hajiya baza ki iya zuwa kaduna ba tafiyar ta miki ni sa , ba neman shawar ka nake ba cewa nayi ka shirya karfe goma zamu bi jirgi dan har na mana booking tickets zuwa kd....

Khairat da yan uwanta na parlour mama sun hira sai dariya suke dan ashanty ma tazo ganin gida nusaiba na basu lbrn yanda aka biyo su ita da kawayen ta tsabar dariyar mugunta khairat harda hawaye, nussy kwa sai cewa take sis it's not funny iswear dan killa da kece a wurin sai kin suma, allah dai ya kiyaye inji mama, wai khairat har yanzu baki fito da manemi ba dan ni wlh nagaji so nake inga kurum anyi biki a gidan nan cewar ashanty. Ina handsome din nan da kike ban lbr inji nussy, wanne irin handsome ki kiyaye ni nusaiba...ana so ana kaiwa kasuwa mama ta fadi, ban ma fada miki ba rannan har gidan nan yazo bayan kin koma skul wurin alhaji...zaro ido tayi ta kasa magana dan ita bata ma san da zuwan shi gida ba a ina ma yasan gidan su. Ashanty na dariya tace mama kice har baba ya bashi, munafuka kila ma ita ta iko shi?? Nan fa khairat ta fara kuka wlh ita bata san da zuwan shi dan ko maganar kirki bai taba hada su ba. Mai abun kuka kin samu miji ya kawo kan shi har gida inji mama...
Ki kwantar da hankali ki bashi dama kigani, mama nifa bansan ma inda zan ganshi ba saboda baiwai na san shi ba kuma ko contact dinshi bani da....kin kore shi khairat kinji dadi shikenan sai kiyi ta zama tunda dama ba auren kike so ba, mama ta mike ta fita bayan ta gama magana. Khairat tayi shiru ta rasa mai ke mata dadi daki ta wuce ta kwanta kan gado tana ta tinani har barci ya dauke ta.

Washegari da safe nusaiba na kitchen tana hada musu breakfast dan in suna gida mama bata aikin komai suke shiyasa ba abinda basu iya ba daga gyaran gida zuwa girkin duk sun iya mama bata da wata matsala da ya wuce su samo zaman lfy a gidan miji da samun miji nagari adduar ta kenan kullum tana gode wa allah ashanty tayi sa'a sauran khairat da nusaiba....

Sani abacha international airport

Hajiya da mubarak na isowa ba afi minutes 10 ba jirgin su ya daga zuwa kaduna, in mun isa sai ka nema mana tickets din koma wa around 4, allah yasa dai mu samu, ameen....
12 daidai su hajiya suka iso kaduna international airport sai addua take allah ya basu sa'ar tafiyar nan da sukayi,mubarak ya kira wani abokin shi yana cemai ya turo mai motor airport yanzu kafin suje suga in zasu samu tickets din koma wa a yau.

Ba yanda basu yi ba ama akace musu ba jirgin da zai koma yau gombe haka suka hakura.
Daidai fitowar su motar na iso wa ya aiko driver shi
Tafiyar minutes 30 suka yi sai gasu a gaban gidan su khairat, zuciyar mubarak sai bugawa take anya hajiya zamu shiga kwa , ai in kaga ban shiga ba toh mutuwa nayi , driver yi horn  mu shiga tace. Nan da nan maigadi ya bude musu.

Khairat, nusaiba da usman suna buga scrabble sai musu ake khairat na wlh kayi cheating, suka ji horn....
Hajiya na fitowa daga motar tacewa Maigadi dan allah nuna min wurin hajiyar gidan, toh bara na mata magana, hajiya ta juya taga bai ma da alamar fitowa daga motar sai bata mai magana ba... malam hamisu ya dawo tare da asabe mai aikin su tana sannu da zuwa muje, wani babban falo takai hajiya tace mama na zuwa, sai ga mama tashigo ta tsaya tana kallon matar da killa shekarun ta sukai 50 tama kasa ganewa dan karamin jiki gare ta irin na fulani wanda tsufan su bai nunawa tama kasa ganeta dan ita bata santa ba , hijiya na juyo wa suka hada ido da fara'arta ta karaso tana sannu da zuwa sai ga asabe ta dawo dauke da drinks da snacks ta ajiye gaban hajiya, ta danyi murmushi tace nagode. Ina wuni mama ta gaishe ta , lfy mun same ku lfy bayan dan gaishe gaishe sai dukan su sukayi shiru, hajiya ta katse shirun tace daga gombe nake nazo wurin ku bara ne... mama ta kalle ta da mamaki a zuciyar ta tace baran me dan dai tasan hajiya nacikin jin dadin rayuwa tun daga kayan jikin ta zaka shaida hakan...ta katse wa mama tunani nazo nemawa dana jika na auren yarki khairat insha allah zamu rike muku yar ku tsakani da allah bazata samu matsala da mu ba...sai bayani take mama na jinta can sai mama tace naji bayanin ki sai dai bani zan bada khairat ba mahaifin ta ke da ikon wanan kuma baya nan yayi tafiya sanan banji ta bakin khairat ba ko taso inhar tana so to baku da matsala dan har ga allah na amince dake ace tun daga gombe kika zo garin nan, ba ma haka ba shi yaron a ina yasan khairat, nan hajiya ta bata lbrn mubarak tun daga huduwar shi da khairat da zuwa gurin mahaifin ta. Na gane shi kuma na yadda yana son khairat dan da wani ne bazai dawo ba balle har ya turo...yanzu ma dashi muke yana waje. A'a toh bara a kira khairat din su gaisa koh, hajiya tace toh kuma taji dadi da yanda mama ta karbe ta...
Mama tashigo ta tadda khairat suna game tace ki tashi ki shirya mubarak yana waje yana jiran ki, nifa ba inda zanje dan ba nina ce mai yazo. Dan ubanki ba rokon ki nake kije ba umarni nake baki dan haka maza ki tashi kije yana jiran ki dan yau da mahaifiyar shi yazo ma (nace mama kakar sace😆) khairat ta mike ranta a bace maiyasa mutumin nan keson  takura wa rayuwarta😠😠

Tun bayan fitar hajiya yana motor yana waya da yan wurin aikin shi sai yaji alamar mutum na tsaye a bayan shi dan baiga fitowar ta daga cikin gida tana sanye da hijab har kasa nan yace wa wanda suke waya tare " I'll call back later " ya fito daga motar yan mata mayan gari yana ta murmushi burin shi baiwuce ya ganshi tare da khairat
Tana tsaye ama bata amsa shi ba dan ranta a bace yake ta dan yi kokari ta bude siririn bakin tace ina wuni dan bata so ta wulakantashi tunda har gida yazo
Lfy kin wuni lfy yan mata na
Kamar baza tayi magana can tace lfy,
Kin ganni da naci ko kiyi hakuri zuciya ta baza ta iya rabuwa dake ba khairat tun randa na fara ganin ki nasan na samu matar aure wacce zata zame min uwar yayyana farin cikina in allah ya yadda neman amincewar ki kurum nake so ki amsa soyyaya ta insha allah baza kiyi dana sani ba.
Kalamai masu dadi yayi ta furta mata nan ta neme fushin da take ta rasa...
Na dame ki da surutu ko kiyi hakuri gimbiya ama baki ce min komai..
Hmm banda abin cewa ne
Kice kin amince da ni
Kai kurum ta daga mai, dan bata ga laifin mubarak ba..
Murna a zuciyar shi bata misaltuwa yace "thank you gimbiya khairat "
Nan sukayi ta hira ita dashi abin ban sha'awa har khairat taji bata son rabuwa dashi dan zuciyar ta takamu da son shi...
Yaushe zaka koma skul take tambayar shi
Wanne skul yace mata, oh kin zata a makarantar ku nake no well i didn't even tell u my full name en u ddnt bother to ask, sorry tace so was the name..
Engr Muhammad habib kuma contract din solar panels ne ya kaini skul din ku har na ganki but kar ki damu zan fada miki sauran lbr na in munyi waya hope dai yanzu zakina picking.
Tace yes
Ga hajiya nan ma ta fito zamu wuce yana fadan haka sai taji ba dadi zai tafi. Ta dan sunkuyar da kai kasa ta gaishe da hajiya,
Dariya hajiya tayi wanan ce kishirya ta wa da tasa uwar gida tasowa neman wa mijin ta aure duk sukayi dariya masha allah, mama tace na zata mahaifiyar shi ai.... la dan dai ban tsufa shiyasa kika ce haka
Mubarak ya juyo gun mama ya gaisheta nan ya burge mama taji ya kwanta mata rai
Mun gode inji hajiya alhairin allah ya kara hada mu ta fada tana bude motar...
Yayiwa masoyiyar shi sallama yace sai munyi wa, allah ya kiyaye hanya tace.
Ya shiga motar driver yaja suka bar gidan....
Hajiya ina mukayi tunda bamu samu jirgin komawa ba

Abuja mukayi tace....

Votes 👇
Comments 🖎                                           

                                             Rema kay💋

KHAIRAT Where stories live. Discover now