KHAIRAT -12

3.3K 213 7
                                    

Masoyan KHAIRAT kumin affuwa na muke laifi na rashin updating...
Amma kumin uziri ina garin su khairat dan jiyo muku yanda ta ke sai dai tunda naje banda network📵📵

Am dedicating this chapter to you all my fans 👭👬👫 godiya duba na voting 👇👇

Yanzu inna anan zamu kwanta, toh dan ubanki ina zamuje ko akwai wanda kika sani ne a garin , kinga fa bera da kenkeso kamar bayan gida,ko maciji ne ba ruwana indai zan samu makafa...

Washegari da safe har zasu wuce tasha indo tace inna mai zai hana mu kara duba wanan hanyar ko zamu ga malam

Kuma fa kinyi tina ni..

Malam na kan hanyar dawo wa daga wurin mai kosai dan su samu suyi karin kumallo da koko da kosai,...

Daidai da zai shiga gida su halimare suka hango shi , ke indo duba min wancan ba malam bane , kwarai kuwa shine, ke daga kafa , allah na son mu shiyasa nace miki mu kara dubawa gashi kuma har gidan da ya shiga mun gani...

Malam har ka dawo ai na zata akwai layi , kinsan da wuri na je dan kar ki fara jin yunwa , malam kenan nagode , dauko kwano na juye kokon mu sha kafin yayi sanyi ,...

Kai malam ka bari zan iya....

Mai nake gani...inna da indo wanda sun shigo tsakar gidan dan kamar bukka yake, malam bai san sanda ya mike tsaye ba da jin muryar halimare..

Ramla na daga zaune dan baza ta iya tashi ba ama yanda taga malam nayi ta tabbatar wannan itace inna halimare kuma indo dake ta kallon ta ko tace hararar take yi tayi kama da malam....

Malam zaman daduro ka fara , kasa magana yayi , yau ake buru'uba a gidan nan da raina toh wlh baka isa ba , ke kuma mayya... sai kuma ta yi shiru tace maikomin kokon da kosen nan..

Indo zauna muci tukun musan nayi tun jiya bamu kai abinci baki ba...
Inna hat kina da lokacin cin abinci , ke dai zauna nace miki,

Zama indo tayi suka tashi da kwanon koko da kosai...

Nan inna ta mike taci damarar ta bismillah allah zamu fara wasa😆😆
Nan ta iyo kan ramla zata shake ta ba shiri malam ya shiga gaban ta halimare ki tsaya kiji abinda zan ce miki

Bakin munafuki kafi ta min daga gaba na kai ma ba karfi na kafi ba, so nake in gama da wannan karuwar sanan in dawo kanka , halimare baki ga ciki gare ta , na gani cikin shege ba , sai kinyi dana sanin kula mijina da kikayi

Ko a yarinta ni halimatu sadiya ba a taba ni a kwana lafiya , kuma ba wanda ya isa ya kwace min abu na ba tare da na kawar dashi ba,

Ramla ba abinda take sai kallon yanda halimare ke tsalle tana dira kamar yar bori , a zuciyar ta tace dole malam yaji tsoron ta

Halimare kar ki shegantar mi  da dana saboda nine uban shi, mai kace malam da fa kace , oh yanzu nagane wato cin fuska ake min , nan ta fara kukan karya saboda tasan malam baiso yaga tana kuka saboda bata taba haifan da namiji

Ba laifina bane saboda ban haifa ma da namiji ba allah ne bai ban ba.

Nifa ba haka nake nufi ba, halimare na auri ramla ba dan in ci miki mutunci ba sai don son da nake ma, wai inna mai kike jira

Ni in baza ki iya ba ki ban wuri kiga aiki da gamawa yanzu indo tace , kin min shiru ku kwa dama nasan wanan aikin ki ne na kawa innar ku nan , munafuka kin ki zama a gidan mijin ki shine ni zaki zo ki tayar min da nawa,

Ba ruwan indo kar ka mata saboda ba ita tace ma ka auro wanan mayyar ba da idano kamar na bujiya...

Ramla dake gefe a zaune ko dagowa ta kalle su bata yi saboda ita a rayuwar ta bata son fitina...

Kinji kunya kin kwace min mijina toh in fada miki bawanda ya isa da malam sai ni , nan ta iyo kan ramla da duka

Malam ya tsaya yayi shiru sai wata zuciyar tace in har haka zaka tsaya toh kaba maza kunya ace ba yanda ka iya da matar ka sai kace ita namijin,gashi tana neman ran ramla da abin cikin ta ,

Ke sadiya , yanda malam ya kira ta ni kai na saida na tsorata balle halimare da bata taba jin ya kira sunan nan ba , ya ishe ki kika kara taba ta sai na lahira yafi kin dadi wlh, kinzo muna zaman lfy mu zaka tada mana hankali ,fice min daga gida dan naga abin naki bana masu hankali bane....

A fusace ta yiyo kan malam , wani tsawa ya daka mata nan naga indo ta fita daga gidan ba shiri dan tunda take bata taba ganin fushin malam ba,

Kin fita kosai na illata ki , rai bace tace wlh sai kayi dana sanin abin nan da kayi dan in dai ina raye bazan bari ku zauna lfy ba , butulu wlh kaci amana ta.

Matsoraciya shine kika gudu kika bar ni , inna kina ganin yanda malam yayi kukan zaki ina zan iya tsaya wa kwanda ke nasan ba zai dake ki ba ni kwa nasan kila akai na zai kare,..

Ni malam zai ma haka duk zaman shekarun nan banda na biyun shi ama sakyayar da zai min kenan shine ni ya samo wacce zata maye gurbi na tunda raina...

Wlh bai isa ba

Yanzu dai inna mu tafi kafin mu rasa motar da zata kaimu rimi....

Aisha indo kenan har yau baki gama sanin waye ce halimare ba , kin na tina nin ina barin ta kwana ne

Toh mai zakiyi inna kar fa ki jamu ka hallaka

Ki wuce ki tafi gida

Ba inda zanje inna kafar ki ka fata...

Yanzu dai mai zai faru

Matso kiji ,

Mi dai naga inna na fadawa indo abu a kunne amma bansan mai ye ba...

Nan indo ta fara dariya , kai inna baki da kirki wlh , wanne irin rashin kirki ai ko Allah ba yasan kan gaskiya ta nake a cuce ni kuma a hana ni kuka...

Ke dai ki tsaya ki kalli innar ta ki

Masoyan inna halimare ina kuke zata aika wani aika aikan da ban sani ba...

Mai kuke tunanin zata yi🙊🙊

Drop your comments to let me know mai inna halimare zatayi

Votes 👇 👇
    
                                             Rema kay💋

KHAIRAT Where stories live. Discover now