KHAIRAT - 11

3.5K 172 6
                                    


Rukkaiya muktar rimi....

Shetima rimi malamin makaranta ne,da matar shi halimare, allah ya azurta su da yaya 6 ,duka mata , suna zaune a katsina nan cikin garin rimi...

Kowa yasan malam shatima da taimakon mutane duk da ba wani karfi gare shi ba dan rufin asirin da allah ya bashi dai...

Abin na batawa halimare rai in taga malam na taimako...
Dan ita son abun duniya ya mata yawa
In ka basu mu dame zamu rayu, kana gani dai ga yara a gaban mu har shida

Haba halimare maiyasa ke baki da tausayin dan adam, allah da ya bani na bada shi zai kara bani, ka fara kenan ban isa inyi magana a gidan nan ba kace kai zaka fara min wa'azi shin kafini sanin allah ne ko ya , kar shen wa'azi ka koma masallacin da zama ka samu masu biyan ka

Halimare kenan ke dai ba a maki, nan ta fara masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba.

Allah ya huci zuciyar ki halimare na ban yi dan in bata miki rai ba sarauniyar mata...
Murmushi ta fara haba malam kar yara suji mu kaga mun tsufa
Ai ba a tsufa a soyyaya..

Gobe in allah ya yarda zanyi tafiya...
Kai malam nikam tafiyar nan taka tafa ra ban tsoro ace yanzu baka mako guda a gida kace zakayi tafiya

Halimare in banje na danyi buga buga dina ba taya zan samu mana abinda zamu sa abaki, kina gani dai yanzu an sallame ni daga aikin koyar wa

Ko so kike in zauna a gida muci kan mu,,,,
Allah ya kiyaye hanya , ba dai shi kake so kaji ba, ko kefa halimare na.

Har ga allah ta fara zargin yawan tafiya nan da malam keyi kwanan , abinda da baiyi da.....

Inna yana ganin ki anan zaune ko baki da lfy ne , indo baza ki gane matsala ta ba, haba sai dai in baza ki fadamin matsalar ki ba , kinsan dai babbar ya kamar kawa take...

Baki lura da mahaifin ku da tafiyar da yake ba , sati baya zagayo wa zai ce zaiyi tafiya , inna ai wanan laifin ki ne baki ga yanda nake da iliyasu ba bai isa yaje inda bance ba

Shiyasa kuka ga naki tarewa a gidan shi , yazo nan muyi zaman mu da a yanzu dai shine matar nice mijin dan sai abinda nace za ayi.

Ke ni ba wanan ba fadamin mai yakamata muyi, muyi kuma ,kiyi dai ai mijin ki ne, toh naji yanzu dai nawa zaki bani in har zan baki shawara mai kyau , daidai kudin ki daidai shagalin ki , lallai indo kin rika nice fa halimare mahaifiyar ki...

Haba inna kinsan dai zamanin nan na yanzu komai ya chanja, toh naji , ki dauki wanan atampar da malam ya kawo min , ehn sai kuma mai, ke ya ishe ki fadamin mai zanyi

Gobe ki shirya ki bi malam , kema dai kin san bazai bari in bishi ba , toh da cewa nayi ki bishi yana sane , haba inna yaki ke abu kamar ba raino na ba. Kuji mun yarinya, kinga inna gobe ki shirya ki bishi a baya ama kar yasan kina bin shi ni ko mutafi tare ne, hakan zaifi , koma mai ma magance abun mu.....

Washegari tun sassafe inna da indo suka gama shirin su.
Malam na musu sallama suka bi bayanshi sai dai niqab suka sa da bakar doguwar riga yanda bame gane su

Mota daya suka shiga da malam sun kujerar da ke bayan shi.
Har suka iso garin malumfashi inda malam ya sauka nan suma suka ce sun iso inda zasu sauka

Da kafa malam yake taka wa suna binshi ya baya...
Wai ina malam zai je ni inji indo,ni kam har na gaji kafafuna sun fara min ciwo , ai inna kwanda ki mike su dan yanzu muka fara tafiya.

Ke tsaya mu sha ruwa ga tuka tuka nan , bara in tuka miki ruwan yanda zan na kallon inda yabi , inna na gama shan ruwa tace mu tafi , dadi na dake inna kin fiye sun kai taya mu tafi bayan ban sha ba , kuma kina kallon shi kar ya bace mana indo tace , inda indo ta gama shan ruwa tana dago da kanta taga ba malam balle mai kamar shi

Ina yabi ta tambaya, ban lura ba , bayan nace miki kina kallon shi

Salamu alaikum, malam sannu da zuwa kasha hanya , sannu ramlat, bara a kawo ma ruwa...

Da daddare malam da ramlat na zaune a tsakar gida kan tabar ma suna hira , allah ya sa dai kerosene din cikin lantar kin nan ya kaimu har lokacin barcin mu, ai da kinyi magana dana fita masallacin dana siyo , haba malam yau fa kazo na fara cema ba abu ko a siyo wani abu tun kafin ka huta...

Ramla kenan shiyasa nake sonki , murmushi tayi , allah dai ya saukeki lfy ya raya abinda zaki haifa, ameen...

Malam ina da maganar da nake so muyi, ina jin ki , lokaci yayi da ya kamata da ka hada kan iyalinka , kaga har yau inna halima bata san da auren mu.... , ramla zaman lafiyar ki shine ki zauna inda kike dan halimare da yaranta baza su bari muyi zaman lfy ba in har suka san da auren mu....

Amma malam kasan jiki da rai , koma mai zanyi hakurin zama dasu ko dan abinda zan haifa ya tashi cikin yan uwan shi., lokaci nake jira zan yiwa halimare magana cikin kwanciyar , hmm shiru kawai tayi dan ta gaji da yiwa malam magana ba tun ba yau akan ya hadasu.....

Indo sai fada da masifa take Kinga abinda kika jawo mana yanzu ina zamu samu ma kwanci tunda gashi dare yayi sunce motar da zata rimi sai dai gobe da safe, haba indo bafa ke kadai bace a cikin matsalar nan kuma naga ai ke kika ce muzo , daga taimako toh daga yau kar ki kawo min matsalarki...

Kinga indo ga wani shago can da alama ba mutane kuma a bude yake muje mu samu ma kwanci...

Comments 🖎 🖎
Votes 👇 👇

Rema kay 💋

KHAIRAT Where stories live. Discover now