KHAIRAT -9

3.6K 219 2
                                    

                                
Kaduna.....

Ki fada min maiyasa kika ce kin fasa auren shi bayan nasan irin son da kike mai , shiru tayi tana kallon mama , kar ki manta ba mai fahimtar ki kamar ni in har kina da strong reason wlh ni me tsaya miki ce dan bazan bari a zallince ki ba in har ina raye ,

mama soja ne , soja meaning what, kin manta sojoji mugaye ne ga shaye shaye da bin mata , yanzu akan wannan ne kika tada hankalin ki kin taba ganin shi yana bin mata ko kin taba gani yana shan wani abu.....

Toh ki saurare ni da kyau yau ba soja ba in allah yayi zaki auri ma shayi ba yanda kika iya kuma baki sani ba in kinki mubarak kika nemo wani zai boye miki halin shi sai bayan aure ki fara gane mugayen halin shi , balle ma shi bai yi kama da irin su...

Kina abu kamar wacce bata da imani.
Addua ce maganin komai da kike gani , kayi adduar allah ya zaba miki abinda yafi alkairi, bazan iya taimakon ki ba dan in baban ki yaji wanan abun dagani har ke ba zai bar mu ba...

Ki cire wanan mugun tunanin a ranki  ki kwantar da hankalin ki komai nufin allah ne . Har ta mike zata fita sanan ta jiyu kuma maza ki tashi kiyi wanka kici abinci , in baban ku ya dawo kije ki bashi hakuri dan ya lura kwana biyu ba kya fitowa daga daki....

Bayan sallar isha khairat taje yiwa baba sannu da zuwa , ina wuni baba , ko kallon inda take baiyi ba saima gyara zama dayayi sanan ya gyara murya, wato kin girma da har kike fushi dani akan nace sai anyi auren, ni ba auren dole zan miki ba ama ki sani bakin alkalami ya bushe dan ke da bakin ki ka ce kina sonshi yanzu kuma shine kike so ki mai damu makaryata eh...

Dake nake kina jina kinyi shiru , yau kwanan ki nawa rabon da kizo ki gaishe ne , kuka ta fara tana girgiza kai , kayi hakuri baba.... bata gama furta abinda ke bakin ta ba taji saukar bulala a jikin ta kafin tasan mai ke faruwa baba ya damke hannun ta ba damar guduwa...

Mama na kwance a dakin ta tajiyo ihu da sauri ta fito lokaci daya ita da nusaiba suka shigo falon shi, haba alhaji , nusaiba na kuka tana baba dan allah kayi hakuri 😭😭 ( fans kuzo mu taimaki khairat hannun baba)....

Kasa karasa wa inda yake su kayi saboda sun san halinshi , har kasa nusaiba ta tsugunna tana rokon shi saboda taga yanda yake dukan khairat kamar an aiko shi , jefar da bulalar yayi sanan ya zauna , fita mun daga falo kafin na kara miki wawiya...

Kasa tashi tayi sai nusaiba ce tazo ta daga ta , ba abinda khairat keyi sai kuka saboda baba ya ji mata  ciwo duk jikin ta marks ne na bulala....

Har suka iso daki ta kasa magana sai kuka take , nusaiba kwa sai hakuri take ba, can kuma tace......

Baba ya tsaneni a gidan nan kowanne laifi nice , ki daina fadan haka , tun muna yara ba wanda yafi duka kamar ni ya mai dani kamar jaka , ke ma dai kinsan baki da gaskiya, hmmmm....

Ranar kasa barci tayi , ni yanzu ya zanyi da rayuwata banson mubarak ko ka dan a raina , me sonshi ma makiyi na ne , ya akayi tun farko ma ban san shi sojo ba ne , alhamdulillahi ma ya daina kira na....

Sai bayan sallar asubahi ta samu barci.
Gari na waye wa ta tashi dan baza ta iya barci da wanan damuwar ga jikan ta na mata ciwo dan ko ina alamar bulala ne a jikin

Da kyar ta samu ta mike ta shiga toilet dan ta samu tayi wanka ama kuma sai da tayi spending 30 minutes tana kuka kafin ta fara wanka

Tana fitowa ko mai bata shafa a jikin ta ba, doguwar riga ta dauka tasa sanan ta zauna kan gado tana tunani

Sis kin kwana lfy , in na kwana lfy zaki ganni haka , daga tambaya , hmm amsar tambayar ki na baki...

Nusaiba wani abu nake so kimin, sis kafin wanan ki tashi muje muyi breakfast, am not hungry,

Toh fadamin mai kike so , alfarma daya nake so ki min, toh wacce irin alfarma, kimin alkawari first cewa zakiyi duk abinda nake so , kiyi hakuri i can't promise yhu first sai naji mai ne ne..

Hmm har ta fasa maganar , sai kuma taga in tayi shiru kanta zata cuta kwanda tayi magana allah dai yasa nusaiba ta yadda da bukatar ta....

Inajin ki , ina so ki auri mubarak, what ! Yhu are sick , dan allah nusaiba ke kadai ce hope dina in baki taimake ni ba wa zai taimake ni....

Kice ma baba ke zaki auri mubarak kice kina son shi, kasa magana nusaiba tayi tana kallon khairat yau ta yadda akan maganar da ake cewa tun suna yara cewa khairat na da taurin kai , da in ana fada sai taga ko dan basu fahimce ta bane...

Kinyi shiru baki ban amsa ba.
Taya zata baki amsa inji mama data fadi rai a bace , wato sonkan naki har ya kai haka , toh bara kiji nusaiba baza ta aure shi ba , ke da kika kawo shi ke zaki aure shi , kuma ki fita da ga idona kar kiga ina kyale ki , mama dan allah, yimin shiru joor kafin in kara miki daga inda baban ki ya tsaya

Kin raina mu saboda bamu da daraja a idon ki in ni kin raina ni ai bai kama ta ki raina mahaifin ki , komai kike so a gidan nan yana miki , shine yanzu zaki jawo mai magana, in kin ki mubarak kina da wanda zai aure ki ne kina ganin duk kawayen ki sunyi aure....

Ban ma da abinda zan fada miki , ki tashi muje kiyiwa mahaifin ki bayanin abinda kike so , mama kiyi hakuri ,,,,,

Shiru duk sukayi a falon baba , lfy sassafe nagan ku haka , dama khairat ce ke son yima magana , in kinsan maganar auren ki ne banso inji , nan mama ta fada mai abinda khairat keson nusaiba ta mata, hmm khairat kenan toh naji abinda kike so sai dai baza ki samu abinda kike so ba ama zan miki alfarma daya , nan ta dago idon dan taji mai ne ,

na baki nan da sati biyu ki kawo min wanda kike so tunda yanzu ba kya son mubarak, in har kika wuce sati biyu koda da kwana daya ne toh kar ma kizo ki same ni dan bazan saurare ki ba....

Har ya kai bakin kofa ya juyo ko kallon inda take baiyi ba yace kuma daga yau har zuwa sati biyun nan ko nan da gate banso in ganki kin je balle ma ki fita daga gidan, yana kai wanan ya fice

Wanan wanne irin haline ta shiga , ko dayake ita ta jama kanta , yanzu allah ne kurum zai iya taimakar ta , dan ita ba wani saurayi gareta ba balle tace ya turo...

Jiki ba kwari haka ta tashi ta koma sama tana adduar allah ya taimake ta , ni dama allah ya dau ranshi sai inga yanda za ayi auren  subhanallah mai nake tinani allah ka yafe min tace.

Bayan kwana biyu

Abinci taje ta dibu a kitchen tana so ta ci ko zata rayu dan dama mama ke bata hakuri akan ta ci abinci toh ita ma ta fita daga har kar ta kowa fushi yake da ita

Ama ita yanzu ta yanke hukunci...

Yau ya khaleel ya dawo yana zaune shi da baba suna hira , khairat taje ta kira mama tace tana son magana dasu , banda lokacin ki ina da abunyi , mama dan allah minute 1 ne kurum , ta mike ta wuce inda su baba suke ,har kasa ta tsuguna sannun ku baba , sannu khairat , sai kuma tayi shiru tana jiran mama ta shigo duk da bata san ko zata zo ba

Kusa da baba taje ta zauna san nan tace ina jin ki, yau kuma dame kika zo inji baba ko har kin samu mijin ne, a'a baba ba wanan magnar bace,

dan allah ku yafemin nasan na muku laifi , na tuba wlh bazan sake ba, toh khairat mun yafe miki yace , kuma na yadda zan auri mubarak , zanyi duk abinda zai faranta muku , shikenan dama baki mana laifi ba , allah ya yafe mana gaba ki dayan mu , ameen, allah ya miki albarka ameen baba nagode

Sarkin rashin ji ya khaleel ya ce , kar ka taba min khairat dina inji baba , yau kuma taka ce mama tace , dama can tawa ce , duk su kayi dariya ama banda khairat....

6 months later

Yau ne helicopter su captain Muhammad da yaran shi ya sauka a nigeria army headquarter, major general safwan yaje tarba su kuma yana congratulating din su akan success din da sukayi a mission din da sukaje , wa yanda suka ji ciwo ambulance ya wuce dasu asibiti....

Ur votes and comments keep me going but i need more 👏👏  to move on
                                         
                                         Rema kay 💋

KHAIRAT Where stories live. Discover now