KHAIRAT -3

5.7K 257 10
                                    

                            
Maigadi yayi wa magana akan ya mai sallama da mai gidan, yace toh minute bai fi 5 ba sai ga malam hamisu ya dawo bismillah shigo...

Babban falon baki nan ya tadda baba na jiran shi da sallama ya shiga baba ya amsa ina wuni baba dan har kunyar baba yake ji shi da bai ma san ko zai samu karbuwa a wurin shi ba, yaro bangane ka ba??

Mubarak ya sunkuyar da kanshi yana susa keyar shi ya dama baba, sai kuma yayi shiru yarasa ta inda zai fara zancen kar ace yayi rashin kunya...

Ina jin ka, dama nazo wurin ka neman izinin auren khairat sai yayi shiru, baba bai ce komai ba ya tsaya yana kallon shi, itace ta aiko ka wuri na, a'a dan bata ma san nazo ba, ina son khairat ama taki kulla taji da mai najo in na rasa khairat zan iya rasa raina, nan ya tina gaban wa yake sai yayi shiru....

Naji bayanin ka sai dai  bazan iya aura wa iyata wanda bata so ba, dan haka kayi hakuri kaje ku daidaita kan ku, ya mike jiki ba kwari zai tafi, har ya kai bakin ko fa baba yace an ma baka fada min kai waye ba.

Asalinshi

Rtd Comptroller general Umar habib na da mata biyu hajiya umma da aunty fatima. Umma na da yaya shida nasir, maryam, Muhammad, khadija, salim da nabeel. Ita kwa fatima yar ta daya tillo wacce ta rasu ta bari bayan haihuwar ta dan ko shayar da ita bata yi ba allah ya dau ranta wacce suke kira yasmin....
Asalin su fulanin gombe ne kuma a nan garin gombe suka taso saboda duk da mukamin da umar habib ya rike baison yayi naisa da gida har lokacin da ya ajiye aiki dan ya samu lokacin iyalin shi duk da sun girma...

A yanzu nasir babba dan shi accountant ne da matar shi maimuna da yaran su uku musa ibrahim da deena.maryam likitace ta auri business man saifullah da yayanta sadiya,fatima aisha da hauwa. Muhammad mechanical engineer da a yanzu yayi joining nigerian army yana matsayin captain,khadija ma tayi aure ama allah bai bata haihuwa ba. salim na makaranta yana karantar architecture nabila kuma tana karantar law, yasmin tana secondary school....

Captain M.U.habib dan ki manin shekara 28 da haihuwa baki ne dogo irin huge body dinan gare shi duk gidan su shi kadai ne baki ba kamar sauran yan uwan shi da hasken su,shi hajiya umma ya biyo wurin kama, yana son yan uwan shi zai iyayin komai dan yaga ya faranta musu balle ma yasmin wanda ya zame mata tamkar uwa, uba a wurinta baison abunda zai bata mata rai saboda hallacin da aunty fatima tamai dan ita ya taso ya sani a matsayin uwa...

*Cigaban labari...

Tunda ya fito daga gidan alhaji abdulrahman kan shi ya mai zafi yaji ba inda yake so yaje sai gida, dan haka ya kama hanyar gombe,kan hanya sai gudu yake da motar yana tina nin yanda zai bullowa khairat dan yanzu ko ya kirata bata dauka tunda ta gane number shi, sai tunani yake sai cikin dare ya isso gombe ... 

Ba wanda ya san da isowar shi sai gate man din gidan dan shi ya bude mai gate ya shigo, dakin shi ya wuce ya kwanta dan ya samu barci ama sam ya kasa sai tinanin khairat yake tunda yake a rayuwar shi bai ga macen da ta dauke mai hankali ba kamar khairat "there's something special about her" har akayi kiran asuba barci bai dauke shi sai bayan sallar asubahi yasa mu barci yayi gaba dashi.....

Sai wuraren 11:15am ya tashi yana mamaki yau yakai har lokacin nan yan barci, toilet ya fada yayi wanka sanan ya fito yasa white lacoste da blue jeans. Ya nufi cikin gida dan yasan basu san da zuwan shi parlour mahaifin su ya fara shiga da sallama abban su na zaune yana karatun jarida yaji muryan shi jiyo wa yayi yana captain Muhammad habib yaushe a gari ya tsugunna yace abba ina kwana ka tashi lfy, lafiya major ya aiki? Aiki alhmadulillah na dau hutu daga zaria nake, hope all is fine, mai ya kaika zaria yace abba naje ganin wani aboki nane, to madallah, mikewa yayi yace bara na shiga wurin umma. Da salim ya fara haduwa bros how far😎 oh na manta good morning captain 🙋 mubarak ya dan buge bayan shi yana dariya morning salim, ama yaushe ka shigo gari bros? Jiya daddare duk kunyi barci, kaga manya masu tafiyan dare ba kwa tsoron komai,"taya zasu ji tsoron hanya bayan suke tsare ta nabila ta fada tana dariya" ina kwana yaya, ya dan bata rai saboda ya san halin nabila yace lfy kuna hutu ne ko mai kuke a gida?? Toh boss yara baza suzu weekend ba ka wani tsare ta da tambaya inji umma wacce shigo war ta kenan.

Umma yunwa nake niji ya fada dan kar ta soma fada yasan halin ta indai akan nabila ne sai suyi fada, ga breakfast chan a kan dinning nabila je kiyi serving dinshi "yaya mai matsalar ka its all written on your face kana cikin damuwa" yazo kai wa dankali cikin bakin shi yaji tana tambaya sai ya fasa ya tsaya yana kallon ta, tabbas gidan nan bawanda yasan in yana cikin damuwa kamar nabila saboda bai iya boye mata duk wata matsala da yake ciki ita da shi kamar tom en jerry suke" ta katse mai tina nin da yake ka fadamin maybe i have solution to your problem, barrister in lokacin fada miki yayi zan fada saboda ni kai na bansan mai ke farawu ba.....

Na wuce gidan hajiya (kakar su ta wurin mahaifinsu) muna gaishe ta inji umma.
Tshohuwa mai ran karfe kin ci zamanin ki kinci na yayya gashi kina cin namu, a'a ubana yaushe a gari . hajiyar mu nayi missing dinki, bawani nan da dagaske kayi missing dina da kazo inda nake yanzu kusan wata bakwai rabon ka da gida, kinsan yana yin aikin mu sai a hankali yanzu ma hutun sati biyu na samu shiyasa kuka gann...bansan ya za kayi ba in kayi aure ka fara tara iyali kai da kullum cikin aiki kuke? Yana yin aikin mu kenan ya muka iya sai in tafi da matata kullum tana tare dani, kai da kaki fito da mata duk sa'an nun ka sunyi aure ama kana nan kullum addua ta allah ya baka bace ta gari, kuma ya bada insha allah,hajiya ta mike tsaye dagaske ubana,ya daga mata kaia alamar a" alhmadulillah allah mun gode ma zata fara taka rawa yace an ma taki amincewa dani ko sauraro na bata yi ba..hmm ya take ,shes kind daz all i kind say, yar waye ce kuma ina take inji in same ta har gidan su uban nawa zata ki wanda yan mata ke ma layi ita ta samu shine zata ki...kar ka damu mubarak zata so ka in allah ya yarda, ya sunan ta?? KHAIRAT yace, suna mai dadi allah yasa ta zame mana alkairi kamar sunanta, bansan ya zanyi ba hajiya har wurin mahaifin ta naje yace sai na daidaita da ita kafin ya yarda ban ta son wata ya mace ba kamar yanda nake son KHAIRAT ki taimake ni..kar ka damu ubana insha allah indai alkairi ce gare mu sai ka aure ta ni da kai na zanje ne man ma aurenta ko da kwa shine abu na karshe da zan ma a duniya ka kwantar da hankalin ka...nagode hajiya nasan a wurin ki kadai zan samu kwarin guiwa dan nasan umma baza ta saurare ni ba tunda naki yar uwanta, bayan minutes talatin ya mike bara na wuce hajiya zanje gidan aunty safiya(kanwar mahaifinsu) tun dazun hamza ke jira na. Allah ya kiyaye hanya ka gaida mutan gida, zasu ji.

Kaifa dan rainin hankali ne tun dazun naki fita na tsaya ina jiran zuwanka bayan kace min kana hanya, wlh wurin hajiya na tsaya, dama sai da nayi tunanin haka tunda naga ka jima baka iso ba kana chan kana biye hajiya da surutu ita kuma taga dan gatanta zatayi ta biye ka... "are you jealous or what" whatever so ya mai lbr, lbr daya gare ni shine KHAIRAT. hamza ya dan matso "are you in love or what" yes ta tafi da zuciya ta kuma taki ta juyo ta saurare ni ko rufe ido na nayi ita kwai nake gane, hamza yayi shiru yana sauraran shi chan yace a ina take in anjima muje mu same ta har ta isa taja wa captain m.u.habib aji ita waye ce..itace KHAIRAT. I can't believe my eyes i have never seen you in this condition mubarak since childhood we have been together, what so special about her? Shes just different❤ hamza yace oh dama captain kalaman soyyaya zasu iya fitowa daga bakin ka da kullum sai dai kayi ta ban lbrn aikin ku da nake gajiya da ji, oh dama kana gajiya ama shine kullum sai kace na baka lbr dan rainin hankali, anan mubarak ya manta da matsalar shi ya biye hamza suna tayi. Sai bayan sunyi sallar magrib hamza ke tambayar shi yar wacce gari, kaduna yace, yanzu duk yan matan garin nan dake binka ba wacce tama har sai da kaje kaduna hmm ka shirya gobe muje kd mubarak ya jiyo yana kallon dan uwanshi da mamaki dagaske kake. Kasan ban ma wasa irin haka kuma matsalar ai matsala tace.

Bayan sati daya mubarak da hamza sunje zaria yafi sau a dirga ama khairat ko kallon su batayi ba wani sa'in in sunje basa samun ganinta gashi yanzu har sunyi hutun semester ta koma gida. Hamza ya riga yace ma mubarak ya hakura da ita shi kuma yace sai dai in mutuwa nayi....

Washegari hajiya na zaune ita kadai tana ta tinani saboda matsalar mubarak ya dame ta tana son jikokin ta ama shi daban yake acikin su ya fisu hakuri da son mutane, wayarta ta fiddo ta kira number shi yana dauka tace ka shirya gobe zamuje kaduna....

Readers mai zai kai hajiya kaduna kuma zata ci sa'ar zuwanta.
Nidai nace allah ya kiyaye hanya hajiyar mu.

                                             
Comments please if you enjoyed this chapter and tell me about your opinions.

Votes👇
                                                  Rema kay

KHAIRAT Where stories live. Discover now