part 17

1.7K 107 33
                                    

Dukan mu muka tsaya mukayi chirko-chirko,daga ni har hadiya, gashi kaka na jiran  Taga me hadiya take kunshe dashi.gashi munyi Shiru dagani har ita Babu me kokartawa yace Wani abu.

kaka Kuwa data gaji saita Tashi tayo inda muke Saboda ta gaji da jiran, gashi Kuma masifa na cinta a ciki. Nikuwa gabana sai faduwa yakeyi narasa yadda zanyi. Ta Karasa tare da yaye hijabin hadiya saiga kwano ya bayyana. Kaka taja numfashi Kafin ta Kalli hadiya Sannan tace, "wannan kuma menene, Daman abunda ke kawo ki gidan Nan Kenan koh?"

Kaka ta Kara da"meyasa kike kawo Mata abinci?,ko Kuma Duk tsabar munafirci NE kawai"

Hadiya tace "aa,ko daya kaka, dayake munyi Dan wake ne shine na yanke shawarar in kawo Mata Saboda abun marmarine... Kuma jiddah Nasan shi... "

kaka ta katseta da Tsawa Tana fadin "Rufe Mani baki, Ashe Kema munafukace Kenan, Babu abinda kuka iya sai munafinci,watakan harta Kai Kina Zuwa da abinci ki shigo dashi ki kawo Mata ban sani ba?"

Na budi baki nace "kaka yaune kawai fah ta kawo mun shima Saboda naje gidan nasu,shine tace zata kawo Mun..."   kaka ta ce "yimun Shiru munafukar banza kawai,kuma sai jikin ki ya gaya maki"

Hannatu tace" kaka Daga gani wallahi ta dade Tana Kawo Mata abincin bawai yau ne Kadai ba, kawai dai  sunaso su Raina mana wayo NE. "

Nadaga idanuwa na Kalli Hannatu, Amman Babu abinda zan iya cemata Saboda kaka ta sakoni agaba da fitinarta. Kaka ta Kalli hadiya tace "ke kuma kafin in bude idona in sake ganinki ki wuce ki Bar gidannan tun kafin Raina ya baci in maki Dukan tsiya"

Hadiya ta Kalleni ,nikuma Nayi Mata nuni data tafi kawai kafin kaka ta bugeta.
Kaka ta doka Mata tsawa, "zaki fita ko Kuwa? Kaji mun yar iskan yarinya sai shegen taurin Kai.... "

Hannatu tace"kaka kawai ki buga Mata warning karta sake dawowa gidan nan,saboda Duk Wani munafirci tare sukeyinshi da ita jiddan...." na Kalli hadiya itama ta kalleni,kaka Kuwa sai cewa tayi " kuma fah Hakane, ke wama kike da suna... " Hannatu tace " hadiya" kaka tace Yauwa "hadiya, Idan na sake ganin kafafuwanki Sun leko gidan Nan da zummar wai Kinzo ganin jiddah Harma ki kawo Mata abinci,toh wallahi allah ne Kadai zai rabani dake dunkuwa saina maki dukan tsiya, maza-maza zo ki fita ki Bar Mani gida"

Idanuwana NE suka ciko da kwalla, kawai ina mamakin irin Halin kaka, ko kara bazatayiwa hadiya ba, kawai ta Rufe ido Tana zabga Mata rashin mutumci yadda takeso.

Aikuwa kafin mu Ankara, kaka ta fizgi hijabin hadiya Tana fadin "Idan bazaki bar mun gida ba, Ni bari in jaki harsai kin fita, kajimun shegiyar yarinya kai"  hadiya dai batace komai ba, Haka ta bari kaka ta Jata.

Nace "kaka Dan Allah ki kyaleta zata tafi da Kanta basai kin Jata ba"

Saiji nake ta kwasa mun Mari a fuska,haka na dafe wurin hawaye na zuba a fuskata Don takaicin abinda kaka keyimun. Amman dukda Haka na cije na bisu har kofar gidan. Wai koda Idan kaka ta dawo cikin gida sai in tsaya in bawa hadiyar hakuri, Amman inaa,tana Gama tura hadiya waje ta kara Mata gargadi akan karta sake dawowa,saikuwa ta kulle kofar gidan.  Nikuwa data juyo ta ganni ta rakoni da dundu har tsakar gida. Hannatu Kuwa in banda shewa Babu abinda takeyi.

Daga hannatun har kakar kallonsu kawai nakeyi da bakin ciki a Raina. Na Rasa yadda zanyi. Alokacin sainaji Daman kawai in mutu in huta da irin wannan cin zalin da takurawar da nake fuskanta wurin kaka.

Hannatu tace "ohhhh kaka wai mutum da abinci a gidansu Amman kamar Maye saiyaci na gidan wasu.."

Kaka tace " AI ki barni da ita, dukan tsiya datake bukata wallahi dai-dai nake da ita.. "

Danaga bazan iya tsayuwa ba in cigaba da ganinsu sainayi hanyar daki in kwanta. Amman kaka ta sake kirana, " keh! Nace ki tafi ne?,ban Gama fadin abinda zan fada ba Don Haka ki dawo"

Na dawo na tsaya ina jiran ta kammala fadin abinda zatace.

Kaka ta kalleni Sosai tare da hadamun da harara kafin tace " daga yau sai yau,kar in sake ji kuma Kar in sake ganin kafafuwanki sunje gidansu yarinyar nan, Idan Kuwa na Samu Labari kin cigaba da Zuwa toh wallahi Rankine zaiyi mugun baci,don saina gasa maki aya a hannu,kina jina? "  ta Kara da " ke hatta kawancen dakukeyi MA na gano kawancen munafircine,don Haka shima na yankeshi daga  yau...." Hannatu Kuwa sai murna da shewa takeyi Tana Dariyar mugunta da jin dadi.

Na kalle kaka idanuwana cike da kwalla nace " eh kaka naji..."

Na sake juyawa na koma ciki abuna. Bakin ciki uku sun taran mun GA rashin Zuwa makaranta da kaka ta hanani GA Kuma rashin Zuwa gidansu hadiya, Da Kuma Yanke kawancenmu  datace Tayi, na rasa da wannan zanji. Abu daya Nasani shine kawancen mu bazai yanke ba Saidai kaka ta Dukeni harta gaji Amman fah Babu Ja. Koda banje gidansu ba still friendship din namu na nan Babu chanji.

***   ***  *** *

Kwanaki sun shude, Amman Babu abinda ya chanza ina Nan zaune a gida Babu abinyi. Kuma mates Dina na Chan makaranta suna shiring yin jarabawar Gama secondary, Wanda ya Kamata ace tare zamuyi dasu. Amman kaka da kafeffen halinta, Sam taki yardar mun da in koma makarantar. Hakanan nake rokan Allah daya kawo mun Wata mafita ta daban Wadda Zaisa in koma makaranta.

Na fito na Gama share-sharena da Duk ayyukana, Nayi wanka Sannan na shiga daki domin in Dan kwanta, na Dan Wani lokaci.

Na dauko Wayata na kunna, dayake ya Dade a kashe, kasancewar bana amfani dashi saina kashe. Koda na kunna sakonni daga wajen umar Babu adadi, dayawa Haka suka shigo. Sam na ma manta da zamanshi, Saboda bawai ganinshi nakeyi ba.

Nan na danno numbar matar kawuna alhanji bala, Nayi Mata flashing,baa Dade ba ta kirani,  muka gaisa Sosai da ita, Wani zuciyar na gayamun in Sanar da ita rashin zuwana makaranta ko tayi MA Kawuna magana ya kira kaka Ya mata magana, Amman sai wata zuciyar tace mun ba yanzu ba. Hakanan har Muka gama gaisawa da ita, ban mata maganar ba.

"jiddah"

Sunana naji ana kira a tsakar gida, na Tashi da sauri na nufi tsakar gidan, nace "kaka gani"

Ta miko mun kudi Sannan tace " gashinan ki siyo mun dawa, masara da Kuma gero, kwano daddaya dukansu..."  

Na ansa kudin " nace toh " Sannan na juya zan tafi, Amman ta jawoni, ta kalleni Sosai kafin tace " saura kije ki Dade ko Kuma inji Labarin kinje gidansu yarinyarnan, wallahi ranki saiyayi mugun baci, kinji na gaya maki"

Bance komai ba na Tafi Na dauko hijabina ,na tafi Aiken kaka. Babban shagon unguwan da Dan nisa Babu laifi. Haka dai harna isa shagon.   Bayan an Gama auna mun komai na dauka zan tafi, sainaji an Kira Sunana.

###

Assalamu alaikum.

Masu karatu ina dada Baku hakuri Akan shirun da kukaji, na tsawon lokaci. Hakan ya farune bada San Raina ba. Kasancewar na Dan shiga rububi. Amman in sha Allah yanzu update zai dinga Zuwa Akan lokaci. Kuma da fatan munyi azumi da sallah Lafiya. Allah ya maimaita mana. Ameen.

I hope my apologies will be accepted 😅😁😁

Ayi karatu lafiya

And don't forget to
Vote
Comment and
Share.

Daga taku,
UmmAimann 😘.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 25, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

JIDDAHWhere stories live. Discover now