part 7

1.3K 61 0
                                    

Da sunan Allah mai rahama mai jin Kai.

***   ***************

Kaka biyo ni tayi daki,sai masifa takeyi "kaji zancen banza Dana hofi, toh in shaida maki Idan har baki tube kayan nan kin fito kinzo kin tafi ba,toh wallahi ranki zaiyi mugun baci. Yar rainin hankali, makaranta kanki aka Fara,yau jidda Idan nace kin Dena Zuwa makarantar MA gabaki daya toh ya zauna... Maza-maza ki cire kayan ina waje ina jiranki, ja'irar kawai"

"Idan MA kinje makarantar uwar WA kike koyowa, Kawai salon yawo dai, GA bukatu a gida ina da shi, saiki dawwama a makaranta, toh karyarki in gayamaki"

In banda kuka Babu abinda nakeyi, kukan MA irin mai cin rai Dinnan har zuciyata nakeji ta Fara mun zafi Saboda bakin ciki. Haka Nan na Chanza kayana na saka hijabi Sannan na fito.

Na iske kaka, a gaban kayan, hawaye NE Suke neman zubowa Amman saina daure na Shanye,don banason inyi kuka a gabansu. Nama nayi WA kaina alkawarin in rage kukan Don bashi da wani amfani, Saboda Babu abinda zaiyimun.

"gashi nan kayan Duka komai a lissafe yake,kibi komai a hankali banda barnatar mun da kaya,kinji ni koh,kuma ki tabbata kin saido komai kaf kafin ki dawo."ta Karasa maganar Tana Mai nuni da kayan Nata.

Kai kawai na girgiza Mata, Don banda muryar da zan Bata Amsa dashi.na saka Gammona na kwashi kayan, Sannan na dauki hanyar kasuwa, da zuciyata cike da kunci da bacin rai.
Komai da yake faruwa Dani saiya dawo mun sabo fill.bakin cikin ya Kara Karuwa.

Koda Rana ta Fara zafi Sosai, lokacin Nayi Rabi, na Kosa ingama sayarwa domin in koma gida in Samu Hutu. Amman Nasan wannan ba Abu bane Mai Yuwuwa,saboda ko yaya NE kaka saita kirkiro aiki ta bani.  Bayan LA'asar NE, lokacin Duk na Gama sayarda komai,na tattara komai na,na nufi gida.

Koda na ISO unguwarmu, yanma tayi Sosai Kuma banjin zan iya komawa gida a Haka, saina wuce gidansu hadiya Kai tsaye.

Ina Shiga gidan na iske su a tsakar gida Kan tabarma suna hira.

"Assalamu alaikum"nayi sallama tare da ajiye kayana a gefe kafin na Karasa inda suke.

"waalaikumussalam," Suka amsamun, na samu wuri kusa da hadiya na zauna.

"ina wuni inna"

"lafiya Kalau, Kece da Yanma Haka a gidanmu"

"eh wallahi Inna, dawowata Kenan koh gida banje ba nace Bari inzo nan"

"dafatan dai komai lafiya?"

"alhamdulillahi"

"toh Masha Allah,hadiya tashi ki zubo Mata abinci mana" nan hadiya ta Tashi, Jim kadan da tafiyartata saigata da kwanon abinci ta dawo. Ta ajiye mun nace"sannu na Gode,ya makarantar Kuwa? "

"alhamdulillahi, an MA bamu assignment a English da Islamic studies, saikizo kiyi" hadiya ta Karasa maganar Tana Mai Tashi taje ta debo mun ruwa.

"ahhhh toh Allah yasa babu wahala dai"

"AI karki damu kina dubawa zaki gane Don bawani wuya acikinshi"

"okay toh AI Masha Allah kawai "na fada ina Tura Loma acikin bakina,saboda balaifi ina jin yunwa.

Inna tace"kinyi sallah Kuwa? "

"Inna ina gamawa zanyi sallah in sha Allah "

"toh maza, abada himma aje ayi"

Nace "toh" ina Gama cin abincin, na Tashi Nayi sallah LA'asar, aka Kira magariba shima na hada Nayi gabaki daya.bayan na Gama NE na shiga Nayi Ma Inna sallama,sannan na dauki kayana, hadiya ta fadawa Inna zata rakani,naji dadin Haka at least ba zanbi hanyar ni Kadai ba ina da Mai Dauke Mani Kewa harna isa gida.

JIDDAHWhere stories live. Discover now