part 9

1K 60 16
                                    

Gabana ne ya dinga bugawa uku-uku. Nayi Shiru kafin bakina ya iya fadin

"baba tanko"

Be ansani ba, sai Cewar dayayi "zaki matsamun in wuce ko Kuwa zaki tsareni da ido kina kallona kamar baki taba ganina ba? "

Sai lokacin hankalina yadan dawo jikina, Ashe ina tsaye NE a bakin kofar.

Matsa mashi Nayi ya wuce cikin gidan na bishi da kallo, Don ban taba tsanmanin zan ganshi a wannan lokacin ba, Saboda rabon shi da gida an Dade Sosai.

Duk Wata Addu'a Dana sani ita na dinga maimaitawa, Don ganin baba tanko a yanzu ba abun alheri bane ba awurina, koda ya wuce sai warin Rana yake Yi, yayi furtutu kamar Wanda aka tono daga Rami, a tare dashi Babu Wani alamar Leda ko wata jaka, da za'ace Idan yayi wanka ya chanza kayan dake jikinshi. Sannan yayi kamar Wanda bashi da nutsuwa ta hankali.

Koda ya shiga gidan ya Gama yan dube dubenshi Sannan yace"wai ina Kaka NE? naga gidan alamar Babu kowa"

"uhmm............ Sunfita, basu MA Wani Dade da fita ba"

"gidan ubanwa sukaje,iyye"ya Karasa maganar tare da yin tsawa, nan take naji hankalina ya Tashi, a zuciyata nace yau na shiga uku. Shirun danayi NE yasa ya Kara Mani ihun"wai bada ke nake magana ba, kinyi Shiru kin kyaleni, Watau ga mahaukaci na maki magana koh?"

Da sauri na dago Kaina nace mashi "wallahi baba tanko bansan inda sukaje ba "
Wuri ya nema  a nan tsakar gidan ya zauna, Tareda yin wata irin muguwar hamma.

Nan kafin na Kara Cewa komai saiga yaron Dana aika ya dawo, na ansa kayan miyan Sannan nace mashi"nagode,kaji"

Na nufi hanyar kitchen Nanne naji baba tanko yace"ke Dakata, uban meye a cikin Ledar nan?"

"kayan miyan da zanyi abincin dare NE dasu"

"toh maza ki dafa abincin nan,dankuwa yunwa nakeji "

Nace mashi" toh",Sannan Nayi hanyar kitchen na Hura wuta, na daura ruwan tuwo, Sannan na jajjaga kayan miyan Sannan na Dora Miya.

Har magariba ta doso, su kaka basu dawo ba, shikuwa baba tanko,juyawar da zanyi naga yana shakar bacci Anan kasa Babu abinda yayi mashi zafi. Tunda ya shigo gidan nake mashi Kallon Wanda ya tabu, Saboda Sam Babu nutsuwa a tare dashi. Tuwo na yayi, harna kwashe, Sauran miyan ta rage,na share tsakar gidan na gyara Duk inda ya Kamata. Na zauna a kan kujera ina tunanin oho, Saboda ni Kaina banma San me nake tunani ba, ni dai Nasan zuciyata cike take da tsoron wannan mutumin dayake kwance a tsakar gidannan yana bacci.

"assalamu alaikum"daga kan da zanyi sainaga hadiya rike da kwanon abinci a hannunta.

"waalaikumussalam"na amsa Mata Sannan Nayi Mata nuni da mushiga daki, kar maganar mu ta Tashi baba tanko.

Da shigar mu daki tace "wai jidda me wannan mutumin yakeyi a giddannan" ta fada tare da miko mun abincin ban Wani Bata lokaci ba Na  amsa na faraci Don banason su kaka su dawo su iske ni inacin abincinnan.

"wai baki ganeshi ba?baban hannatu ne fah,nima dazu Kawai saigashi ya shigo gidan bayan dadewar dayayi baya gida, sai yau zai dawo"

Idanuwa ta zaro Tana kallona"kai Dan Allah, Amman Sam wallahi ban ganeshi ba, shine ya koma Haka? "

"wallahi Kuwa kema kya Gani, Ni dana ganshi wallahi tsorata Nayi, Kuma  ya hauni da fada saboda baiga su kaka a gidan ba"

"toh Fah,kedai ki bishi a hankali, kar kiyi mashi Wani abun dazai sa ranshi ya baci, Saboda gudun Karya maki Dukan tsiya."

"in sha allah,ni Duk na kosa sure dawo sure iske kayansu, Don tsoro yake bani, kamar Baya cikin hankalinshi"

"Yi sauri ki Gama Karya Tashi ya ganni a gidan nan"bayan na Gama NE, na Mika Mata kwanon, muka fito mukayi sallama da ita ta wuce gida. Na dawo na kada miyar Sannan na wuce naje Nayi sallah, na dawo tsakar gidan inason In Tashi baba tanko yaje yayi Sallah,amman ina tsoron Karya Kare da dukana Don Kuwa Nasan zai iya,kawai saina rabu dashi. Daga baya kawai saina yanke shawarar tashin shi daga baccin.

JIDDAHWo Geschichten leben. Entdecke jetzt