part 16

1.1K 61 11
                                    

Koda na shiga gida Babu kowa a tsakar gidan. Hakan yasa na wuce daki Kai tsaye,na cire uniform dina Nayi sallah Sannan na fito tsakar gida. Na dan Jira ko zanji motsin mutum amman Shiru,alamar kila kaka Tana bacci Kenan. Hakan yasani na fita na tafi gidansu hadiya,mudanyi hira.

Koda naje gidan nasu ita Kadai na iske a tsakar gida Tana zaune kan tabarma, nace "Inna fah?bata nan ne"
Tace"ta Fita taje kasuwa tayi siyayyan kayan Miya,kinsan yau baba zai dawo.. "

"Allah sarki, Allah ya dawo dashi Lafiya, wai yaushe rabon baba da gida?"

Hadiya tace"ameen,kedai Bari baba ya Dade rabonshi da gida, kullum-kullum in munyi waya dashi yace zai dawo Amman Shuru, yau dai Allah yayi zai dawo din"

Nayi murmushi nace "toh Allah ya maidoshi gida lafiya,idan ya dawo saiki kirani inzo in gaisheshi,kinji"

Tace"toh in sha Allah..." hadiya ta Kama ta kura mun ido Tana faman Kallona. Nace".......lafiya kike Kallona Haka,saikace Wanda Nayi maki karya"

"ina Kallonki ne,saboda naga duk kin firgice mun NE, ba kamar yadda na Saba ganinki Ba,kinga jiddah ki kwantar da hankalinki Don banason abinda zai dinga Tadawa kawata hankali. "

Dariya Nayi kafin nace"su kawa Manya, kinganni, Lafiyata Kalau wallahi... ,kona firgice hadiya inada Damar firgicewa Saboda Bansan me zai taso ba, Amman dai Allah ya Tsare. "

Tace"amin,in sha Allah,babu Abunda zai taso, ki kwantar da hankalinki ,kinji.. "

Nace"toh" na Dan jima gidansu hadiya kafin Nayi Mata sallama na wuce gida Don kar kaka ta nemeni, abun Kuma yazo ya zama abun Rigima,kartace na tafi yawo. Na shiga gidan zuciyata na dukan uku-uku,kamar zata fito daga cikin kirjina. "Assalamu alaikum... "Nayi sallama na shiga gidan, nan na Tarar da kaka a tsakar gidan a zaune kan tabarma, ta kunna radio tanaji,

"WA'alaikumussalam. "ta ansani ciki-ciki kamar batayi niyyan ansawa ba.a zuciyata Kuwa nace data barshi MA,basai ta amsa ba,tunda baa dole.

Na tsaya nace"kaka ina Wuni.. "

Bata ansa ba tace"ke daga ina kike? Gashi ba kayan makaranta bane ba ajikinki ballantana ince ko daga makaranta kike, ko Kuma kinje yawon da kika saba"

Nace"kaka na dawo gidan tun dazu,amman banji motsin kowa ba, shine na tafi gidansu hadiya,yanzu MA daga gidansu nake...."

"shegiyar yarinyar nan da wannan munafukar uwar tata, saina rabaki dasu inga ta tsiya, bakida aiki sai Zuwa wurinsu, kin makale kin mannewa ladidi da yarta,toh kishiga taitayinki, yau Idan nace Babu ke Babu su,ta zauna wallahi, kuma dole kibi umarnina,ehe!"

Zuciyata ce ta Fara bugawa da karfi, koh meya kawo maganar kaka tace zata rabani da Inna da hadiya Kuma?, nan dai na kokarta nace "kiyi hakuri kaka" Sannan na Tashi Na shiga daki koh cire hijabina banyi ba ta kwalo Mun kira"jiddah.."  nace Mata "na'am " na sake komawa inda take, sai cewa tayi "kin Dauka na sallamekine dazaki Kama ki Tashi ki tafi?"

Nace "kaka naga kinyi Shiru NE shiyasa na Dauka koh kin Gama maganar ne"

"Kinga Dallah Rufe Mani baki,ga wannan Kudin inaso kije ki siyo Man kayan Miya, Kuma banason kije wurin malam na bakin layi me kayan miya, kasuwa zakije Don nafison na chan"

Na amsa kudin, naira Dari ce, nace" kaka da kayan miyan malam na bakin layi da Kuma na kasuwa Duk Dayane fah,saboda nashin shima suna da kyau.. "

"Idan baki Tashi kin wuce ba,saina fasa maki Kai, kaji ja'irar yarinya kawai,nace GA inda nakeso ki siyomani kayan Miya, Kuma kina gaya mun kabali da ba'adi... "

"kiyi hakuri kaka, Amman baki bani kudin mota ba"

"kudin motar uwar WA zan baki, kinga Idan baki wuce kin tafi ba wallahi jikinki zai gayamaki.." Nayi sororo da fuska Saboda Babu abin Cewa, Kaka ta aikeni wuri me nisa Saboda kasuwar akwai nisa, kuma duk Abunda take bukata akwaishi a bakin titin anguwar Amman tace batason na wurin Saboda tsabagen mugunta, dakuma tanaso in wahala, gashi bazata bani kudin mota ba Haka zan taka inje Duk Nisan kasuwar.

JIDDAHWhere stories live. Discover now