part 5

1.4K 60 2
                                    

Asuba Nayi na Tashi da kyar,kasancewar na gaji Sosai, Haka Nayi sallar asuba Nayi adduo'i na Sannan na fito tsakar gida na tarkato Duk kwanukan da'aka Bata dayake lokacin Gari ya Fara Haske ,Kuma tsorona kada kaka ta fito ta hanani Zuwa makaranta Tunda Daman yau Monday, Kuma Daman halintane ta Saba hanani Zuwa makaranta,kuma tace Hannatu taje makaranta,kuma ita Hannatu yawon ta Kawai Tasa a gaba da bin Samari Don makaranta bawai ta Dameta bane ba,shiyasa nake ta Sauri in Gama Duk abinda zanyi Kafin ta Tashi daga bacci. Kuma ina ta Taka tsantsan kartace yau MA Nayi Mata Wani laifi Don taji dadin hanani Zuwa makaranta.

Karfe 7:30 Zuwa 8:00 yakamata ace dalibi yana cikin makaranta. Dayake makarantar government ce, bawai kullum suke tare Wanda Suka makara ba,wani lokacin MA kaka Saboda tsabar mugunta said 9:00 zata barni na bar gida,innaji makaranta Haka zansha bulalar makara. Inje class nan MA teacher din dake class Shima yayi mun Tasa bulalar. Kuma Da gayya takeyi Tunda zata kyale Hannatu ta tafi ni Kuma ta Lodamun Aikin datasan zaisa in Dade, Wanda bazan Gama da wuri ba.

Ahaka na Gama wanke-wanken kaka Kuwa da Hannatu har lokacin basu fito ba.bayan na Gama Sharar gidan sai GA kaka ta Tashi. Ta fito ta tsaya a tsakar gidan sai yastina fuska takeyi.bayan ta Koma daki da jimawa NE Na je domin in gaisheta.

"kaka ina kwana" Duk da Nasan dakyar zata ansani Amman na gaisheta. Ta zabga mun Harara.

"ina ruwanki da Kwana na,ko dai Kawai tsabar munafuncin ki da kilibibi da sukayi Miki yawa" ta Fada da ihu saikace ba Safiya bace ba yanzu.

"A'a kaka, gaisuwa ce kawai"na sadda Kaina Kasa.

"tsabar kilibibi ne Kawai kaka, Don Taga munacin abu me raida lafiya"hannatu dake gefenta take wannan maganar

"aikuwa dai itama intaji haushi ta Samu Wadda zai dinga Bata kudin Tana cin me rai da Lafiya"

Sai a lokacin na fahimta me sukeci, kazace a cikin kwano an dumamoshi,suke ta faman ci.

"ha! AI yar jikan nan tawa Akwai Farin jini, su Kuwa wasu Inbanda bakin Jini abunda ke Masu yawo acikin jininsu, shiyasa Babu me Tayawa,ko dayake AI abun gadonshi akayi."

Da Sauri na dago Kaina, lallai nide Nasan Ba'a banza Wani 'da na miji zai bawa Hannatu kudi da abinda duniya ba, Kuma gadon bakin jini datake cewa Nayi, AI alhamdulillahi Tunda ina bin dokar Allah yadda ta Kamata. Daman inde zagine na Saba shanshi, na Tashi Na bar Dakin na tafi Nayi wanka na shirya domin in tafi makaranta.

Bayan na kammala komai NE saiga Hannatu ta shigo dakin.

"ke kije kaka na kira" Nayi Shiru ban Ansata ba.

"wai ba dake nake magana ba"

"inace Kunne keji koh ba baki ba ko?,Don Haka ki kyaleni, because I don't really have your time"

"kutuma!! Ni Kika Zaga da wannan harshen"

"au yanzu Duk Zuwa makarantarki bakisan banbancin in an zageki da harshe turanchi da Kuma kalma ba? "

"ke, Karfa ki Raina min wayo ,Ni Nasan zagina kikayi Saboda inma a ilimine AI na Fiki Naisa ba Kusa ba" na tsaya ina Kallon ikon Allah.

Nace "AI naga Alama tuntuni, Don Haka please can you kindly leave this room?"

Dariya na cina Amman Jira nake ta Fita inyi Abuna.

Nan ta Fita Ta bar dakin,nima nabi bayanta Saboda Kiran da kaka takeyi mun.

"wayyo kaka, jidda Tanata zagina har dake a Cikin Zagin nata"tafada Tana kakalo kuka

"zagi Kuma......" kaka ta Fada

"eh kaka, kin ganta nan, Don nace Mata tazo kina kiranki shikenan saiya Zama abin da zata zageni."

"kaka wallahi ban zage Kowa ba, Kawai don na Mata magana da harshen turanci nace ta bar dakin shine Nayi zagi"

JIDDAHOù les histoires vivent. Découvrez maintenant