part 3

1.6K 83 5
                                    

بسم الله الر رحمن الر حيم

Da hanzarinta kaka tashigo dakin har ta Kusa tuntubewa da dokar kofa.

Tana fadin "Hannatu wai meke faruwa NE? Kike ta kwalamun mun Kira haka"

"ince dai Babu abinda wannan munafikar yarinyar tayimiki koh"? Kaka ta Fara Tana hararata

Shiru Nayi ina kallonsu, Tareda jiran me Hannatu zata fadawa kakartata.

Nan Hannatu Ta tura baki zata Fara shagwabarta data Sabayiwa kaka, Kuma tare da shirin yimun Sharri Don yadda take Kallona says it all.

Inde wajen hadawa mutum Sharri NE, Hannatu ta iyashi.

Kawai saita fashe da kuka, cikin Raina Babu abinda nake ambato sai innalillahi waa'inna ilaihi raji'un, tsorona Karta fadi abinda banyi Mata ba.

"kaka Saboda nace tazo tayi wanke-wanken Chen shine ta zageni hakan bai isheta ba shine ta hada harda dukana"

"wallahi kaka idan bakiyi maganinta ba, abinda zata dinga mun saiya wuce haka"

Shiru Nayi ina Kallon ikon Allah, na Kalli kaka Wanda Takai hannu ta rike baki Cikin alamun Mamaki, "kaka wallahi abinda take fada bai faru ba, hasalima ita ta Fara tonata da fada"

"lallai NE jiddatu Watau wulakancin naki da iya shege ya Kai har kin Fara Dukan Hannatu?,lallai yuwanki ya isa yanka"

"kaka Karki so Kuma yadda take Mani magana akan inje inyi wanke wanken saikace ban girmeta b............... " Bata Bari na Karasa maganata ba ta fizgo Wanda har Kaina saida ya Sara ,Saboda karfin yadda ta jani.

"zaki Rufe mun baki ko Kuwa? "ta fada tare zabga mun Mari Mai zafi, bansan sadda hawaye yafara sauka kan kumatu na ba.at least AI ta tsaya taji side of my story,amman inaaa ita abinda Hannatu ta fada shine gaskiya.

"nide Nasan abinda Hannatu ta fadanmaki karya takeyi.... " na Fada ina share hawayena.

"lallai wuyanki ya isa yanka,nayi imani in ban dauki kwakkwaran mataki akanki ba, toh wallahi wataran gagarata zakiyi " kaka ke fadin haka

Hannatu ta Matso wurin kaka Tana fadin"menake gayamaki kaka, Amman kin Samata ido, sai rashin mutumci takeyi yadda Taga dama"

"nide nasan ban dukeki ba Amman Tunda kince nayi to ban yafeba"

Na wuce,zan bar dakin Amman kaka ta jawoni, tare da dukana, da Sauri na kwace Kaina daga hannunta,na kwanta a Kasa na Fara kururuwa da ihu.

"zaki Rufe mun baki ko Kuwa "Nayi Shiru Na Samu wuri na zauna gefe daya,da muka hada ido Kuwa na galla Mata Harar cewa zamu hadu,kuma haduwar ba dadi zatayi ba.

"zaki tashi ko saina Kara maki dukanda zaisa jikinki yayi tsamin tukkunna"

"zan Tashi kaka"

Haka na Tashi Nayi wanke-wanken na gyara kitchen din Sannan na gyara dakin kaka, Nayi Duk Wani Sharan gidan na gyara ko ina.

Daman nice Jakar gidan,sai inta aiki Amman kaka na Kallon Hannatu Amman bazata ce Mata ta Kama wani aikin ba.

Haka dai na cigaba da aikin, Kaina na saramun Sosai Saboda ciwon dayake Mani,yasa Na Yanke shawarar samun kaka in gayamata Bazan iya zuwa Tallah cikin ranar nan ba Saboda Kaina na min ciwo Sosai.

Bayan na kammalla komai nayi wanka,sannan Nayi sallah ta. Na nufi wurin kaka Saboda zummar in fada Mata Kaina na ciwo.

Nashiga dakinta Bata nan,saina nufi kitchen inda na Ganta tare da Hannatu,kaka na faman Daura shinkafa a wuta.

Na Karasa wurinta,sai Kawai in'ina ya kamani Saboda tsoron abunda Zai biyo baya"kaka... Dama.. Inaso zan gayamaki bazan iya Zuwa Tallah ba Banida........"ba ta Bari na Karasa ba ta hayayyako kaina

JIDDAHWhere stories live. Discover now