part 15

1.2K 51 20
                                    

JIDDAH.

Notice:Yanzu mun dawo P. O. V din jiddah.

Akan kunne na aka Kira sallar asuba hakan yasa na Tashi domin in gabatarda da Sallah ta,bayan na idar da sallah NE Na zauna na danyi lazumi da Yan adduo'i na, kafin na fito tsakar gida na Fara ayyukan da suka zaman mun dole inyisu a gidan.

Koda na Tashi Yau,alhamdulillahi nake jin jikina, babu Wani ciwo ko Damuwa a tattare dani.aikina nakeyi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, Sannan duk Wani abinda Zaisa kaka ta fito tayi Mani fada akai ina kiyayewa Saboda yau inason inje makaranta domin in nuna MA shamsiyya Cewar kurin bakinta bawai shi zaisa in fasa abunda nakeyi ba. Kuma zancen umar da bana bashi fuska Sosai Amman abinda ya faru tsakanina da ita yasa yanzu inajin zan dinga bashi fuska Idan yaso saita hadiyi zuciya ta mutu ta huta da bakin ciki.

Koda na Gama wanke-wankena gari ya Fara haske Sosai, haka yasa na dauko shara inayi harna Kawo inda baba tanko yake kwanciya Dan kwana biyun dayazo Yi gidan yana kwana.
Sai a lokacin tunanin baba tanko ya fado mun arai,na tuna tun jiya da sukayi fada da kaka ya Fita Ya bar gidan bai sake dawowa ba. Ataikace dai da alamun ba'a gidan ya kwana ba.

Na gama Sharar NE saiga kaka ta fito hannunta rike da kular Tuwon jiya,dayake basuci ba, kila shi zata dumama suci da safennan. Nidai nasan Bana cikin lissafin wadanda zasuci tuwon nan,saboda Daman bawai Tana bani abincin safe Bane ba. Inde ba Kwanan nan ba da suke shirin yimun mugunta shine suke bani abinci akai-akai. Ta wuce kitchen sai faman shan kunu takeyi, Chan itama saiga Hannatu ta fito ta wuce bayan gida da alamar wanka zatayi.

Harna Gama Duk abinda zanyi, ya zamana wanka Kadai ya rage mun inyi, Amman Hannatu kamar Tana wankan chanza fata,dan Kuwa taki fitowa gashi nikuma inata Faman jiranta. Gashi lokacin makaranta na niyar kuremun, haka na nemi wuri na zauna a tsakar gidan ina jiranta Ta fito in Shiga.

"jiddah..." kaka na jiyo ta kwalo mun Kira daga cikin kitchen, na ruga da gudu inje Don kartace na Dade, saboda ba Karamum aikinta bane ba ta aikata Hakan. Nace "kaka gani" sai Wani faman yatsine-yatsinen fuska takeyi kamar Wadda akayiwa mutuwa. Azuciyata nace kaka kenan.

"sai yanzu kikaga Daman Zuwa, tun dazu nake Faman kwala maki Kira, iye?, sai yanzu kikaji?"Shiru Nayi bance Mata komai ba Daman Nasan zaayi Haka Saboda Tana neman ta kalamun Sharri da safiyar nan, Idan kuma Nayi magana tace abakacin marantar da zanje,kuma alhalin sau daya naji ta kirani.

Da kyar na iya cewa"wallahi kaka banji bane, Amman inajin kiranki nazo da gudu"

"Dallah malama rufamun baki anan wurin, ubanwa zakiyiwa dadin baki? Nida na san halinki, wuce ki kiramun tanko,yazo ya dauki abincin shi, mayunwacin banza dashi Shima,ke Kuma ki wuce tun kafin in Kai maki duka" inde rashin mutumcine da Kuma kala Sharri kaka ta Iyashi, yanzu Kuma me nayi Mata take shirin kwayewa Dani Da safenan.

Nidai Nasan baba tanko bai kwana a gidan Nan ba, Dan Haka Da sauri nace mata "kaka baba tanko Baya nan danko ina ganin bai kwana a gidan Nan ba,kuma koda safen nan MA bai shigo ba. "

"wannan AI zancen banza NE zancen hofi, ya zaayi kice mun tanko bai kwana a gidan nan ba? Kina so kice tun jiya be dawo ba Kenan?" mamaki kaka ta bani yadda take wani tada jijiyar wuya, kamar dama ta damu da tankon bayan in banda tsana babu abinda take Nuna mashi.

Nace "eh kaka tun jiya, Amman ban sani ba koya dawo,kila kafin mu Tashi ya Kara fita....."dakatar Dani tayi ban Gama jawabin nawa ba, "ki wuce ki bani wuri Dan Allah,banason jin komai"

Ta Kara da "shikuma shegen Allah yasa daga nan ya shiga duniya karda ya sake dawomun gida yasamun ciwon kai"

Haka nan na wuce na Bata wuri Don banason abinda zaisa raina ya baci Don yadda na Tashi Na Jini da karfi a jikina bana son abinda zai batamun rai koh kadan.

JIDDAHWhere stories live. Discover now