part 6

1.1K 63 8
                                    

Da Sunan Allah Mai rahama Mai jin Kai.

*** ** *

Bayan da na Dan Jima kafinnan na Samu muryar da zan Bata ansa,da kyar na iya furta mata "eh.. Na dawo.. " jikina Babu kwari na shiga kitchen domin in ajiye Mata kayan miyan Dana siyo Mata.

Ta ansani Dani Da "toh maza aje a cire  kayan, Sannan GA abinci a kitchen kije kichi" bakina a sagale yake ina Kallon ikon allah, a nawa tunanin kodai kaka ta Samu matsalar rashin fahimtar mutane NE?, Meya faru Haka da lokaci daya Kawai zata chanzamun?

Babu yadda zanyi,kawai saina bar komai a Raina Nasan Bada dadewa na zan samo answers Dina.

Nazo zan wuce in Shiga diki NE, saina Lura da takalma a kofar dakin kaka da Kuma yar hayaniya, Wadda tun shigowata banji ba. Juyowar da zanyi muka hada ido da kaka, hararar data zabga munce yasani shan jinin jikina,kuma tamun alamun in kame bakina. sai yanzu komai ke falling into place a kaina, ashe baki mukayi shiyasa kaka ke mun wannan mutumcin,Daman ance ruwa baya tsami banza.

Koda na shiga dakin, alhaji bala ne tare da matarshi Mai suna hajiya hadiza da yaransa sadiq, Asama'u da ahmad. Wani dadi ne ya kamani Sosai,da sauri na nemi wuri na zauna kusa da asma'u, Dayake itace sa'ata acikinsu.

Na rusuna na gaidasu "ina wuninku" Suka amsa mun da fara'a a fuskarsu.

Hajiya hadiza tace mun "jidda,tun dazu mukazo akace kina makaranta, hope kina nan kalau"

"Lafiya Kalau mommy, Dayake na Dan tsaya jiran kawata shiyasa na Dan jima, ya hanya kunzo lafiya"

Ta amsa da"alhamdulillah"

Alhaji bala yace"ina fatan dai kina maida hankali a karatun naki koh"

Nace "eh, ina maidawa"

"Masha Allah"ya fada,ya Juya suna magana da matarshi.

Na juya na Kalli asma'u nace"kin Kara zama Wata katuwa wallahi,me kike ci hakane"

Dariya tayi tace"jidda ki Dena yanzu zakiga Sun Fara tsokanata..." aikuwa Rufe bakinta Keda wuya sadiq yace"wallahi jidda kinganta nan sai San jiki, ba dole ba tayi ta zabga kiba ba."

Dariya Nayi nace"ahhhhhh haba dai nifah ba haka nasanki bafah asma"  Dariya asma tayi kafin tace"dan Allah a bar topic dinnan"

Ahmad yace"munyi munyi ta Fara exercise taki, sai lalaci kawai dake damunta"

"mummy kinga sun dameni da magana koh"ta Karasa maganar Tana turo baki,dariyane yaso ya kamani.

"yar autar tawa kuke damu haka,kace zan Bata maku rai"kaka ke fadin Haka,data shigo dakin ta tsinkayi me ake cewa.

Dariya mukayi, kafin hajiya hadiza ta juyo ta kalleni kafin tayi mun nuni da in matso kusa da ita,itakuwa kaka sai zuba mun Kallo takeyi na Karna fadi komai, nan naja jikina na matsa kusa da ita tace"wai jidda meke damunki ne? Naga Duk kin rame Kuma kinyi baki, meke faruwane? "

Nace "mummy,zirga zirgan makarantace da Kuma shirin jarabawa.." ta kalleni da kyau,kawai nasan Bata gamsu da abinda na gaya Mata ba.  Tace" karya fah" nace Allah da gaske nakeyi "  tace "toh shikenan,koma menene in kin shirya gayamun kinsan ta yadda zaki sameni"

Shiru Nayi Bance komai ba.

"ina Hannatu NE,inace tare ya Kamata ace kun dawo ba. "alhaji bala ya tambaya ,zan Bada amsa Kenan kaka tayi Saurin cewa "Tana hanyar dawowa dayake na Dan aiketa NE shiyasa ta Jima Bata dawowa ba."Shiru yayi bace komai ba. Nan kaka ta Kara da cewar "dayake Bata Kaiwa dadewar Haka, danasan kuna hanya AI da ban aiketa ba"

Alhaji bala yace" toh ,Adai dinga Lura Dan Allah a dinga sa ido da kyau"

Kaka tace"inayi iya kacin kokarina"

JIDDAHWhere stories live. Discover now