part 45

4.6K 183 4
                                    

💖SAHRA💖
  Hot Love💋

45......

    Gaba dayansu bawanda bai firgita dajin kalaman samha ba , duk suka juya suna ganin Aliyu wanda ya runtsa idonsa da karfe yana ambatar "HasbunallAllahuwani'imalwakil..la'ilaha'illa'antasubhanaka'innikuntuminalzalumin.." Fashewa sukaji hajja tayi da kuka tayi kan samha tana fadin"wllh karya kike munafuka bakar mitsiyaciya , nasan wllh sharri kika masa aliyuna bazai taba kula mace i'rinki ba..wllh saikinci ubanki da duka kinfadi gaskiyar wanda yay miki ciki.." Duka hajja tafara kaimata tana dausar cikin nata, da kyar  likata yazo ya riketa yana bata hakuri, don kowa suman tsaye yayi bamai i'ya tabuka komai. Da kyar abba ya'iya bude bakinsa dayayi masa nauyi ya kalli aliyu dahar lokacin idonsa a runtse yace"ka fadamin gaskiya tsakaninka da Allah ya abun yake son!?." Sai a snn yabude idonsa dasuka koma kamar gaushi ya saukesu akan samha data kura mishi ido tana murmushi kasa2 yanda bawanda zai kalla, ta juya idonta "tarkona yayi babban kamu..sainaga yanda za'a koreni da cikin dan gida a jikina." Tafada a ranta tanajin wani irin dadi da kwanciyar hankali da yazo mata area.  "Son ...ina jinka." Abba yay maganar yana k'ara kallon Aliyun, dawo da hankalinsa yayi kan abba yace"abba kayarda da abinda ta fada?." Daka mishi tsawa  yayi yana fadin"ya i'na mata tambaya kana dawomin da i'ta, ni sa'ankane!?." Shima tsawa yaji  hajja ta daka masa tana cewa"yazakazo kanama yaro tsawa bayan sharri da'aka masa , so kuke ku kashemin jikana ne?.." Tadaura hannuwa biyu bisa kanta tana fadin"ni Aishatu nabani zasu kashemin jika..nashiga uku."  Dafe kai abba yayi yana fadin "haba hajja..kibari a warware wnn matsalan mana.." Yafada a sanyaye cikin sigar rarrashi, juyowa yayi ga aliyu yana cewa "ina jinka!." Da kyar ya'iya bude bakinsa, jiyayi kirjinsa yay masa nauyi  sai zafi yake masa, da kyar ya'iya tattara kalamansa yace"abba ni ban mata ciki ba..shine kadai abinda nasani!."  Zabura samha tayi , ta mike tana cewa"karya kake wllh aliyu, nizaka yaudara?,,,,kaimin ciki snn kazo ka gujeni...wllh bazai taba yiyuwa ba,,Allah saika karbi cikinka." Tafashe da kuka tana durkushewa a gurin. Mami dake tsaye kamar wanda aka dasata jitake kamar zuciyar ta zai fado, wani bangaren na zuciyarta na tursasata akan ta yarda da maganar samha saboda mutanen mu na yanzu basuda  tabba, wanda kake tunani bazai aikata wani abuba sai kaga ya aikata,, yaro ka haifeshi bakasan halinshiba,,,halin dazai nuna maka daban wanda yake cikin zuciyarsa daban..lokaci daya kaddara na i'ya sauya mutum...baka taba aikata abunba amma idan yazo a kaddararka lokaci daya ka ai'katashi kuma kazo kai nadama. D'a yana i'ya kashe iyayensa..dan uwa zai i'ya kashe dan uwansa, miji zai i'ya kashe matarsa, mata zata i'ya kashe mijinta, to ba'abin yarda a duniya kenan." Dogon numfashi taja , tadago idonta dasukayi jaa tace"son!." Juyowa yayi yana kallonta a raunane , tacigaba da cewa"bazan goyi bayanka akan bakai ka aikata wnn abunba, don anan Allah ne kadai yasan gaskiyar wnn alamarin saikuma kai da i'ta, nidai shawarata a gareka kafadai gaskiyarka tsakaninka da mahaliccinka donshi zai tsaya maka , kuma shizai cire maka hakkinka akan abinda baka aikata ba akeson laka mata, indaihar bakai kayiba." Daga haka taja hanun sahra suka fita.Shiru dakin yayi sai kukan samha dake tashi tana cewa"wllh shiyamin , yace nayarda yayi zai aure ni." Ran hajja yayi matukar baci tazo gadan gadan tataka bayan samha da karfi tana cewa "shegiya nunafuka mayya dangin mayu, a gidan ubanki yay miki...to wllh duk maitarki haka zaki hakura kibarmin jikana don bazai taba aurenki ba,,kuma wnn sharin naki bai karbuba, sai kije kisake sabon shiri..mayya mai bakar aniya kawai." Takara takata . fasa ihu samha tayi tana cewa "wllh shiyamin kuma bazan yarda ba saina haifa masa abunsa." I'ta ma hajja bakinta  baiyi shiruba , bakin ciki yagama cikata sai zagin samha takeyi ,  tai gurin aliyu fuuu takamo hanun sa sukayi hanyar fita. Harsunkai bakin kofa ta juyo ta nuna abba da yatsa tana cewa "kaikuma wllh mahammadu, ka , k'ara tunkarar wnn yaron da maganar nan wllh saina sab'a maka..munafukan banza da wufi  kawai." Ta fizgesa suka fita sai bala'i take.  Ihu mom tafasa tadaura hanun ta a kanta tana cewa"nashiga uku alhj kaga yanda yaronka ya batamin rayuwar 'ya , yacuci marainiyar Allah ya gurbata mata rayuwa...nashiga uku...i'nazankai wnn balai da tashin hankali?." Harara abba ya watsa mata tareda daka mata tsawa, tsit tayi a gurin ya dafe kansa yana rasa wani irin tunani zayyi,  shidai yasan da matukar wuya ace aliyu ya aikata wnn abun, to amma yazaiyi?, dan yanzu baa shaidarsa...kumama tayaya zai tabbatar da cikin bana aliyu bane, tayaya?." Yafada can kasan ransa.  Dafashi yaji likitan yayi yana fadin"dan Allah ka kwantar da hankalinka alhj, kubar duk wnn maganganun kuje ku raini wnn cikin, daga ranar da'aka haifeshi to a lokacin ne za'asan d'ansa ne koba dansa ba...kuyi hakuri duka dan Allah,  wnn abun  nadan lokaci kadan ne komai zaizo karshe." Hakuri doctor yarinka basa yana kwantar masa da hankali harya amince, mom da samha jisukeyi kamar su goyi likitan don tsabar farin ciki..koba komai zata koma gidan taci gaba da zama, kafin lokacin kuma ya cika zasusan abinda zasuyi. Da wnn damar samha  ta kwantar da hankalinta tafara samun sauki, tareda da raya mugayen kudurirrikan cikin ranta.

Haske writer's asso💡

habiebahlurv👄

💖SAHRA💖Donde viven las historias. Descúbrelo ahora