part 8

2.8K 167 3
                                    

*💖SAHRA💖*
    *Hot Love💋*

8.....

   Bayan kamar minti ashirin  wayan safwan yashiga kara, video call ne yashigo bashiri ya dauka ganin  guards dinsa dasukaje dauko abban sahra ne, Ajiye wayan yayi yanda kowa zai kalla . da karfi tafizge jikinta daga rikon da momy tai mata tatafi gurin wayar da gudu tareda fashewa da kuka . daga daga cikin guard dinne yace "sir gashi munkarb'oshi can cikin wani jeji kuma munbasu kudin." "Yayi kyau safwan yace yana fallon abban sahra da kanshi yake akasa , juyowa yayi ya kalli sahra daketa faman kuka yayi gyaran murya yace" to alhmdllh tunda gashi ankarbo saiki fada mishi maganar damukayi." Afusace tadago da jajayen idonta tana watsa mishi harara tace "don rashin imani ko gida baizoba shine zan fada mishi."  Daure fuska yayi ba alamar wasa yace "i'dan kinmanta abinda kikamin kwanaki ni banmanta ba, kokifada mishi kokuma amaidashi yanda aka karboshi abani kudina!."  Kallon mamaki tarinka binsa dashi tana ganin rashin i'mani atare dashi waikuma ahaka zata aureshi. Ganin tana bata mishi lkc yace "inbazaki i'ya magana ba za'a maidashi, jiki a sanyaye tadago tace " abba!." Muryanta na rawa.  Karo na farko a hankali yadago ya kalleta da i'donsa wanda sukayi ja saboda zafinda zuciyarshi keyi.  Cikin kuka tafara magana tace "banida kowa sama dakai banaso inrasaka abba na, abba bamuda kudin dazamu taimaka maka dole saita hanyar safwan, hakanne yasa yanarda da aurensa domin yabada kudin  da'ake bukata. Abba nayarda zan aureshi, kuma dis coming Saturday yace yakeso ayishi.." Shiru gurin yayi sai sheshekar kukanta dake fita, a hankali abban yabude baki zaiyyi magana saikuma yayi shiru dalilin wani tunani dayazo ransa. Dan sakin ajiyan zuciya safwan yayi ganin baice komai ba its means ya amince kenan, murmushi yasaki yayiwa guards din umarni dasu karaso dashi gida yakatse kiran.  Momy kamar tadaka tsalle tayi rawa takeji , tadade tana jiran wnn rana sai yau Allah yakawo..jitakema  kamar har anyi aure angama shi.    Dan kallon site din da sahra take tayi taga har lokacin kuka take, zuwa gurin tayi ta dagota tana share mata tawaye tace "haba habibty meye na kuka kuma ayyanzu kingirma..kumama gacan abban naki ana kawoshi kikwantar da hankalinki. Fizge jikinta tayi tashige dakinta tareda banko kofa tafada gado tana kuka. Kallon safwan tayi tace " kaga saikabi yarinyarnan a hankali don wani irin taurin kai gareta." Daga kafada yayi yace "kiyi list duk wani abu dazaku bukata daga yanzu har lokacin auren saiki fadamin kudin zanturo maki. Ni zanwuce yanzu kafin sukaraso."  Jikin momy har rawa yake jin maganar kudi  tace"to shknn zanyi ..saida safe.." Baiko tanka mataba yafice driver yabude mashi mato yashiga suka tafi. Har bakin falo guards din  suka rakoshi sukaimasa saida safe ganin yanzu yazama sirikin ogansu ya kamata suyi mishi biyayya. Kofar dakin sahra yatura yaganta kwance  tafara bacci bayan kukan datayi mai i'sarta, wani tausayinta yaji ya lullubesa haka yarufa mata bargo yakashe mata wutan dakin yafita .   misalin karfe biyun dare tafarka dawani matsanancin ciwon kai da zazzabi  ko gani mai kyau  bata i'yayi, a hankali tasauko daga gadon tana dafa bango tafice daga dakin. Kofar dakin abbanta tatsaya tanagani adan bude kadan, hangoshi tayi yana salla tadan sauke ajiyan zuciya takoma batare da  tabari yaji motsinta ba.  Da asuba ma dakyar tayi  salla a daddafe takoma ta kwanta,  karfe 6 momy  tashiga kitchen tahada musu lafiyayyen breakfast cikin shauki don kwana tayi tana juyi tana murmushi har mafarki tayi suntafi dinner din auren sahra .  karfe takwas momy tagama hadawa ta jerasu kan dining tawuce dakin abba don sanar dashi angama abin kari.   Da sallamarta tashiga fuskanta dauke da fara'a tayi gurin dayake zaune kan kujera yana karatul Qur'an. Zama tayi gefenshi sai washe baki take kamar anbata kujerar makka, tsayawa da karatun yayi  yajuyo yana kallonta. "Brk d sfya mijinna, inafatan katashi lpy?." Kallon mamaki abba yarinka binta dashi don rabon datai mashi irin haka tunkafin  yarasa aikinsa ne , bayan lokacin dayarasa kuwa wani abun arziki baitaba shiga tsakanin suba. "Alhmdllh" yace mata yadauke kansa daga kallonta. Dan sanza fuska tayizuwa na tausayi tace "haba dear kamanta daduk abinda yafaru  yawuce. Yanzu kataso muje break fast is ready. Am sorry minti biyu  bari inkira sahra ." daga haka tafice daga dakin yabita da kallon shi har tsoroma take bashi wani zubin.

Masoya abin alfahari😍😍

_vote me on wattpad @habiebahlurv_

Beenaf/beelurv👄

💖SAHRA💖Where stories live. Discover now