part 12

2.9K 141 4
                                    

*💖SAHRA💖*
   *Hot Love💋*

12.....

😍😍

Karfe biyu mutane suka fara shirin fitowa daga masallaci bayan  an i'da sallan anyi addua da tunatarwa, tashi abban sahra yayi dakansa yanufi gurin alsheik  . guri suka  samu a gefe cikin natsuwa abban sahra yashiga kora mishi bayani akan damuwarsa harda dan guntun hawayen sa yak'ara da cewa "ka taimaka kadaura mata aure koma dawaye ne bayan komai ya lafa sai a raba aure, ni wancan yaron ne banaso ta aura ." ajiyan zuciya alsheik ya sauke ya dafa kafadun abba  yace" ka kwantar da hankalin ka, insha Allah matsalanka yakau..bari ina zuwa." Yafice bayan yabada umarnin kar kowa yafita sujira shi. Bayan kamar minti talatin yashigo  dawasu samari bayanshi hannyensu rike da manyan kwalaye dakuma takardu.   Lokaci daya gurin yayi shiru bayan jawabi da alsheik yafara gabatarwa cikin mintu na goma aka daura auren Aliyou Madu Indabo da Sahra Yousuf  Aliyou . Razana Aliyu yayi jin sunan da'aka ambata amma alsheik yay masa alamu daya kwanta da hankalinsa.  rabon minti da goro akayi daga haka kowa ya watse akabar alsheik.. abban sahra da  Aliyu dakuma sadiq autan alsheik mai shekaru 17.  Zufane yake ketowa Aliyu ta ko'ina jin bayanin da alsheik yake mishi , bakaramin taba mishi  rayuwarsa wnn aure yayi ba , shida baida burin yin aure yauzu ..to wama aka aura masa !?..wace irice!?,,,shin tanada duk qualities din da yake nema gun macan dazai aura ko bata dashi!?.  Dafa shoulder dinsa da alsheik yayi ne ya dawo dashi hayyacin sa "Aliyu ka kwantar da hankalinka, kadauki wnn abu amatsayin kaddara.. Kadubi wnn halin da bawan Allah nn yake ciki   ka taimaka in bayan  abubuwa sun lafa  za'a i'ya raba auren  ka auri wanda kake so. Kuma zan kira abban ka nai mashi bayani dakaina  ."  Aliyu bai i'ya cewa komai ba sai wani abu mai daci daya tadiye yafara kokarin mikewa.  Rikeshi alsheik yayi yamaidashi ya zauna yace "ka dawo da nutsuwarka mana Aliyu !,  kadawo hayyacinka."  Dago idonsa dasukayi  jajaye  saboda tsabar zafin zuciya  yayi  ya kallesu duka yace "i'na cikin hayyacina!, kawaidai abin yazomin wani kalane,, bantaba tunanin haka zata faru dani a rayuwa ta ba!."  Gaba daya sai hausayinsa yakamasu . shafa kansa alsheik yayi yace" nasani Aliyu amma kayi hakuri ..yanzu ga mahaifin yarinyar zaku tafi dashi   a yan zunnan i:nzaku koma abuja tareda matarka zaka tafi! Kuje Allah yayi maka albarka!." Daga haka alsheik yatashi yafice daga masjid din yashiga gidansa.  Jikin Aliyu har rawa yake  yagama kidime wa gaba daya baimasan abinda yakeba .  d'agashi sadiq yayi suka fita  abban sahra ma yabi bayansu batare da bata lokaci ba securities dinsa suka bude mota sadiq yasashi snn yay mishi sallama suka tada mota suka tafi bayan abban sahra ya zauna gefen driver don yin kwancen  gidansa.     Suna isowa gidan yafita yashiga da sauri harda bigewa da get ,   Aliyu baiko daga kanshi ya kalli gidan ba hasalima tunda yashiga motar kansa ke kasa maya bukatar ganin komai a yanzu.    Abba yana shiga falon ya sauke ajiyan zuciya ganin momy bata ciki, bedroom dinta yashiga yaji tana wanka dasauri yakoma dakin sahra tana kwance kan gado  idonta lumshe. Zama yayi bakin gadon yakira sunanta a hankali tashi tayi ta zauna tace "abba!."  Murmushin yak'e yayi yace "tashi kidauki hijabinki kibiyoni." Daga haka yayi gaba jiki a sanyaye tadauki hijab dinta tafito inda taga abba nn falo yakama hannunta suka fita.  Tunda taga manyan motocin dake kofar gidan kirjinta yafara bugawa da sauri2  tanajin wani tsoro na shigarta . "SAHRA! Abba Yakira sunanta kai tsaye, kallon shi tayi hawaye na taruwa idonta duk tarasa ma meyake faruwa. " kishiga motarnan kutafi!, daga baya i'nkin samu waya kikirani zan maki baya ni..yanzu ba lokaci!."  Kamar sokuwa haka tatsaya tana kallonsa i'ta duk batama san meyake cewa ba. "Kiwuce kije umartarki nakeyi!." Jiki a matukar  sanyaye kamar wanda kwai yafashewa a ciki haka take takawa, wani guard ne yafito yabude mata kofa  a hankali ta karasa zata shiga Aliyu yadaka wani uban tsawa yace "karki yadda ki shigomin mota..ka rufemin mota nace kasata wata.." Yadakawa guard din tsawa still kanshi a kasa bai kalli kowaba. jikin guard din  har rawa yakeyi yarufe motan yabudewa sahra wani tashiga suka tada motar suka tafi.   Sosea idon abba yaciko da hawaye baibar gurinba har saida yadena kallon motocin. Hade kai da gwiwa sahra tayi cikin motar tana kuka batare da kowa yajiba. "Meyake faruwa da'ine? , i'na zamuje haka?  suwaye wadannan ?.., a i'na abba yasansu?." Kukanta taci gaba dayi tana tausaya wa rayuwarta  yanda kaddaranta yazo a haka.
 
habiebah lurv &anfa novels , jameesha sadnaf novel mom of 12  hat u ol💖

View wattpad @habiebahlurv

Beenaf/beelurv👄

💖SAHRA💖Kde žijí příběhy. Začni objevovat