part 37

3.3K 154 1
                                    

💖SAHRA💖
  Hot Love💋

37.....

   Dawo da abincin yayi jin kamshi curry, ya kalla  yaga yazama yellow ya maida kallonsa kanta da yake a kasa ta maida hankalinta kan bowl din dake gaban ta cike da fruit salad, matsowa yayi dab da i'ta, ya ruko duka hanunta cikin nasa ya yalangwabar da kai kamar karamin yaro yace"baby! Kinsa curry ciki ko!?." Murmushi tayi snn ta gyada kanta tace"eh!."  Ture abincin yayi daga gabansa yace "sahhrr banason curry, bazan i'ya cin abincin ba!." Langwabar da kanta i'tama tayi kamar zatayi kuka ta kalli abincin mai rea da lafiya ta juyo ta kallesa tace"to kayi hakuri, bansani bane!." Dogon hancinta yaja yana murmushi yace "karki damu." Yafada yana daurata kan cinyarsa yana feeding dinta da fruit salad shima yana kaiwa bakinsa. bayan sun gama tare suka tattare gurin suka kai dishes din kitchen , tun daga falo ya dauketa a kafada yana mata cakulkuli sai dariya take yashiga bedroom da i'ta.  Ranar samha gagara bacci tayi, don duk a tunaninta da zarar maganin ya ratsashi ko cikin darene zai zo gurinta, amma shiru har 4 bai zoba daganan jikinta yafara sanyi tafara sake2 a ranta kila maganin baici ba, zabura tayi ta tashi daga zaunen datake a bakin gado "tace bazai yiyuba, inko har maganin nan baiyi aiki ba sainacj uwar bokan nan,,don jikina daya lallatsa bazai tafi a banza ba." Zagaye taa rinka yi har akayi sallan asuba, tashiga toilet da sauri-sauri tai wanka tafito ta shirya cikin English wears masu matukar jan hankali. Aliyu na dawowa daga masjid ya tarda ta  tana karatun alkur'an, murmushi yayi yadauki wani yafita falo shima yayi nasa. Sai karfe shida da rabi yakare karatun, ya shiga bedroom dai2 tana ninke praying mat yazo ya ruko waist dinta ta baya, ya manna mata kiss a gefen cheek dinta yace "I LOVE U!!!." Wani kalan abun taji yana mata yawo jikinta tsikan jikinta ya tashi sosea, ba'a binda takeji yana mata yawo a kwakwalwarta sa "I love u!" Din dayace. Shima kansa baiyi zaton wnn word zai fito daga bakinsa ba, gaba daya jikinsa yayi sanyi shi kansa yana mamakin ta yadda wnn abun yafito daga bakinsa. rungumota yayi jikinsa ya daurata kan gado shima ya hau ya kwanta ya jamusu bargo. Sai 7:30 suka tashi, dole aliyu yasa sukayi wanka tare bayan romancing dinta daya rinka yi, i'tade duk kunya ya rufeta a haka suka fito ya daukota kamar wata baby doll, yazo ya shiryanta cikin uniform dinta shima yay shirin office. Hanunta yakama suka tafi main house yin break. ba kowa falon sai karan AC dake tashi da kamshin airfreshner, ga dining dayake cike da manyan wermars an hada breakfast komai tsaf2. Kallonta yayi yace "kishiga gurin mami zan shiga gaida small mom." Gyada mishi  kai tayi, ba musu tace "to." Tazame hanunta cikin nasa tashiga gurin mami. da kallo ya bita har saida yaga shige wanta snn yayi murmushin , wani  irin sonta ne yaji yana shigansa a 'yan kwanakin nan , daga kansa sama yayi ya daga hannuwansa yace "ya Allah kabarni da sahhrr!, kasa tajini a ranta kamar yanda nake jinta a reana!." Ya shafa a fuskarsa ya tura dakin small mom yashiga. Kusan cin karo sukayi da samha yay baya da sauri yana kauce masa don yaga alaman fadowa jikinsa zatayi, wani mayen kallo ta rinka binsa dashi taga yayi gaba zai wuce tai saurin shan gabansa tana cewa"broda katsaya mu gaisa mana." Wani kaskantaccen kallo ya watsa mata ya rab'a tagefen ta ya wuce yana jan tsaki, dafe kirjinta dake balain dokawa tayi, tayi baya tafada kan kujera kanta na balain hargitsewa , surutu tafarayi kamar wata mahaukaciya tana cewa"indai na fatimta dai2 wato maganin nan baiyi eaki ba?" Damko gashin kanta tayi tafara fizgarsa tana cije  lips dinta kamar mai borin haihuwa. tana cikin wnn yanayin taji alamun zaa bude kofa tai saurin saita kanta, tatashi tsaye tana nufar inda yake. ruko riganshi tayi ganin har yakai bakin kofa , ta durkushe a gurin lokaci daya hawaye suka fara wanke mata fuska tace "dan Allah ya aliyu ka taimaka ka aureni koda baka sona wllh zan i'ya mutuwa a kanka, ka taimaka ka ceci rayuwa ta." Tafashe da kuka tana kara rukon dataiwa rigar tasa. Fizge rigar shi yayi da karfi daga hanunta yafice abinsa batare da yajuyo ya kalleta ba. A falon mami ya tarda ta tana zaune kusa da i'ta ta hada mata breakfast mai lafiya tana zaune tanaci hankali kwance yay sallama yashigo, murmushi yayi saka makon kallonta dayayi yaji duk wani bacin ransa ya gushe, ya karaso ya zauna gefenta sukaci tare bayan ya gaida mami. Tare suka fita akayi dropping nata a bakin skull dinsu shikuma aka wuce dashi office zuciyarsa cike da kewar matarsa!, a yanzu ba abinda yake tunowa dashi yaji dadi a ransa sama da i'ta!. lumshe ido yayi yana murmushi wanda baisan yana yiba. A fusace samha tashige dakin mom tana goge hawayen karya dake fuskanta, tashiga sai zage2 takeyi tana cewa"wnn tsinan nen mutumin bai i'ya komai ba , shege dan iska kwarto yazo ya kulla wani abun banza ya bamu yagama lallatsani a banza a wofi maganinsa baiyi aiki ba." Sake baki mom dake zaune bakin gadonta tayi tana kallonta tace "idan kingama balain saiki sanar dani abinda ke faruwa , keda yakamata ma yau inganki cikin farin ciki tunda  magani ya samu kuma na tabbata eaki yaci." Dogon tsaki ta buga ta malmalo uban ashar ta kundumawa bokan , sauri rike mata baki mom tayi tana cewa"ki rufa mana asiri samha kada boka yaji kina zaginsa, don nasan zai i'ya jiyowa." Wani bakin cikine ya kara kullanta takara kundu ma ashar tana cewa"inya fasa jiyowa yaci kan uwar sa, kina ganifa mom wnn maganin baiyi eaki ba ko kadan!, don bakiga irin wulakancin da aliyu yamin yanzu ba!." Dafe kirji mom tayi tace"nashiga uku, taya haka zata faru?." Girgiza kai mom tashiga yi tana cewa"sai dai idan baici abincin ba, amma tabbas dayaci nasan dayanzu an wuce gurin!." Naiman guri samha tayi ta zauna tana kada kafa sai huci take fitarwa , cikin bacin rea tace"lallai inkuwa bai ciba yagama dani, in bada jikina a wancan kazamin yayi wasa dashi duk don biyan bukata na, amma kuma don tsabar rashin mutunci  yaki ci ?." Fuu tatashi tafita daga dakin kamar zata tashi , ta kofar baya tabi ta zagaya part dinsa. fakan idon securities tayi tabude kofar falon tashiga, Kai tsaye kitchen tashiga ta kuwa kalli warmers din jiya wanda aka zuba abincin ciki ,   budewa tayi taga bakomai cikinsu a wanke  ta wulla gefe ta dafe kanta dake jujjuya mata tarasa gane kan wnn lamari. "shin yaci baiyi aiki bane, koko duka ma baici ba?." jitayi kamar ta daura hanu akai taita zunduma ihu ko zataji sassaucin bakin cikin dake damunta cikin ranta. Tafi minti goma a gurin snn taja kafarta tafice daga part din takoma nasu. Girga2 mom tarinka yi cikin dakin tana nema musu mafita, kamar wanda ta tuna wani abun ta dawo gefen samha ta zauna ta dafa shoulder dinta tace"ki kwantar da hankalinki, natuno wani malami wanda yake eaki kamar yankan wuka, Don shiyamin eaki akan auren alhj, ki kwantar da hankalin ki..yanzu ma mantawa nayi dashi." Ta karasa maganar tana daukar wayar ta tai dailing no din abba. Bugu biyu ya daga , cikin kidima mom tace "alhj yanzu akamin waya cewa aunty i'ya ba lafiya zanje in ganta." Cikin kulawa abba yace "ayya Allah yabata lpy, saikin dawo."  Ta katse wayar tayi tana murmushin nasara . mayafinta kawai ta dauka da handbag takama hanun samha suka fice.  Wnn karon kam a cikin abuja gidan yake, gidane mai kyau babba yasha flowers driver yatsaya kofar gidan suka fita suka shiga, don haka gidan yake ba mai gadi saboda na kowa da kowa ne. A babban falon sa suka samesa zaune ya daura kafa daya kan daya , bawani babba bane don bazai wuce shekaru 45 ba yana kallon mom yasaki murmushi yace "Ashe zaki dawo!." Murmushi tayi suka zauna sai bin samha yake da kallo gaba daya tagama tafiya dashi,, duba da irin dressing din dake jikinta mai matukar tada hankalin namiji.

Naso nai maku wanda yafi haka amma bansamu lokaci ba.

View wattpad @habiebahlurv.

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*
_(Home of expert and perfect writer's)_

Beenaf/beelurv👄

💖SAHRA💖Where stories live. Discover now