part 13

2.7K 157 2
                                    

*💖SAHRA💖*
   *Hot Love💋*

13......

    Wani abu mai daci Alh Madu Indabo ya hadiye Jin abinda yayan nashi yace, "to ..Allah ya sanya alkhairi." kawai yace ya ajiye wayar. Gaba daya hankalin mutanen gurin yatashi so kawai suke suji abinda yake faruwa ,,, kasa jurewa mami tayi  ta zauna gefen shi tareda dafa shoulder dinsa tace "dear meyake faruwa wai? , naga gaba daya kashiga damuwa." Still shiru yayi baice komai ba don baima san ta inda zai fara musu bayani ba. Baby dake gefen shi zaune tarushe da kuka harda birgima tace "abba kafadamin abinda ke faruwa, ko wani abu yasamu yayana.." Kuka tarinka yi harda tsalle kamar wata karamar yarinya . kamota abban yayi yazaunar da i'ta kan cinyarsa yace "stop crying baby na,   ba abinda yasamu yayanki yana cikin koshin lpy.."  "To abba kafad'a min abinda yafaru." Tafada tana kokarin fashewa dawani kukan , saurin rungumo ta yayi yace "karkiyi kuka zan fada maki .." Kollon mami yayi da hankalinta yaba daya ya tattara yakoma kansa haka small mom da samha dasuke tsaye. "Abbey yakirani yacemin ya daurawa Aliyu aure! Yanzu haka yana tafowa tareda matarshi!.   Wani uban tsalle baby tayi tasaki ihu tana rawa tana cewa " it's finally over alhmdllh yau yayana yayi aure yeeee..."  Tafice da gudu waje tana rawa .  samha dake tsaye  gagara daukanta kafafunta sukayi tanemi guri ta zauna  kanta yana bala'in juya mata " taya haka zata faru!?, wnn wani irin munafurci ne Aliyu zaiyi aure bayan yasan i'rin son datake masa! ...to wama ya aura!?, wace shegiyarce ta!?,,, tabbata asiri akai mishi ya aureta ...to koma waye lalle ta d'ibama kanta .. saitayi dana sanin  shigowa rayuwarsu!."  Mami dabata ma fahimci abinda abba yafada ba kawai sai kallon shi datakeyi.  "Hajiya maryam nace maki Aliyu danki an mishi aure!." Yafada yana dan hura mata iska a ido don irin kallon datake mishi. Ajiyan zuciya ta sauke tace "kace Aliyu yayi aure ko ?." Gyada kai yayi yana tabbatar mata da maganar "to Allah yasanya alkhairi." ..tashi tayi ta wuce bedroom dinta donyin bacci ko Allah zaisa kanta yasaki don tafahimci  inda maganar abba ta dosa ..don kamar almara haka take ganin abun.  Shima abba tashi yayi yafita yabar small mom da samha i'tama data tashi fuuu kamar zata tashi sama tashige falonsu tareda banging kafo.  Bayanta small mom tabi aranta tana cewa " ko wace wnn miskilin ya aura sai Allah. "  tadaga kafada tashige.  Samha bedroom dinta tashiga tarufe da key ta hautsina gashin kanta tana kaiwa da kawowa   zufa nata keto mata gaba daya tagama daukar zafi. "Ni Aliyu zaiwa haka?, watoma don tsabar bura'uba da muna firci ba anan akai auren ba don karmuji ko? saidai akawo mana amarya ... " murmushin dayafi kuka ciwo tayi tace "lallai Aliyu zaka had'u da bala'i dakuma tijara irin tawa..muzuba mugani !..."  Daga haka tabude fridge tasha ruwan sanyi amma dukda haka bataji sanyi a ranta ba.  Baby tana nan waje ta dasa kujerarta setin get yanda zata hango duk mai shigowa  , bayanda abba baiyi da 'itaba amma fir taki shiga ciki tace saitaga dawowan yayanta.  Securities da soldiers din gidan sunyi matukar mamaki jin abinda baby tace "wai sir Aliyu got married"  kowa da irin tunanin dayake a ransa na mamaki.      Har abba yaje masallaci sallan magrib ya dawo baby na nan zaune, girgiza kai kawai yayi yay shigewarsa apartment dinsa.  Karfe 8 dai2 motoci suka fara horn  megadi yafara kiciniyar bude get... A guje baby ta tafi lokacin data i'sa  harsun gama shigowa ko parking basu gama yiba tafara leka motocin   tanaga tayadda zata hango amarya . turus tayi ganin wata mace  mai katon hijab kanta sunkuye ba'a kallon fuskanta, mamakine yakamata aranta tace "badai wnn ce matar yayana ba?, nayi tunanin zanga big gal wayayya wanda tacika mace ...amma ai wnn bata fini bama..." Saurin katse tunaninta tayi ganin Aliyu yafito yana neman wucewa, dasauri tai gurinshi ta rungume shi tace "yayana barka da dawowa, nd Congratulation!."  Kafin yace wani abu gaba daya ma'aikatan gidan sunyo gurinshi suna mishi "congrate!." Ko wanne fuskanshi dauke da faraa , gagara cewa wani abu yayi sai murmushin yak'e da yakeyi yana daga musu hanu. "Yayana warcanne amaryar tamu.." Tafada tana nuna sahra dake can nesa dasu kanta sunkuye kasa.  Kallon gurin datake yayi yaga dogon hijab din jikinta amma baiga fuskanta ba , wani kululun bakin cikine yaji ya kamashi "wai wnn abun aka aura min!?."  Tsaki yayi cikin ransa azahiri kuwa yayi murmushin yak'e yace "eh!.." Ganin yanda baby takafeshi da i'do ..daga haka yay wucewarsa batareda yabari kowa ya bishi ba.   Takawa inda take baby tayi ta rungume ta tace "barka da zuwa amaryar yayana, i'na fatan zakiji dadin zama damu!."   Gagara cewa komai sahra tayi sai jikinta dake rawa  don kowama rsarinshi take agurin "wannnan wani irin al amari ne!." Tafada cikin ranta.  Ganin haka baby tace "kikwanta da hankalinki ,,kisaki jiki damu kinga ba'abinda zamuyi muki. " tai maganar tana kama hanun ta suka shiga ciki.

Duk maison SAHRA daga farko yama wa dannan numbers magana: 08030865816 or
07035668210

View wattpad @habiebahlurv

Beenaf/beelurv👄

💖SAHRA💖Where stories live. Discover now