GAMON JINI 104

211 11 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽
                   *GAMON JINI*
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
(together we stand and succeed)

1⃣0⃣4⃣

Da asuba da qyar ta tashi ya taimaka mata ta taka zuwa toilet tayi wanka,wankan shima yayi suka fito,wata doguwar riga mara nauyi yadauko mata ya saka mata,hijabin jiya ya miqa mata ta karba,ya jasu sallar asuba,bayan sun idar da qyar ta tashi ta koma kan gadon don wata iriyar kasala da take ji a jikinta,tana kwanciya kamar jira take wani baccin yayi gaba da ita,tashi yayi daga inda suka yi sallar shima ya kwanta a kan gadon,fuskarta yake kallo wani irin sonta yana ratsa jini da jijiyoyin jikinsa,kwanciya yai shima ya koma bacci.

Qarfe 9:00 daidai ta tashi,jinta tayi a jikinshi,a hankali ta zame ta shiga toilet,ta dade a toilet din kafin ta tashi tayi wanka,bayan ta gasa kanta da ruwan dumi,ba abinda yake damunta sai dan slight pain a qasanta,hakan yasa tafiyarta ta dan canza,cikin lallabawa ta fito daga toilet din,sai a lokacin taga yadda dad ya narka mata dukiya a bedroom din,wardrobe din ta bude taga kayan lefenta ne wanda dama an riga an dinka,rasa wanda zata dauka tayi,da qyar takai hannunta kan wata atamfa super sheraton red colour,a tsanake ta gama sa kayanta don tasan bacci yake yi,parlor ta fita,anan ma qara sakin baki tayi data ga yadda aka qawata mata parlon sosai,farin ciki sosai tayi da Allah ya bata madadin uba a duniya,zagaya gidan ta cigaba dayi dukda da ba wani girma ne dashi ba.

Tun fitowarta daga toilet ya tashi daga baccin,lamo yayi cikin blanket har ta gama shiryawa ta fita,tashi yayi shima yai wanka,kasancewar ba kayanshi a dakin ya fito daga shi sai towel dinta,ita da zanin atamfar data sa jiya ma tayi wankan,don bata saba da towel din ba ma,a parlor ya sameta kan doguwar kujera ta kwanta kamar mai bacci,tsayawa yayi yana qaremata kallo,alama taji kamr mutum tsaye a kanta,kanta ta dago suka hada ido,saurin dauke idonta tayi ta tashi ta zauna a hankali ta furta

"Ina kwana" 

knocking din qofar gidan aka fara yi,saboda haka bai tsaya amsa gaisuwarta ba yai saurin shiga daki ya zura jallabiya ya fito,fita yayi daga dakin yaje qofar gida ya bude,khadija,sameerah,nabelah da rukhy ya tarar,a tare suka dan rissina

"Ina kwana yaya"

"Lafiya lau sisters"

sakin qofar yayi hakan ya basu damar shigowa da kayan food flask din dake hannunsu,suna shiga cikin parlon fadeelah ta gansu,tashi tayi zata ruga da gudu taji qasanta ya amsa,daurewa tayi ta qarasa wajensu da murnarta don kada su fahimci komai,shi gogan ma tuni ya shige daki,kan dining suka jera mata warmers din suka dawo suka zauna,mommah ta fara tambayarsu da sauran mutanen gidan,ko minti goma basuyi da zama ba suka miqe da niyyar tafiya,marairaice fuska tayi tana riqonsu su zauna,rukhy ce tace

"Mommah tace minti 30 ta bamu,don haka kinga tafiyarmu,ai zamu dinga zuwa miki akai akai"

don dole ba don taso ba ta barsu suka tafi,suna fita shima ya fito cikin shigar shadda ruwan qasa dinkin boda,yayi kyau sosai sai zuba qamshi yake,taji fitowarshi amma bata daga kai ta kalleshi ba,har inda take ya qaraso,hannunta ya riqe ta miqe tsaye,ganin yadda take tafiya ne yasa ya daga ta chakk har dining,kan kujera ya dire ta,ita kuwa wata iriyar kunyarshi ce ta qara rufeta,muryarshi ta jiyo yana cewa

"Baby serve us"

a hankali ta yunqura zata tashi,hannunta ya riqe ya maida ita ta zauna,miqewa yayi ya nufi kitchen,plate ya dauko guda daya cup daya sai spoon biyu,da kuma serving spoon,qarasowayayi ya zauna,warmers din ya bude,daya irish chips ne,dayan plantain,dayan kuma soyayyen qwai,zuba kowanne yayi dai dai dai cikin plate din,tea ya hada a cikin cup dayan daya dauko,sai da ya gama hada komai sannan yace

"Baby bismillah"

Kan dining din ta kalla taga plate daya cup daya,kafin tayi wani tunanin ya dauko a hannunshi ya kai bakinta,bude bakin tayi kawai ya sa mata,yana bata tea din,bai ci ba sai daya tabbatr ta qoshi sannan shima ya fara ci,tana zaune ya gama cin abincin ya maida kayan kitchen,daga ta ya qara yi ya dora ta kan sitter,shima zama yayi kusa da ita ya janyo ta ta kwanta a jikinshi,ita dai kamar wata wawuya kawai jinshi take ta na biye mai a duk abinda yake,cikin dashewar murya yace

"Thank you baby for making me d most happiest man on earth,kin tabbatar min da cewar nayi dacen mata,dakon sonki da na dade inayi gashi Allah ya cika min burina na ganinki a matsayin matata,don Allah baby never let me down, *I LUV U*"

Shiru tayi sai qara lafewa datayi a jikinshi,dago fuskarta yayi suka hada ido,da sauri ta runtse idonta,cewa yayi

"Kunyar ta dawo kenan"

bata san sanfa ta qyalqyale da dariya ba,shima dariyar ta bashi ganin yadda take dariyar ya sa shi farin ciki sosai,kunenta yaje ya rada mata wani abu wanda nima ban jiyo ba,dariyarta naga ta qaru,kuma daga baya ta sa hannunta ta rungumeshi sosai.

A yinin ranar ba inda yaje,tare suke sallah a gida,da rana ma mommah ce ta aiko driver da abinci,haka da daddare,ba laifi ta dan sake dashi sosai tunda dama ta saba ganinshi,bayan sun idar da sallar maghrib ne ya shiga daki ta dauko wayarta,number mummynta tayi dialling ringing biyu ta daga,a tsanake suka gaisa,nasiha ta qara yi mata sannan ta kashe wayar,mommah ta kira itama gaisawa sukayi sannan ta kira hannan,suna cikin magana da hannan ma ya dawo dakin,sai da suka gama,ya ce

"Baby har kin fara gajiya da gidan kenan"

"A'ah,me ya faru??"

"Gani nayi tun daxu kike waya"

"Ayyah,su mommah na kira"

"Ohk yayi kyau,tashi muyi sallah"

Tashi sukayi sukai sallar isha,bayan sun idar ya riqe hannunta suka tafi daki,labari ya fara bata har ta fara mamakin surutu irin nashi,wanda bata sanin yana dashi ba,sai da yaga ta fara hammar bacci sannan ya qyaleta,kwanciya sukayi yana rungume da ita sukai bacci.

Bayan sunyi sallar asuba sun koma bacci,a cikin bacci yaji wayarshi na ringing,tashi yayi ya dauki wayar yaga sunan mubarakh yayi appearing,daga wayar yayi mubarakh cikin zumudi yace

"Man,kayi 'ya" miqewa yayi ya zauna kasancewar shi mai son yara,yace

"Wow!! Kuna asibiti kenan,ya maman baby"

"Ehh muna asibitin"

Sunan asibitin ya fada mai sannan ya kashe wayar,tashi yayi daga kan gadon,bude idonta tayi taga fitarshi,wanka yayi ya sa kaya ya dawo dakin,tadda ita yayi ta fito daga toilet,cewa yayi

"Baby zan fita,hannan ce ta haihu"

"Me ta haifa" ta tambaya cikin zumudi

"I think mace ce"

"Pls yaya zanje" ta fada tana nufar wardrobe don dauko kaya,ji tayi yace

"No ki zauna,nima bazan dade ba"

Shagwabe fuska tayi tace

"Yaya plss"

"Yi sauri ki shirya to"

Murmishi tayi tace "thank you yaya"

Zuwa yayi ya karbi kayan data dauko ya fara sa mata,ba abinda ta shafa a fuskarta,mayafi ta dauko ta yafa,ta dauko wani flat shoe ta saka,hannunsu cikin na juna suka fito har inda mota take,bude mata yayi shima ya zagaya ya shiga,suka ja sai asibitin da su hannan suke,suna zuwa an sallamesu ma suka dunguma sai gida,da gudu ta shiga ta rungume mommah tana murna,anata shagalin barka ba su suka baro gidan ba sai bayan maghrib.

Marriam mayshanu 👌🏻

GAMON JINIWhere stories live. Discover now