GAMON JINI 103

211 15 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽
                   *GAMON JINI*
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
(Dashen Allah bana mutum ba,together we stand and succeed)

_jinjina gareki *batuul adam jattko* lallai kinyi namijin qoqari kan litafin ki *DAMA TA* akwai darrusa da dama a cikin shi,masoya ku nemo *DAMA TA* Ku karanta nasan tabbas zaku qaru da basirar aunty batuul,Allah ya qara basira,ya daukaka ki,ya raya miki zuri'arki cikin addinin musulunci,i so much love you da duk en qungiyar kainuwa,Allah ya qara hada kanmu amyn_ 😘😘😘

1⃣0⃣3⃣

Washegari da safe ta tashi ta shirya cikin uniform dinta,wayarta ta dauka ta fito parlor,hanyar dakin mommah ta nufa,knocking tayi taji ba'ai magana ba,bude qofar tayi ta shiga ba kowa,hkan ya tabbatar mata tana part din dad,muqullin motar da ke kan bedside drawer ta dauka ta fito,kan dining ta tsaya,ruwan tea ta kurba kawai ta fita,har ta tada mota taga fitowarshi,ganin ya nufo motar ta yasa bata fara tafiya ba,qarasowa yayi ta sunkuyar da kanta qasa tace

"Ina kwana"

Bai amsa ba sai hannu da ya miqa mata,ganin haka yasa ta miqa mai key din hannunta,juyawa yayi ganin haka itama ta fito tabi bayanshi,motarshi ya bude ya shiga,itama ta shiga,tada motar yayi har yanxu bai ce mata komai ba,itama shiru tayi don dama tana ciki dashi na abinda ta gani a diaryn shi,har qofar skuul sukaje,bude qofar tayi ta sauka,ko qara kallon motar batai ba ta shige ciki,don in mikskilanci ne tafishi iyawa,tana shiga taji qara shigowar saqo a wayarta,dubawa tayi taga shine,ta bude

*Idan kun fito ki kirani na maida ke gida* A ranta tace" baza'a kirakan ba,ai nasan hanya" tabe baki tayi ta qarasa cikin makarantar,hall suka shiga aka fara exam,sai da ta fito ta tsaya a bakin skuul din tana neman napep,har ta samu ta shiga kenan ya qaraso don dama yasan tym din fitowarta neman magana ne yasa shi yi mata txt,bin napep dun yayi har suka zo gida yana binsu a baya,tana sauka,ta miqawa mai napep 1k,ganin motarshi ya sata kidimewa yana zaune yana jifanta da wani irin kallo,tsabar kidima kawai ciki ta shige ba tare da ta karbi canjinta wajen mai napep dinba.

Shigarta cikin gida taga anyi wa harabar gidan decoration ga kujeru an jera wajen yayi kyau sosai,jikinta ne yayi sanyi tunowa da tayi yau za'a kaita gidan aurenta,da gudu ta qarasa cikin gidan ko jinsu rukhy da suke mata tsiya batai ba,kifewa tayi a kan gado ta fara rusa kuka iya qarfinta,mai lallen da take jiranta tun daxu ne suka taso suka taho dakin don yi mata lallen kafin tym ya wuce,jin alamar kukanta yasa rukhy dago ta,da qyar ta lallasheta ta samu tayi shiru aka fara mata lallen,lallen yayi kyau sosai na amare har yafi wanda akayi mata da lokacin daurin aurensu,wayarta ce ta hau qara,tana leqawa taga shine,rukhy ce ta daga mata wayar tasa mata a kunne,daga can bangaren yace

"Kizo ina jiranki a mota" da qyar ta iya bude baki tace

"Lalle ake min" ba tare daya qara cewa komai ba ya kashe wayar,tunani ya farayi yaushe ta koyi taurin kai,murmushi yayi da ya tuna cewar duk ida yakai da bacin rai baya iya mata koda tsawa ne,juyawa yayi ya tafi harkokinshi.

Qarfe 4:00pm dai dai,tayi daidai da shiryawarta cikin wani material mai kyawun gaske purple,su rukhy da su khadija harda frds dinsu da suka gayyata ankon suma material sukayi orange,sai decoration din wajen ya tashi a purple da orange,ba wani heavy makeup akayi mata ba amma shigar tata ta fita sosai,jerowa sukayi suka fito daga cikin gidan tare da 'yan mata sun hadu har kujerar da aka tanada domin zaman ta,zamanta ke da wuya aka fara partyn,an ci ansha anyi watsi da naira,shagali yayi kyau,qarfe 6:00 dai dai aka tashi,wanka ta shiga sannan mommah ta bata wata atamfa ta saka,wasu abubuwa ta bata a kofi tasha,turaruka masu dadin qamshi ta fesa mata na jiki, na kaya, na kai ,ko ina ma dai sai da aka shafa mai nashi turaren,hannunta mommah ta riqe suka fito daga gidan,part din dad suka je,nasiha yai mata sosai akan zamantakewar aure,anan ta fara kuka har suka taso,ba'a maida ita cikin gidan ba aka sata a mota,nan kukanta ya qaru,basu tsaya ko ina ba sai qofar gidan mummynta,ba zato mummy taji suna shigowa,a gaban ta fadeelah ta tsugunna  ta qara rushewa da wani irin kuka,da qyar ta iya mata addu'a dan itama kukan takeji zai taho mata,rungumeta fadeelah tayi da qyar aka banbareta a jikin ta aka maida ita mota,ko da sukaje gidan da qyar ta fito,addu'ah aka ce tayi suka shigar da ita har master bedroom dinta,har yanxu fusjarta a lullube,da yake ba wata gayya sukayo ba,mota biyu ne,mota daya suka koma aka bar rukhy,khadija,da samira a gidan,sallar isha'i suka yi har ita da idonta yayi luhu luhu saboda kuka,sun idar da sallah ne suka jiyo sallamarshi shi da mubaraq,kafin ya qaraso dakin suka figi mayafansu sukayi waje,inda driver yake jiransu,saura ita kadai a dakin,shima mubaraq din juyawa yayi dama takura mai yayi sai ya rako shi.

dakinshi ya wuce ya canxa kaya zuwa na bacci,ledar da mubaraq ya bashi da baisan meye a ciki ba ya bude ya ga kaza ce gashashiya da yoghurt,kitchen yaje a dauko plate ya dora ledar akai,dakinta ya nufa har yanxu tana zaune inda suka barta amma ba kuka take ba,da sallama ya shiga,bata dago ba ta amsa sallamar ciki ciki,ajiye plate din yayi ya matso inda take,mayafin kanta ya dage gabadaya yanda zaiga fuskarta,qara sunkuyar da kata tayi,hannunsa yasa kan habarta ya dago fuskarta ta kalleshi

"Kinyi sallah?" Gyada masa kai kawai tayi yace

"Good,tashi kici abinci" Girgiza kai tayi alaman bazata ci ba,gani yai zata bata mai lokaci yasa hannu a kafadarta ya dago ta,hannunta yaja har kan carpet din dake gefen gadonta,zaunar da ita yayi ya bude ledar ya fara bata abaki,a kunyace take karba har ya isheta,kai ta girgiza mai,cup ya miqa mata ta karba yoghurt din ta dan kurba ta ajiye,kallonta yayi yace

"Shanyewa zakiyi" ba musu ta dauka ta shanye tas ta ajiye cup din,fara cin abincin yayi yace mata

"Kije kiyi alwala ki dawo" miqewa tayi jikinta  a sanyaye ta nufi toilet din dake cikin dakin,alwalar tayo ta fito,lokacin har ya gama cin abincin shima,hijab ya miqo mata wanda bata san a inda yasamo shi ba,zura hijabin tayi ya jasu sukayi sallah raka'a biyu,bayan sun idar ne yayi mata tambayoyi akan tsarki da asu wanka dai,dafa kanta yayi yai mata addu'a sannan ya tashi,yace

"Wanan kayan jikin naki basu dameki ba"  tabbas sun dameta amma ya zata yi?? Ji tayi ya ce

"Akwai sleeping dresses a cikin wardrobe ki duba sai ki canxa,yana fadan haka ya fita daga dakin,fitarshi ce ta bata qarfin gwiwar tashi ta canza kayan,tana gamawa ta haye gado ta kwanta,ba tafi minti goma da kwanciya ba taji shigowarshi,fitilar dakin da ta bari a kunne ya kashe, ya kasance saura bed side lamp da take bada din light,qarasowa yayi kan gadon ,tana jinshi tayi luff a kwance,a zatonshi tayi bacci,hkan yasa ya matso kusa da ita ya rungumota jikinsa,tun rana jin numfashinsa har bacci yai gaba da ita,shi kuwa scent din dake tashi ta ko ina a jikinta shi ya hanashi sakat,a hankali ya fara jin saukar numfashinta,alamar tayi nisa a bacci,yadda qamshin ke fusgarsa yaga dauriyar tashi ba inda zata kaishi,a cikin bacci taji ana taba ta,a firgice tabude ido,sai a lokacin ta tuna inda take,kuka zata saki taji bakinshi cikin nata,inda hannunshi yake kai kawo a ko wane sashe na jikinta,kasa yin komai tayi don jikinta bashi da wannan qwarin,tana ji ya dinga sarrafata ta yadda yake so,dim light din dake haska dakin ya miqa hannunshi ya kashe

*kasancewar dakin da duhu,ko tafin hannu ba'a iya gani yasa na tarkata kayana nima na fito* _asuba ta gari_

Marriam mayshanu 👌🏻

GAMON JINIWhere stories live. Discover now