GAMON JINI 3

289 17 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽 *GAMON JINI*💃🏽❤💃🏽
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

3⃣

*A* bbansu rashida ne wato malam shafi'u Wanda ya kasance yaya ga mahaifin fadeelah zaune a zauren gidanshi shi da tawagar qannensa,gyaran murya yayi sannan ya para magana

"Kamar yadda kuka sani akan maganar waccan yarinya fadee,Sauran sati 2 a kwanakin da na diba mata ko ta pito da mijin ko inyi kyauta da ita ga Wanda naga Dama"

malam hashimu ne yayi saurin cewa

"Yaya kayi dai dai,abinda ya dace dama kayi kenan a matsayinka na babba a gidannan"

" Da Har za'a zauna a zuba musu ido ita da uwarta suna abinda suka ga Dama"

Malam saleh ne ya dago kanshi ya kallesu

"Ai tun lokacin da za'ai auren wa 'yannan yaran naso a hada su,uwar tace yarinya CE"

"Ai yanxu ba tsayawa za'ayi bin takan wannan uwar tata ba,ko tana so ko bata so yarinya

''yar Dan uwanmu CE kuma mune Muke da ikon jagorantar rayuwarta"
malam shafi'u ya qara.

"Kai ana magana baka CE komai ba"  ya fada yana kallon kabiru Dan autansu

"Toh nidai malam abinda zan iya cewa shine ayi haquri abi komai a sannu,Idan kayi la'akari da mahaifiyar yarinyar nn ba irinmu bace,daga wata qasar a dauko ta aka kawo ta,kuma bata da kowa yanxu in ba wannan 'yar tata ba"

"Kuma maganar jagorantar rayuwarta da akeyi,yarinyar nn tunda aka haipe ta,ko suna Baku tsaya Kuka rada mata ba a matsayinku na iyayenta, ba Wanda yasan cinta,Shanta ko tupapinta a cikinku,saboda qasa ta rupe idon mahaifinta"

"Bayan lokacin da yake da rai ba wani gatan da bai muku ba,nidai bana goyon bayan wannan hukuncin"

Ran malam hashimu yayi qololuwar baci,kallon kabiru kawai yakeyi saboda maganganunshi sun Sosa masa zuciya

"Tunda Allah yasa ba Kaine yayanmu ba,mu haka muka ga Dama kuma babu Wanda ya isa ya hana wannan aure,sha sha sha kawai"

"Tashi ka bamu waje" inji malam hashimu

Jiki ba qwari ya mike yana mamakin hali irin na yayyenshi da suna kasa tallapawa rayuwar 'yar Dan uwansu amma yanxu suke qoqarin yin abinda zai shiga haqqinta Dana mahaifiyarta"

Yasha yi musu tuni Kan haqqin yarinyar da yake Kansu amma ko da yaushe saqon zagi ne suke binshi dashi saboda ya kasance shine qarami a cikinsu.

❣❣❣❣❣❣❣❣

*Q*amshi ne gaba daya ya cika gidan na girke girken da akewa baqin libya,jirgin da zai sauka qarfe shida na maraice ne zai sauka da su don haka tun misalin sha biyu na rana mommah da rukhy suka shiga kitchen,tun jiya ta gama  tanadar abinda zasu buqata domin yiwa mijinta abin alfaharinta abincin da yapi so,kasancewar shi baya cin abincin en aikin gidan saboda hka dk wacce take da girki ita zata shiga kitchen ta dafa was masa abincin da zai ci,miyar agushi suka soma hadawa wadda ta wadata ta da busashen kifi hade tantaqwashi sannan ta hada natural juice kala uku,na lemon zaqi,kankana da na cocumber.

bayan sallar la'asar suka para suyar wainar shinkafa,sun  kammala suna qoqarin Jere su a dining suka  jiyo shigowar abdul.

"kai yau kice su daddy da santi kenan''

murmushi mommah tayi
agogon dake hannunsa ya kalla

" mommah zamu tapi"

"Toh sai kun dawo"

Juyawa tayi ta kalli rukhy dake fitowa daga kitchen da warmers din abincin tace

" qarasa fitiowa da abincin bara in shirya"

"Toh mommah"

ta fada gami da qarasowa ta gaisheshi ta cigaba da abinda takeyi.

Bayan ta kammala Jere komai ne a dining ta nupi NATA dakin domin tayi wanka.

Mommah CE ta pito sanye cikin wani swiss lace da aka yi wa dinki sunfurin dinkin dubai ash colour da ratsin baki baki a ciki,baqin mayapi ta yapa,takalminta,jaka da agogon hannunta duk baqaqe,kasancewarta farar mace ne yasa shigar bakin ta karbe ta sosai.

Hayaniyar data para jiyowa ne daga waje ya tabbatar mata da cewar sun qaraso,bata gama tunanin ta ba tajiyo sallamar su Abdul,mubarakh da kuma alhaji umar.

A tare suka shigo cikin parlon suka zazzauna a cushions,gaishe gaishe akayi kapin nan Abdul da mubarakh suka miqe suka pita zuwa part din Abdul.

Mommah CE tacewa mubarakh

"Mubarakh kayi wanka ka dawo ga abinci a dining"

Kai ya kada gami da ficewa daga dakin.

Wanka yayi sukaje masallaci sallar maghrib sannan suka dawo cikin gidan domin cin abincin
Hira suka Dan taba da mommah bayan sun gama sannan suka miqe domin tapiya nasallacin isha'i.

Ko da suka dawo daga masallaci part din Abdul suka wuce,mubarakh ne ya zube a gado ya para baccin gajiyar hanya,Inda shi kuma ogan sai daya gama duk wasu al'adun daya saba kapin kwanciya bacci,a cikin harda zuwa yiwa mommah da alhaji sai da safe sannan ya dawo ya kwanta.

Kwanciyarshi keda wuya fuskar wannan yarinyar ya para dawomai,a lokaci daya kuma wani sashen na zuciyarsa yana fada masa bai kyauta ba abinda yayi mata,sannan abinda yaci gaba da bashi mamaki shine yadda ko magana batayi ba ko ta rama abinda yayi mata dk da bai ga alamar tsoro a fuskar tata ba

Tunanin da yai tayi kenan har bacci yayi a won gaba dashi.

❣❣❣❣❣❣❣❣
*F*adeelah CE shirye cikin uniform dinta na makarantar boko,ta pito daga daki Inda ta Tarar da kunu da qosan da ummanta ta ajiye mata,a nutse ta zauna kan tabarmar ta para cin abincinta har ta kammala sannan ta nupi kofar dakin ummanta.
Samun ta tayi a zaune tana qulla kayan su barkono da citta data ke siyar wa

"Umma zan wuce"

"Toh fadee,Allah ya bada sa'ah"

"Amyn "

tace tare da juyawa ta fice daga Gdan.

Tafiyarta takeyi ta dau hanyar bakin titin unguwarsu ta gandu domin samun motar gwamnati da take kaisu makaranta,qarasowarta bakin titin yai dai dai da zuwan motar, ta hau  ta zauna suka dau hanyar sharada.

Sun qaraso sharada Inda motar ta ajiyesu a bakin titi ne,suka yo ayari domin shiga cikin unguwar da makarantar tasu take ta G G S S sharada.

Gabanta ne ya para faduwa da ta zo dai dai titin da wannan mutumin ya kusa bigeta kuma ya zageta,

kamar ance ta juya ta hango motar jiyan tana tahowa,sauri ta qarawa tapiyarta

Acikin saurin datakeyi ne ta hau titin zata tsallaka,

ba tare da tasan motar tazo dab da ita ba
Burki ya taka da qarpi Wanda ya jawo hankalinta zuwa wajen,

gabanta ne ya tsananta faduwa,takai idonta kan motar amma da mamakinta ba na jiya bane ya pito daga motar.

Marriam dianah👌🏼

GAMON JINIWhere stories live. Discover now