GAMON JINI 45 to 50

224 14 3
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽
                   *GAMON JINI*
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

_This page is dedicated to all members of kainuwa writers association_
*Batuul adam jattko,maryam lawal mk,mom ayman,maman twins,stylish,aysha machika,jamila sama'ila and others da banyi mentioning ba*   _ana mugun tare_🤝🏻

4⃣5⃣ to 5⃣0⃣

Abincin ya debo yakai bakinshi daidai lokacin da wayarshi ta dau qara,ganin mommah yasa ya maida abincin cikin plate ya rupe ya tashi ya pita zuwa part din mommahn,yana shiga dining ta nuna mai,kai tsaye ya nupi can,waina ya gani exactly wacce ya baro a dakinshi (abinda ya paru shine,lokacin da saleema take girki khadija ta shigo wajen mommah,ba tare da tasa komai a ranta ba ta bawa mommah labarin yadda sukai da salima akan dafawa abdul abinci,hakan ne yasa ta tashi tayi wainar)

Yayi mamakin ganin irin abincin a wajen mommah,amma sai yayi tunanin shine dai khadijan ta kawo mata,a haka ya gama cin abincin ya pita,yaje part dinshi ya dauki coolers din abincin ya miqawa masu gadi.

Shiryawa yayi ya pita yaje ya siyo dk wasu abubuwan da za'a buqata na abinci ya nupi unguwar su fadeelah,sai da yaje sannan ya tuna ma baya son ganinta saboda samun kwanciyar hankalinsa,yara kawai ya samo yasa suka shiga da duk kayan abincin cikin gidan sannan ya hau motarshi ya tapi.

A hanya ne ya kira mubarakh ya fada mai ya kai kayan amma yara kawai yasa suka shiga dashi,ya rage nashi ya fada mata cewar shi ya aiko aka kawo.

mubarakh ya gama duk wani shirye shiryen da ya kamata yayi domin para zuwa office,a lokaci daya kuma kullum yana tare da gimbiyar tasa a waya.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Yau ta kama ranar laraba,mubarakh yana cikin pasinjojin da suka sauka a kano daga abuja,abdul ne yazo daukar shi a airport kallo daya mubarakh yamai,yace

"Abdul baka da lapiya ne??"

"No,lapiyata lau,me ka gani??"

"Kai baka ga yadda ka rame ba,me yake damunka??"

"Ba komai"

Qyaleshi yayi amma badon ya yadda ba,kuma yaci alwashin cewar sai ya nemo mai yake damun dan uwan nashi,tapiya sukeyi akan hanya abdul yana mai bayanin abubuwan da yayi na bikin kapin ya dawo,a haka suka iso gida suka je part dinsu,ya huta sannan sukaje part din mommah suka gaisheta suka pito

"Yauwah,abdul ka rakani wajen fadilah mana"

"Ba zanje ba"

"Ohk,no problem,sai na dawo"

Key din mota abdul ya miqa mai ya wuce ya koma daki,diary ya dauka yayi ributu ya mayar dashi inda yake.

Mubarakh kuwa unguwarsu fadeelan ya tapi,yana zuwa ya kirata a waya akan ya qaraso,pray mat ta sa mishi a zaure as usual suka zauna,sun gaisa yace mata yana soyau ya gaida umma,miqewa tayi ta koma cikin gida domin sanar da umman.

Tana dawowa suka shiga cikin gidan tare da ita,tana zaune kan kujera irin ta katakon nan qarama,mubarakh ne ya tsugunna har qasa ya gaisheta ba tare da ya dago kanshi ya kalleta ba,umma kuwa jin muryar mubarakh yasa tai sauri dago kanta,bugun xuciyarta ne ya qaru sosai amma tasan bazata taba manta wannan muryar ba,sai dai fuskar data gani ce bata santa ba,sun gama gaisawa mubarakh ya pito ya miqawa fadeelah ledar tsarabarta ya tapi,bayan ya sanar mata cewar lepenta sai an kaita gidanta.

❣❣❣❣❣❣❣❣

A cikin baqin da suka sauko yau daga libya ne hadda en gidansu hanan,ita da batai niyyar zuwa ba,takura matan da maminta tayi ne yasa ta haqura suka taho tare,duk ta rame ta qare,amma dk sanda aka tambayeta me yake damunta sai tace ba komai.

Mubarakh ne zaune a daki yana waya da gimbiya,ta shigo ,yana ganinta ya katse wayar da yakeyi ya tashi zaune,qarasowa tayi ta zauna akan dressing chair dake dakin kanta a qasa,duk cikinsu ba mai iya cewa wani komai,jin shirun yayi yawa ne yasa ta para magana

"Yanxu yaa mubarakh da gaske aure zakai ka manta dani,beside duk son da kk min,ni na tabbata ko ita wannan din baka sonta kamar yadda kk sona amma meyasa zakai mana haka??"

Shiru yayi don yasan hanan gaskiya ta fadi,baya wa fadeelah son daya ke mata amma qaddararsu ce a haka

"Hanan na zata mun gama maganar nan dake,and ni bani da ra'ayin zama da mata biyu.....

Katseshi tayi da muryar kuka

"Nima bazan iya dama da wata a gidanka ba,pls yaya mubarakh ka yafe min kaji tausayi na"

"Yanxu me kike so nayi??,in ce mata na pasa aurenta?? Ko yaya??

Ya jero mata tambayoyin yana kallon cikin idonta,miqewa tayi zata pita ya kira sunanta

"Hanan" tsayawa tayi ba tare data juyo ba,tashi yayi yaje inda take ya janyo hannunta ya dawo ya zaunar da ita

"You know bana son kukan nan ai,meyasa zaki yanke hukunci akan abinda bazaki iya ba?? Ko kin manta u said "zaki iya rayuwa babu ni,meyasa kika kasa da wuri haka?? Pls kiyi haquri ina son matata,a nawa ganin na miki adalchin daya dace"

Tashi yayi ya pita ya barta a dakin ,don bai son sautin kukanta,da ace yana da yadda zaiyi da yayi,yana sonta sosai amma ba abinda zai iya yi,he love fadeelah too.

Durkushewa tayi anan tana kuka cike da nadamar abinda tayi a baya,gashi tana gani mubarakh dinta ya kubuce mata,ya zama na wata,miqewa tayi ta fita daga dakin,yana parking lot yana hango ta,saidai tana zuwa qopar part din mommah ta yi baya baya zata fadi,da gudu mubarakh ya taho ya tareta,amma sai yaga ba alamar numfashi ajikinta,ba tare daya fadawa kowa ba ya dauke ta yakaita mota suka pita sai asibiti

❣❣❣❣❣❣❣❣

Saleema ce ta kasa zama sai zarya take tana jiran sakamako daga bangaren abdul,nt knowing dat sai dai daga bangaren masu gadi (😃 lol).

❣❣❣INTERMISSION❣❣❣

_Shin a ina umma tasan irin muryar mubarakh??_
_ya mubarakh zaiyi da auren fadilah,bayan hanan dake barazanar mutuwar sonshi??_
_ya abdul zaiyi da son fadeelah,bayan an kusa daura mata aure da qanin babanshi??_
_shin saleemah zatai nasara akan abdul ko kuwa??_

Ku biyo ni don samun amsoshin ku
Marriam mayshanu 👌🏻

GAMON JINIWhere stories live. Discover now