GAMON JINI 5 to 10

240 14 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽 *GAMON JINI*💃🏽❤💃🏽
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*
      *This page is oll urs* mum izuddeen and abideen *maryama tana godiya da kauna,Allah ya raya mana su izuddeen amyn*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

      5⃣  to  1⃣0⃣

         *S* hirya wa yayi tsap cikin wani baqin yadin kupta Wanda akaiwa dinkin abuja style,yayi kyau sosai cikin shigar tashi ya pito ya nupi mota,ya Dade a cikin motar kapin nan ya tada ta ya bar cikin harabar gidan.

Cikin yan mintinan da basu dara sha Biyar ba ya qaraso bakin titin layinsu fadeelah,parking yayi ya pito domin shiga cikin lungun da qapa,
Qarasowa yayi qopar gidan ya tsaya yana Neman Dan aike,yana tsaye kuwa wani almajiri yazo wucewa,kiran yaron yayi

"Dan Allah shiga nan gidan kace ana kiran fadila"

"Toh" yaron yace ya juya ya shige cikin gidan.

"Salamu alaikum,wai ana kiran fadila a waje"

"Inji wa??"

Umma ta tambaya

"Wani ne" yaron ya amsa

Fadeelan CE ta leko daga daki tace

"Kaje kace bata nan"
Daquwa umma tayi mata
"ungo nan"

Ta kalli almajirin

"kai je kace tana zuwa"

Dakin ta koma ita kuma tai zamanta,da auren da aka CE za'ai mata zata ji ko da Aiken da aka para yi mata??

"Zaki pito ko kuwa??"

"Gani nan umma"

Hijabi ta dauko har qasa ta saka sannan ta pito ta nupi qopar gida

A nutse ta pito ta nemi waje ta tsaya sannan tace.

"Ina wuni" kanta a qasa

"Lapiya qalau malama fadilah,an yini lapiya"

"Lapiya"

ta amsa ataqaice ba taree da ta dago ta kalle shi ba.

Shiru ne ya Dan gipta na Dan wani lokaci,mubarakh ne ya katse shirun da cewa.

"ni sunana mubarakh aleey,ina zaune a unguwar sharada,ni dan kasuwa ne,kuma Dan asalin qasar libya,ina fata kin gamsu da dan taqaitaccen bayanin da na miki''

Bata CE komai ba kamar kuma yadda bata dago kanta ta kalle shi ba.

"Ina sauraron ki"

yace yana ci gaba da kallon ta.

Shirun dai ta qara yi.

"Ya kamata kice wani abun fadeelah, amma tunda naga kamr shirun ya pi maki dadi,Ina ganin ni zan tapi domin in baki lokaci kiyi tunani gobe in Allah ya kaimu zan dawo,duk da naga ko kallo na bakiyi ba ,bare ki tantance nayi miki ko banyi ba"

Kanta ta dago a hankali idanunta suka sauka akanshi,wani faduwar gaba taji ganin Wanda ta gani dazu da safe ne da ya kusa bi ta kanta,kuma tan mamakin yadda akai yasan gidansu.

Sai yanxu na qare wa mubarakh kallo,zamu iya kiranshi giant,fari ne yana da manyan idanuwa sai kasumba da tasha gyara,take kwance  luf luf akan fuskarshi.

A hankali ta sauke idonta ,ya qara cewa

"Kina da waya??"

Girgiza kai kawai tayi,tanajin ta wani iri saboda ita bata taba tsayuwa da wani ba.

"Zan shiga gida" tace sannan ta juya da nupin komawa gida.

"nagode fadilah,sai na dawo gobe"

Kai ta gyada masa ta wuce

Ya para tambayar kanshi anya kuwa da alamun nasara??

Wani yaro ya gani yana ta wasansa a kopar gidan yai kiranshi,sannan yasa hannu cikin aljihunshi ya Ciro bandir din yan dubu daya ya bashi

"Shiga ka kai cikin gidan nan"

Karbar kudin yaron yayi,shi kuma ya juya ya tapi gida.

Zuwanshi gida yai dai dai da dawowar Abdul daga office

A tare sukai parking suka pito,Abdul ne ya kalleshi
"Hmmm,daga INA??"

"Ko dai kaje kapa gwamnati ne??"

"Kai pa ka raina ni,eh can naje,sai akai yaya??"

"Haba,koo da nace,wannan irin daukan wanka haka"

Duka mubarakh ya kai mai ya kauce

"Ince dai ka samu Shiga"

"Ina ruwanka"

A haka suka shige,sai da sukai wanka sannan suka pito suka nupi part din mommah

    ❣❣❣❣❣❣❣

*A* bangaren fadila kuwa,tana shiga gida ta zauna ta pada wa umma dk abnda mubarakh yacee mata, har haduwarsu ta dazun da safe,suna cikin hirar ne suka jiyo sallamar yaron daya shigo ya miqawa umma kudin

"Wai gashi inji wani a waje"

Karbar kudin tai tace

"Yana ina??"

"Ya tapi"

Toh zo ka karba,ta Ciro naira hamsin ta bashi,ya tapi.

"Gaskiya wannan kudin sunyi yawa,goben Idan yazo a maida masa kayansa"

A haka suka ci gaba da hirarsu har aka kira sallar maghrib,a tare suka miqe sukayo alwala suka tada sallar

Umma ta dade tana addu'ar tabbatuwar alkhairi akan lamarin yar tata.

Bayan sun idar ne fadeelah ta dauki qur'aninta da sauran littattapai ta tapi makaranta,kasancewar bata islamiyar yamma sai dare.

❣❣❣❣❣❣❣❣

*A* tare sukai sallama cikin palon mommah,a zaune suka sameta tana kallo ita da wata yar matashiyar budurwa.

Abdul ne ya murtuke fuska bayan ya gane wacce suke zaune tare da mommah.

Qarasowa sukai suka gaida mommah

Matashiyar da ake kira da salima CE ta kalli Abdul

"Ya abdul INA yini" ta pada tana wani kwarkwasa.

"Lapiya" yace a takaice ba tare da ya kalli inda take ba

Mubarakh ta qara gaisarwa,amsa mata yayi da fara'ah duk da bai Santa ba.

Salima qanwa CE ga hajiya saudat,tana shigowa part din mommah ne saboda Abdul,tana mugun sonshi tun lokacin data para ganinshi taxo gidan,tun daga lokacin ta maida gidansu gidan zuwanta sosai saboda shi,amma shi Sam baisan tana yi ba ma.

Miqewa sukai suka nupi dining Inda suka tarar da jollof din cous cous da ya sha naman kaza dakuma vegetables.

Bayan sun gqma cin abincin ne suka miqe suka tapi masallacin maghrib

A bakin qopa suka ci karo dasu khadija 'yayan hajiya saudat

" yaya INA wunin Ku"

"Lapiya lau kahadija,ya skul"

"Lapiya qalaw yaya"

"Ina su nabeel??" Ya tambayeta

"Suna daki"

"Ki turo mn shi bayan maghrib muyi game"

"Toh"

Tace sannan ta qarasa shiga cikin dakin ta gaishe da mommah sannan ta sanar da salima kiran da mummy(hajiya saudat) take mata,suka pito a tare suka bi hanyar part din mummyn.

Marriam dianah👌🏼

GAMON JINIWhere stories live. Discover now