GAMIN JINI 2

378 17 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽 *GAMON JINI*💃🏽❤💃🏽
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

           2⃣

*T* uki yakeyi acikin motarsa qirar discussion continues,ya kunna karatun qur'ani qira'ar khaleelul husary, ji kake qiiiiiiiiii! Ya taka burki,kallon yarinyar yake ranshi a bace,yayinda itako tsayawa tayi ta na masa kallon uku saura kwata

Abinda ya qara hasala shi yasa ya bude murfin motar da Sauri ya pito

"Ke wace iriyar mahaukaciya ce,ko makauniya ce ke"

"kina ganin mota tana tahowa amma kika wani taho tsallake titi,da na take ki na take banza wlh"

mtswwww yaja ysaki gami da komawa motarsa.

Tsayuwa tayi a wajen kamar an Dasa ta,tanajin saukar maganganunsa acikin kunnuwanta alokaci daya kuma ta kasa tanka masa akan cin mutuncin da yayi mata

Tayar da motar da taga yayi ne yasa tayi saurin barin kan titin tayi hanyar zuwa makarantarsu dayake Dama tana dab da shiga makarantar ne.

Anashi bangaren kuwa kai tsaye ya nupi hanyar da zata sada shi da gidansu,horn yayi mai gadi yai saurin bude qaton gate din gidan ya danna hancin motar tashi Inda ya samu guri cikin rumpar ajiye motoci dake harabar gidan

Parking yayi ya pito ya nupi part dinshi kasancewar part dinshi ne a parko ta gepe a gidan

Yana shiga kayan jikinshi ya rage ya fada toilet don yin wanka,yakai kusan minti 20 kapin ya pito dga toilet din daure da towel a qugunshi da wani qarami a hannunshi yana goge gashin kanshi.

Zama yayi ya janyo mayuka na jiki Dana gashi masu qamshi ya shafa tare da combing gashin kanshi,Closet dinshi ya nufa ya Ciro wata farar T shirt da wando 3 quarter ya saka,turare ya dauka ya fesa kadan  ya pito.

Main part din gidan ya nupa kai tsaye,ba kowa a palorn,dining ya kalla Inda yaga an jere coolers na abinci nan ya nufa ya para budewa,da shinkafa ya para cin karo(ta gidan kowa😝😝)ya bude dayan yaga pepper soup ne nakan rago,dayan kuma cabbage sauce CE data ji sauran kayan vegetables da naman rago.

Zama yayi ya para serving kanshi,takun saukowa daga bene yaji,can idonshi ya gane masa hajiyarsa wacce suke kira da mommah,murmushi ta sakar mishi shima ya mayar mata

Qarasowa yayi tai ma kanta masauki acikin qayatattun cushions din da suke zagaye da parlon

"Sannu da gida" ya fada

"Yaushe ka shigo banji shigowar taka ba??"

"Shigowata kenan na zauna cin abinci"

"Toh a gama lapiya"

Remote din TV ta dauka ta para kallo tana nn zaune har ya gama cin abincin ya qaraso inda take shima ya para kallon suna hira jipa jipa.

❣❣❣❣❣❣❣❣

*A* zaune take ta buga tagumi tana tunanin maganar da wan mahaifinta ya zo ya fadawa ummanta,gashi ummanta bata CE mata komai ba tun lokacin,kawai dai tana yawaita ganinta tana tunani.

Dafa ta taji anyi ta dago idonta ta sauke su akan ummanta

"Fadee kiyi haquri da halin da kika tsinci kanki a ciki,ki dage da addu'a,Allah yanaji kuma yana gani"

"Umma yanxu da gaske kenan kawu aure zaimin??"

"Ki yi haquri fadee,Allah ya pishi,kuma shi zai Samar mana mapita"

Haka ummanta taita bata baki har ta samu taji zuciyarta tadan fara washewa da baqin cikin da take ciki

Take maganganun wannan mutumin na dazu suka para dawo mata cikin kunnuwanta

"mtswww"

"Me yake nupi da CE min mahaukaciya"

"Mahaukaciya pa"

Abinda yapi tsayuwa a ranta knan

❣❣❣❣❣❣❣❣

*D*awowarshi kenan daga masallacin sallar isha'i part din mommah ya nupa ya Tarar da ita a zaune a parlor kan sitter,wajenta ya nupa ya zauna a qasa gepen qafafunta ya Dora kanshi akan qafarta

"Abdul ya dai" tace dashi

"Yau ka kira abbanka kuwa??"

"Ehh....daxu munyi waya yake cewa gobe suna hanya,amma jirgin yamma zasu bi"

"Maasha Allah,zasu dawo tare da Mubarak saboda wancan company din dake abuja,tunda kai kace bazaka koma abuja da zama ba"

"Ohk mommah"

         WAYE ABDUL??
*A*inihin sunanshi abdulrahman umar,mahaipinshi alhaji umar aliyu da mahaipiyarshi hajiya zainab asalinsu en qasar Libya ne.

Alhaji umar su shida ne a wajen mahaifinsu,shine babba,sai qaninshi naseer,gaddapi,zubaida,fauziyyah,sai Mubarak Dan auta Wanda yanxu sa'anni suke da abdulrahman.

Dukkaninsu suna da iyalansu sai dai mubarakh ne kawai bai kai ga yin auren ba,ya kammala degree da masters dinshi a fannin industrial chemistry amma maganar aure dai shiru,duk da Cewar shekarunsa bazai wuce 27 ba.

Kasuwanci shi ya kawo alhaji umar Nigeria Inda ya samu wajen zama a jihar kano cikin rukunin gidajen dake unguwowin sharada nndc quarters.

Matansa biyu hajiya zainab data kasance uwar gida kuma 'yar uwarshi sai hajiya saudat wacce a zamanshi a Nigeria ya aureta.

Suna zaman lapiya acikin gidan,ba mai shiga harkar wani acikin Matan gidan,sai dai yaran gidan Kansu a hade yake.

Hajiya zainab Nada 'ya'ya uku dashi Abdulrahman shine babba wanda a yanxu ya kammala karatunshi akan computer science,yana aiki a company din mahaipinshi dake nan sharada,abdulmaleek yana karatu ne a Cyprus Inda yake karantar MBBS,sai rukayyah da take S 2.

Rukayya ta tashi yarinya 'yar gata daga both parents dakuma yayyenta,amma hakan baisa sun saka mata ido tarbiyyarta ta lalace ba.

Hajiya saudat itace take da yaya biyar abdullahi, khadija,fareedah,nabeelah,sai autansu nabeel,Abdullahi tare suke da abdulmalyk a Cyprus amma shi yana degree dinshi ne akan kasuwanci.

khadijah tana S 3,fareedah tana S 1,nabeelah js 3,sai nabeel da yake js1.

Marriam dianah👌🏼

GAMON JINIWhere stories live. Discover now