GAMON JINI 80 to 85

217 11 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽
                   *GAMON JINI*
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

8⃣0⃣ to 8⃣5⃣

Washegari ya kasance lahadi,ranar da mubarakh da hannan zasu tapi abuja,dad ne yai mata komai na kayan daki, aka saka su a dayan gepen gidan.

Hannan da tuni ta gane cewar mubarakh ne mijinta amma tana mamakin yadda suka rabu,da kuma yadda har ranar daurin aure bata ga ana wani shirin biki da ita ba,rashin sanin wanda zata tambaya ne yasa ta kama bakinta tai gum 😷 rashin ganinsa tun ranar daurin auren ya dameta sosai,a wajen dinner ma gaisuwa ce kawai ta hada su.

Tun da gari ya waye take kuka,tunda tasan shirin da ake mata na tapiya abuja ne,gashi ta baro libya ba da shirin zuwa ta zauna ba,wata zuciyar ce tace mata ai zata iya komawa libya nan kusa tunda yaya mubarakh dinta ne,da haka zuciyarta tai sanyi amma bata daina kukan rabuwa da maminta ba.

Shikuwa ango da dama a shirye yake, kayanshi wanda yai pitar biki ne kadai zai dauka,don ya kai kaya abuja last zuwanshi,shiryawa yayi da wuri don suje ayi gyare gyare kapin yamma.

Bayan ya gama shiryawa ne ya tapi cikin gidan,ba wanda ya gani a parlor hkan yasa shi yin hanyar dakin rukhy,a bude qopar dakin take,ita kadai ce a ciki zaune a gefen gado da ganita she's absent minded,har ya shigo cikin dakin bata san da shigowarsa ba,sai da yakai hannunsa ya kade mata idonta sanan ta lura dashi.

Binshi kawai tayi da kallo ba tare da tace komai ba,zama yayi a kusa da ita,ya riqo hannunta cikin nashi ba wanda yayi magana sai sukuyar da kanta da tayi qasa,kallonta kawai yake yana admiring kyawunta itako qwaqwqwaran motsi ta kasa yi saboda wata kunyarsa ta ji ta rufe ta,shagala yayi da kallonta har ya manta da abinda ya shigo dashi gidan wajen mommah,shigowar mami dakin ne duk yasa su dagowa suga mai shigowar,yana ganinta ya miqe ya nufo ta yana sosa kai,gaisheta yayi ita kuwa murmushi kadai tamai ta amsa gaisuwarsa ya fita daga dakin.

Wajen mommah ya tapi,knocking qopar dakin yayi ya tsaya yana jiran ta,jin qarar bude qofan ne yasa ya kai idonshi wajen,fadee ya gani sabanin mommah,murmushi ya sakar mata tace

"Yaya ina kwana"

"Lapiya lau gimbiya,mommah fa??"
"Sun fita ita da umma"
"Ok,ina rukhy??"
"Itama ta fita karbo dinki"
"Toh" yace ya juya ya fita ya koma daki,duk ya damu saboda ganinta da yayi daxu suka zauna tare yaji dadin moment din sosai,tunanin halin da hannan take a libya da frnds dinta ne ya fado mai,take ranshi ya baci sosai

"Yanxu haka ma ta riga ta bawa wani banxan kanta"  zuciyarshi take fada mai,kawar da zancen yayi don yanxu ya aureta ko bai sameta yadda yake so ba zai zauna da ita tunda yana sonta.

Sai wajen 11:00 am su mommah suka dawo da umma,shirin tapiya suka para yiwa hanan,amarya ta hadu duk wani abun da zata buqata sun hada mata,sai da suka gama shirinsu tsaf sannan aka aika a kirawo angon,ai yanajin kiran ya taso ya pito,shigowa yayi ya tadda su a parlor, a gefen inda yaga hanan shina ya zauna,nasiha sosai mommah da umma sukai musu tare da fatan zama lapiya,hannan kukanta take inda shi kuwa godiya yai musu ya miqe suka fito da hannan aka sata a mota,rukhy taso a tapi da ita dad yace yace su bari zasuje amma ba yanxu ba.

Lefen da aka hada da sunan na bikin fadeelah aka sa a mota driver ya kai masu abujan tunda jirgi zasu bi.

Airport drivern ya kaisu ya juyo ya dauki hanyar abuja

❣bayan sati daya❣

An gama shagalin biki,baqin libya duk sun  tapi,fadeelah da ummanta hankalinsu a kwance yake a gidan,abdul ko takan amaryar tasa baibi ba,kuma basu taba haduwa ba ko by mistake.

Dad ne ya kira abdul a waya,a lokacin yana hanyar dawowa dga gandu gdansu fadeelah,wani yaro ya tambaya ya shaida masa cewar ai tayi aure,tunanin daya taho yana yi knan dad ya kirashi,daga wa yayi ya sanar dashi gashi nan dawowa.

Yana qarasowa gida can yayi direct ya samu dad a parlor yana zaune,gaisawa sukayi ya zauna yana jiran dalilin kiran da dad yai masa,dad yace

"Abdoulrahman"

"Na'am"

"Ina son kaje ka tambayi qanwarka fadeelah,class din data tsaya a school a duba mata makarantar su rukayya kafin ku tare,ko kuma a sama mata ko SSCE ne,amma dai kaima mijinta ne duk yadda kukai deciding"

Sai da dad ya qarasa maganar sannan ya gane wacce ake nupi,don shi ya manta da ita ma

"Toh dad,za'a duba"

"Yauwa,Allah yai muku albarka,ba wata matsala dai ko??"

"Ba komai dad"

"Toh shikenan,duk yanda kukai ka fada mn sai in sa maka kudi a account dinka"

"Toh daddy,mun gode"
Ya tashi ya tapi,ji yayi yana son ganinta tunda bashi da wani hope,tunda waccan dayake so tayi aure.

Ba kowa a parlon sai motsin da yaji a kitchen,kitchen din ya nupa,a tsaye take a sink tana wanke lettuce,qarasowa yayi ya dage ya ranqwashi kanta a zatonshi rukhy ce

"Ke wane jagwalgwalon kike hada mana"

Zapin da taji ne yasa ta juyo da sauri don ganin waye meyi mata wannan aikin

_Ya tabbata ba zai taba mantawa da wannan fuskar ba a rayuwarshi,toh me ya kawo ta gidansu ne bayan an ce masa tayi aure a unguwarsu da yaje??_

Marriam mayshanu 👌🏻

GAMON JINIWhere stories live. Discover now