50 to 55

203 12 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽
                   *GAMON JINI*
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

_this page is urs,gaisuwata tai nisan kiwo daga kano ta tapi abidjan wajen_ *aunty nabeelah* _Thanks for the luv,ana tare_ 🤝🏻

5⃣0⃣ to 5⃣5⃣

Parking yayi a harabar asibitin ya dauko ta ya shiga da ita,ganin halin da take ciki ne yasa aka para bata taimakon gaggawa,yana tsaye a bakin qopa yana tunanin yadda zaiyi da hanan don bazai jure ganinta cikin wannan halin ba,ji yayi an bude qopar dakin da take ciki da sauri ya tapi

"Doctor ta farfado??" Ya tambaya cikin tsananin tashin hankali,kallon shi likitan yayi yace

"Calm down,ta farfado amma bacci take,ko zamuje office ina son magana dakai" bin bayanshi kawai yayi har suka isa office din suka zauna,likitan ne ya dubi takaddun dasuke hannunsa yace

"Kai waye dinta??"

"Mijinta ne" yace ba tare daya san lokacin da hakan ya pito daga bakinsa ba.

"Amma meyasa ake barinta tunani yai mata yawa,har gashi ya janyo mata hawan jini sosai" shiru mubarakh yayi ya rasa amsar da ze bawa likitan.

"Ayi qoqarin ganin an rabata da damuwa domin tsira da rayuwarta,mun mata allurar bacci,yanxu haka baccin take"

"Toh doctor xan iya ganinta??"

"Yah,surely"

"Thank you" yace ya tashi ya nupi dakin da take,yana shiga ya ganta kwance tana bacci fuskarta tayi fayau,abinka da farar mace,dogon gashinta ya kwanta akan fuskarta ta inda ba'a ganin rabin fuskartata,bacci take a kwanciyar hankali,qarasawa yayi ya tsugunna a bakin gadon yana qare mata kallo,lokaci daya kuma yana jin yadda qaunar ta take ratsa cikin jikinshi.

Ko me ya tuno?? Da sauri ya tashi ya pita daga dakin,wayarshi ya zaro ya fara dialing numbern abdul,sai data gama ringing ta tsinke bai daga ba,qara kira yayi amma still no answer,bashi da wani zabi sai na kiran mommah ya sanar dasu suna asibiti da hanan amma yana tsoron susan halin da hanan din take ciki,bai gama tunanin ba ya ji wayarshi na ringing,a zatonshi abdul ne amma sai yaga mommah,daga wayar yayi daga can tace

"Mubee kna ina??"

"Ina asibiti ni da hanan"

"Alhmdlh" mommah tace

"Dama tun daxu muke nemanta,bamuga inda ta shiga ba,me kuke a asibiti??"

"Itace ba lapiya"

"Subhanallah,wane asibitin"

"Kwatancen asibin yai mata ya kashe wayar,wayar abdul ya qara kira shiru bai daga ba.

Dakin da hanan take ya koma,ya zauna kan kujerar roban dake gepen gadon,bude qopa yaji anyi,mommah ce da mamin hannan suka shigo

"Mubee mai ya sameta??" Mommah ta tambaya tana qarasawa kan gadon

"Mommah a parking lot na ganta zata shiga cikin gida sai jiri ya debe ta na tareta,da naga bata numpashi shine na kawo ta nan"

"Toh me sukace likitocin??" shiru yayi,mamin hannan ce ta daka mai tsawa,
"Ba tambayarka akai ba??"

"Amm wai hawan jini,tana da damuwa ne"

Mommah ce ta para salati,mami kuma ta tashi ta pita "shashancin banza,damuwar meye da ita,saboda nace sai taxo nigeria biki,ta mutu ma" ta pita tana fada kasancewarta mace mai zapi sosai.

Mommah ce tace mai

"Ina abdul??"

"Nayi ta kiran wayarshi bai dauka ba"

"Ok,to tashi ka koma gida zan zauna anan,kapin ta tashi"

"Toh" yace ya kama hanya ya pita,a waje ya tadda mami,suka tapi tare.

Yana zuwa gida,part dinsu yaje ya tadda abdul yana ta bacci,zama yayi shima akan gadon yana tunanin wannan rudanin daya shigo rayuwarshi.

A can asibiti,mommah ta idar da sallah,tajiyo kamar hannan tana magana,qarasawa tayi da sauri don jin me take cewa,a hankali take magana.

"Yaya mubarakh,wallahi in ka auri wata mutuwa zanyi,ba zan iya jure ganinka da wata ba" duk maganar da takeyi idonta a rupe yake.

mamakin maganganun hannan mommah takeyi,idan ta fahimta,auren da mubarakh zaiyi ne yasa ta hawan jini,lallai da aiki don ya zama dole ta san yadda za'ayi.

A hankali ta bude idonta ta saukesu akan mommah,bin igiyar ruwan da aka sa mata tayi da kallo,hakan ya tabbatar mata cewar a asibiti take,runtse idonta tayi wasu hawaye masu zapi suna pita,duk abinda take akan idon mommah,duk tausayinta ya cika ta,pita tayi ta kitrawo likita,B.p yai mata yaga ya kusa saukowa daidai,sauran magungunan yai wa mommah bayani ya sallameta.

Tashin hannan tayi suka pito tasa ta a mota ta juya tashiga suka tapi gida.

Isarsu gida yai daidai da pitowar mubarakh domin ya koma asibiti,qarasawa yayi wajen motar,idon hannan akanshi,tare suka shiga cikin part din mommah,daki mommah ta kaita ta kwantar da ita ta pita domin samo mata abinci.

Tana pita ta samu mami a parlor,ta fada mata abinda taji hannan tana fadi,a take mami ta bata labarin soyayyarsu da cewar rashin kunya hannan taimai ya haqura har yaxo ya nemi auren wata saboda haka idan hannan zata mutu saidai mutu.

Mommah miqewa tayi ta nupi kitchen tana tunanin labarin da mommah ta bata da kuma hanyar da zata nema don mubarakh ya auri hannan.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Ranar friday ta kama ranar daurin auren mubarakh,bayan an idar daga masallacin juma'ah,dubban mutane daga tawagar alhaji umar na kusa dana nesa da kuma dangin abban fadeelah sun taru a masallacin juma'ar domin daurin auren.

Abdul ne da mubarakh sunyo shigarsu iri daya,amma da ganin abdul kasan baya cikin walwala,haka mubarakh dinma don tunanin halin da hannan take ciki ya dameshi.

A hankali mubarakh ya nemi abdul ya rasa a wajen,kwata kwata ba alamarshi.

Alhaji umar ne suna gaisawa da mutane,tun daga nesa ya hango wani kamar kabeer( autan baban su fadeelah) da sauri ya qarasa wajenshi,suka gaisa sam kabeer bai ganeshi ba,sai shine yace

"Kamar kabeer ko?"

"Ehh nine" cikin rudewa alhaji umar yake tambayar shi

"Baka ganeni ba,umaru na libya,ina mahmoud da zubaida??"

Cikin halin mamaki yake cemai

"Ai auren 'yar wajensu akeyi"

Da sauri yace kana nupin itace fadeelar da zata auri mubarakh??"

"Kwarai kuwa"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji' un,ai mubarakh qanina ne"

"Subhanallahi,rashin sani kenan"

A tare suka tapi domin sanar a dakata da daurin auren.

Marriam mayshanu 👌🏻

GAMON JINIWhere stories live. Discover now