GAMON JINI 15 to 20

221 18 2
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽 *GAMON JINI*💃🏽❤💃🏽
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

_dix page x oll urs_ *ameenatu sulayman* _thnx for the love dear_😘😘

1⃣5⃣ to 2⃣0⃣

"Ahmm dama wajen fadeelah Nazo"

"Toh in aurenta zakayi ka pito dan nan da qarshen wani satin zan Mata aure"

Mamaki ne ya cika mubarakh ganin cewar yarinya CE qarama bayan haka ma ko candy batai ba,amma da yake nan ba hurumin tambayarsa bane yasa ya haqura yace

"Inshaa Allah za'a turo"
Fitowa tayi

"Kawu tana zuwa"

Mubarakh ganin haka yai mata sallama ya tapi,fitarshi daga gidan yai dai dai da shigowar umma soron

"Ina wuni" ko kallon arziqi bai mata ba bare ya amsa gaisuwarta

"Yau Allah ya rupa muku asiri yaronnnan yace zai turo,dama zuwa nai na qara tuna miki,kuma Idan har bai turo din ba,zan bata Dan liti mai nama"

Daga haka ya juya ya pita daga gidan,fadeelah tana tsaye a gepe tana ta kuka,ita kuma umma kukan rashin mafita take,wannan yaron da kawu yace ya turo daga gani mai kudi ne kuma basusan waye shi ba,gashi baisa ayi wani bincike ba kawai yace ya turo,shi kuma danliti ba Wanda baisan halinshi ba na auri saki sannan babu cimar kirki a gidanshi.

A haka takama hannun fadeelah suka Shiga gida,ta zaunar da ita

"Fadee a kullum bazan FASA CE miki kiyi haquri da qaddara ba,saboda kowa da irin tashi qaddarar rayuwar,kuma yanxu abinda nake so dake shine ki dinga qoqari kina tashi tsakar dare kiyi sallah fada wa Allah damuwarki,tunda kikaji ya tashi maganar auren nan,toh abinda xai hana auren nan ba qaramin Abu bane,saboda haka ki dage da addu'a,Allah maji roqon bawansa ne"

A haka take rarrashinta har ta daina kuka,suna zaune aka kira maghrib umma ta tashi tai sallah,Ana idar da sallah fadeelah kuma ta dauko litattapanta ta tapi islamiyya.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Komawarshi gida ya Tarar Abdul ya dawo,zama yayi ya bashi labarin yadda sukai fadeelahn,kuma zai Sanar da dad domin su tura Neman aurenta,Abdul fatan alkhairi yamai sannan suka pito suka tapi part din mommah kamar yadda suka saba,sukaci abinci suka pita masallacin maghrib.
Bayan sun dawo daga massalacin isha ne su uku harda dad mubarakh ya shaida mishi zasuyi maganar,hakan ne yasa yace yaje part dinshi ya sameshi.

A tare suka wuce part din dad banda Abdul,zama sukai mubarakh yace

"Yaya dama akan maganar jiya CE,yarinyar iyayenta sunce a turo Neman aure,amma mahaifinta ya rasu,sai en uwanshi"

"Toh,alhamdulillah,zan yi qoqari in samu su alhaji badamasi(abokanshi) sai muje,sai ka Sanar dasu ranar juma'a inshaa Allah zamuje,Allah yayi albarka"

"Amyn,na gode yaya"

"Sai kayiwa Dan uwanka fada ko shima ya pito da tashi ayi auren"
Dariya kawai yayi ya miqe ya pito,

A bangaren Abdul kuma shidai ya rasa gane kan wannan al'amari,ba ita kadai CE macen daya para yima irin wannan abun ba,amma meyasa sai NATA ne ya dameshi,maganar mubarakh ya tuno na cewar ko Sonta yake,take wata zuciyar tai saurin amsa hakan amma shi bai San yadda ake son bama,kuma Indai wannan ne son toh zai iya yadda Sonta yake,amma ya zaiyi?? Tunda bai Santa ba,kuma baisan ta Inda zai para Neman ta ba.

Mubarakh ne ya shigo ya sameshi ya kwanta rigingine yana ta tunani,taba shi yayi sannan yasan cewar ya shigo dakin.

"Haba Abdul,yau kuma me ya paru?? Kodai tun maganar yarinyar nan ne??"

Dama mai Neman kuka ne aka jepe shi da kashin awaki,irin yadda yakejin zuciyarshi na mishi ne yasa ya miqe zaune ya jingina kanshi kan kafadar mubarakh

"Ku memo min ita pls,zuciyata ta kasa mantawa da kamanninta,don Allah Ku memo min ita,bansan a Inda zan ganta ba" maganar yake cikin muryar tausayi,yana zubar da hawaye.

"Zan bata haquri,in kula da ita kuma in mata gata yadda zata manta dk wani Bacin rai da yake Tare da ita,don Allah mubarakh ka memo min ita,itace rayuwa ta.

Rarrashin shi mubarakh yayi tayi,akan gobe zasu para nemanta yayi haquri,a haka har ya haqura ya tashi ya canxa kaya ya kwanta amma Sam bacci yaqi zuwa,juyi kawai yake yi akan gado,hakan yasa ya tashi yaje yayi Alwala ya tada sallah yana fadawa Allah damuwarshi,yana nn a zaune har aka para kirayen kirayen sallah yana karatun qur'ani,a haka har aka kira sallah ya tashi mubarakh suka je masallacin suka dawo,sannan ya Dan kwanta yayi bacci kapin gari ya waye.

Ko da gari ya waye ya tashi yaji zuciyarshi fes,bayajin damuwa sosai amma deep inside him yasan me yake damunshi,so da qaunarta ne suke nuqurqusarshi,tare suka pito sukai breakfast sannan suka wuce office,a kan hanya sukai ta hira har mubarakh yake fada mai yadda sukai da dad akan yarinyar da yakeso,kuma idan sun dawo daga office yau tare zasuje su ganta.

Bayan isarsu office ne mubarakh ya pita zuwa shagon siyar da wayoyi,infinix ya dauka hot note ya biya kudin,ya sai layi da katin 10k sannan ya pito ya koma office.

❣❣❣❣❣❣❣❣

A bangaren fadeelan ma a Daren jiya bata samu bacci ba,saboda tunanin makomar rayuwarta,kasancewar bata sallah ne yasa taita addu'o'in ta har bacci barawo ya sace ta.

Da gari ya waye ta tashi ta shirya domin tapiya mkrnta,shamsu ne yayan su rashida ya shigo gidan,babansu ya aiko shi,fadeelah ta gaisheshi shi

"Yauwah fadeelah, dama wajenki aka aikoni,baba yace wai kije yana kiranki yanxu"

"Toh,inazuwa sannan ta juya ta koma daki ta fadawa umma ta fito ta nupi hanyar gidan kawun NATA.


Marriam dianah👌🏼

GAMON JINIWhere stories live. Discover now