GAMON JINI 101

211 9 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽
                   *GAMON JINI*
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
(Dashen Allah bana mutum ba,together we stand and succeed)

1⃣0⃣1⃣

Yana fita ta koma kan gadon ta kwanta,sai a lokacin ta fara da ta sani ta ci gaba da bude diaryn ko zata yi sa'a taga ko sunan budurwar tashi che,da wannan tunanin tajiyo kiran sallah,tashi tayi taje ta dauro alwala ta dawo dakin tayi sallah,tana idar da sallar ne ta fita don ganin time yayi da za'a dora abincin dare,a parlor taci karo da 'yan biyun mommah,abdulmalyk da abdallah suna ta hira suna kallon tv,abdulmaleek ne ya kalleta yace

"Auntynmu barka da fitowa"

Abdallah da ya guntse dariyarsa ta kalla,abdualeek yai saurin cewa

"Kai kuma me kakeyi wa dariya??"

"Gani nayi kana cewa wannan yarinyar wai aunty" ya fada yana ci gaba da dariyarsa,tabe baki tayi tace

"Yaya abdallah kaima ka fada,na ce mai ya dinga fada min sunana amma yaqi"

"Toh aje ai mana girki,kinsan ko wancan mijin naki in kikai abinci sai ya gane ke kika yi shi,don kwana yake yana santi"

"Da yake ai tare kuke kwana ko??" Inji abdulmaleek

Dariya suke yi dukansu har ita,sai da ta ci dariyar ta qoshi sannan ta wuce kitchen,abdallah ne ya tashi ya bi bayanta don dama mostly in yana nan yana taya mommah wasu ayyukan don a wajenta yake cin abinci,part dinsu ma bai damu yaje ba sai gaida mummynshi kawai ke kaishi can,abinci ta dora mai sauqi sukayi komai tare da shi suka fito suna jera warmers kan dining,sai da suka gama,sannan suka fita shi da abdulmaleek don tafiya masallacin isha'i ita kuma ta shiga daki don tayi wanka.

A bangaren abdoul tunda ya shiga dakin yaga yau tabbas anyi shara amma babu wannan qamshin da yake welcoming dinshi,yasan cewar something went wrong,yana jin cewar a ranshi kukanta ba na mutuwar da tace  bane,amma he can't force her tunda bata son ta fada,duk yana rage kayan jikinshi yake wannan tunanin,wanka ya shiga,ya fito yai sallah,sannan ya kunna tv,ganin bata dan jin dadi yasa ya dau waya ya kira khadija don ta dafa mai lipton,lipton din ya zauna yana sha har aka kira sallar isha'i,tashi yayi ya tafi masallaci ya dawo, cikin gidan ya nufa,qannenshi ya tarar a parlon,sai da suka gaisa yaci abinci ya fita.

Shigarta daki ta tuno abinda yake damunta daxu don surutun abdallah yasa ta manta da halin da take ciki,ai tana yin wanka tai sallah itama,mommah taje tayiwa sai da safe don bata jin zata iya sa komai a cikinta,dn hka tabi lafiyar katifah tare da kashe wayarta don tasan sai ya kirata kafin yai bacci,bata dade ba kuwa baccin yai gaba da ita.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Washegari da safe ya shirya don tafiya office,time rable din fadeelah dake kan drawer dakinshi ya dauko,1:00am yaga tana da exam,hakan yasa ya dauki waya don ya kirata,don tun jiya wayar a kashe,kira yayi still wayar a kashe take,breakfast ya shiga gidan yayi,kofar dakin ya je ya murda ya jita a qulle,kawai ya juya ya fita,a office dinma duk hankalinahi ba'a kwance yake ba,yana ganin 9:30  tayi ya miqe ya dauki key din motarshi ya taho gida,sai a lokacin ya kira wayarta yaji ta shiga,tana ganin kiran tasan cewar ya dawo ne,dama a shirye take a uniform,tunda ta fito idonshi yake kanta har ta qaraso jikin motar ta bude ta shiga,tana shiga yana kashe motar,dagowa tayi don ta gaishe shi taji gaba daya ya rungumeta,cikin kwantawar murya yace mata

GAMON JINIWhere stories live. Discover now