GAMON JINI 65 to 70

182 12 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽
                   *GAMON JINI*
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

_wannan page din naku ne 'yan *miss marriam novels group* thanks for your support,i heart u oll,muna tare_ 🤝🏻

6⃣5⃣ to 7⃣0⃣

Dalilin da yasa alhaji umar yasan kabeer kuwa shine,bayan auren su zubaida da baipi wata daya ba,sunje libya da mahmoud,har a lokacin suna fushi da ita kuma shine zuwan shi na qarshe har ya rasu bai qara komawa ba

❣❣CIGABAN LABARI❣❣

Zubaida ce ta para basu labarin tun daga zuwanta nigeria har mutuwar mijinta,da zaman da suka yi da dangin mijinta.

mubarakh da yake zaune duk gabadaya kanshi ne ya kulle jin cewar matar da ya aura 'yar yayarsa ce wacce suke uwa daya uba daya,shi kuwa abduul bai san yadda akai akaga aunty zibaidan ba,don shi ya san sunanta sosai a wajen dad da mommah amma bai santa ba,kuma har yanxu da ake zancen nan bai san itace maman fadeelan da mubarakh ya aura ba.

Tsit dakin yayi sai kukan mommah,zubaidah da na fadeelah akeji,dad ne ya kalli mubarakh yace

"Mubarakh,kaji dai yadda al'amarin aurenka ya kasance,toh sanadin haka nai maka wani zabin a matsayina na yayanka kuma dai na tabbatar ko kai na barwa zabin abinda zaka zaba kenan,saboda hka an daura aurenka da hannan"

A tare abdoul da mubarakh suka dago suka kalli dad,kallon da abdoul ya ai na rashin fahimtar abinda yasa a ka fasa auren mubarakh da budurwarshi aka aura masa hannan at the same time kuma yana jin kamar wani chance ne ya shigo rayuwarshi na yaje ya nemi soyayarta,shi kuwa mubarakh kallon farin cikin mafitar da aka samo na aura mishi hanan yake,don a ko da yaushe yana tunanin makomar ta sbd rashin aurensu.dad ne ya juya ya kalli abdoul

"Abdoulrahman" Har cikin ranshi yaji wannan kiran sunanshi da dad yayi hakan kuma ya haddasa mai faduwar gaban da baisan dalilinta ba.

"Na'am"

"Ni mahaifinka ne,kuma nasan kai me biyayya ne a gareni,and ka tabbata bazan yi maka abinda zai cutar dakai ba" Gyada kai kawai abdoul yake,a zuciyarshi yana tunanin mai dad yamai,dad ne ya cigaba

"Hakan yasa a dazu aka daura aurenka tare da na mubarakh,na aura maka er uwarka 'yar auntynka zubaida"

Ai ba abdul kadai ba,har mommah da zubaidan sai da suka  dago rinannun idanuwansu suka kalli dad jin abinda yace,farin ciki suke,saboda sun qara hada wani zumuncin amma a bangaren abdul gabanshi ne ya dinga faduwa,sam baiso ba,amma haka ya daure yace

"Nagode,Allah ya qara girma" murmushi yayi ya kalli zubaida yace

"Allah yasa ban yi muku laipi ba dake da 'yata"

"Haba yaya,da ni da ita ai duk kana da iko damu,kuma nasan bazata bamu kunya ba,nima naji dadi sosae,Allah ya qara girma"

Abdul ne ya miqe,mubarakh ma ya miqe,dad yace

"Abdoul ko zaku je asibitin yanxu??"

"A'ah dad zan kwanta ne kawai" yace suka pita da mubarakh,daki suka wuce,suna shiga ya kife a gado,tunaninshi gaba daya ya tsaya,shi dai baisan dalilin da yasa mubarakh ya pasa aurenta ba,to wa zai tamabaya??

Kuma gashi anzo ance an masa aure da cousin dinsa,bai santa ba,taya za'ai ya sota ma,bayan wacce yake so daban.

Maganar mubarakh ce ta katse masa tunanin da yake

"Kai angon gimbiya sai ka tashi ka shirya ko??"

Wani kallo ya watsamai

"Shirin me??"

"Ooh ka mamta cewar yau ne event din bikina,kapin ya zama namu mu biyu??"

"Sai ka dawo"

"Hhh ita taka amaryar da wane angon zata??"

"Ba zan iya zuwa ba kasan banda lapiya dai ko"

"Naji" yace ya cigaba da shirinshi.

Shidai abdoul yana tunanin wannan al'amari mai rudani,toh meyasa mubarakh bai damu ba da rashin aurenta da yayi,wata zuciyar tace mai ai dama yana son hannan shiyasa,yana tunanin ne har bacci barawo ya saceshi.

_Note_ *Abdul baisan 'yar auntynshi ce budurwar da yakeso ba,kuma baisan itace matar da aka aura mai ba*_
❣❣❣❣❣❣❣❣
Su mubarakh na pita dad ya kalli fadeelah

"Fadeelah" kanta ta dago ba tare da ta amsa ba yace

"Taso kixo nan 'yata" ya fada yana nuna mata dayan gefenshi.

Tasowa tayi a hankali taxo kusa dashi ta zauna ya daura hannunsa kan kafadarta.

"Yata fadeelah kin yadda da zabin auren da na miki??"

Daga kai tayi,cikin farin ciki yace

"Dana na aura miki na cikina,kuma ko babu shi ni babanki ne,ki dauke ni amatasyain mahaifi wanda ya haifeki fadeelah,duk abinda kikasan mahaifi yana wa danshi ni zanmiki,kuma duk abinda kikeso kizo wajena kai tasye ni zan miki shi kinji fadeelah"

Kai ta qara dagawa alamar gamsuwa da maganarshi.

Mommah da ummah suna kallonsu cikin farin ciki,yace

"Mubarakh zai tapi da matarshi jibi lahadi,amma ita fadeelah bazata tare ba sai nan gaba,amma zan samu kabeer domin fadeelah zata dawo gidan nn da zama ko ba komai suna da haqqi a kanta"

"Kema zubaida zaki zauna ne a wajen zainab,har asan yadda za'ayi tunda ai baki girma da aure ba"

"Mun gode yaya,Allah ya qara girma"

Mommah ce ta miqe ta qarasa ta janyo hannun fadeelah suka fita,zubaidan ma ta bita suka koma part din momah.

Marriam mayshanu 👌🏻

GAMON JINIWhere stories live. Discover now