GAMON JINI 90 to 95

Start from the beginning
                                    

"Lallai abdul,wai ina ka shiga ne,ni yau kwata kwata ban ganka ba tun safe"

"Ina nan mommah,lapiya lau,dama shawara nazo nema wajenki"

"Toh inajinka,ya akayi??"

"Akan fadeelah ne,dad ya kirani akan maganar skul dinta,kina ganin a kaita skul dinsu rukhy ko kuma a yi mata registration tayi S S C E kawai"

"Toh kai in banda abinka,ai akaita makaranta a ga yanayin karatun nata tukunna,idan xata iya sai a cireta a yi mata registration din,idan kuma bazata iya ba sai ta qarasa daga inda ta tsaya"

"Toh mommah,gobe in shaa Allah zamu je da ita skul din,sai aga yadda za'ayi"

"Toh Allah yasa albarka"

"Amin" shiru yayi tace

"Da wani abun da yake damunka ne??"

"Ba komai" yace sannan ya miqe ya fita daga dakin.

Ta gama dafa mai tea din ne tace rukhy taxo ta rakaata tace ba inda zata iyakaci ta rakata qopar part dinshi ta dawo,hakan kuwa akayi,tana raka ta ta juyo,a hankali ta fara shiga,tsayawa tayi a bakin qofa, ta dan dade a tsaye kafin ta daure ta fara knocking a hankali,jin knockin yayi yace

"Shigo" a hankali ta murda qofar gabanta sai faduwa yake ta shiga,tsayawa tayi ya taso yaxo inda take tsaye ya karbi tray din ya ajiye a kan dressing mirror,ganin ya karbi tea din ta juya zata fita,taku biyu yayi ya qaraso inda take yayi hugging dinta ta baya,qoqarin kwace kanta ta shiga yi amma ta kasa,har gajiya tayi ta haqura shikuwa ajiyar zuciya ya dinga yi lokaci xuwa lokaci,sai da ya gaji don kansa ya saketa,ai yana sakinta dama jira take ta fita da gudu,sai da tazo qofar part din sannan ta tsaya ta daidaita kanta ta shiga don kada ta hadu da wani,sa'a tayi kuwa ba kowa a parlon ta shige daki ta kwanta,rukhy tana mata dariya ta share ta don har yanxu gabanta baibar faduwa ba,tana kwanciya bacci ya kwashe ta.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Washegari tare suka tashi da rukhy ta shirya cikin wata atamfa ja,ba tayi wani make up ba,ta dauko mayafi fari ta yafa,ita kuma rukhy cikin school uniform suka jiyo horn din shi,fitowa sukayi a tare,tun da suka fito ya bita da kallo,gani yai ta mishi kyau sosai har suka qaraso rukhy tayi sauri ta bude baya ta shiga,ganin ba yadda zatayi yasa ta bude gaban ta shiga,tana shiga ta rufe,rukhy ce tace

"Gud mwnin yaya"

"Mornin lil sis"

Duk yana kallonta sukai gaisuwar da rukhy,kanta a qasa tace

"Ina kwana"

"Lapiya lau,amma ki koma ki saka hijabi"Dago idonta tayi yayi rau rau don ba abinda yafi bacin rai irin sai ta shirya ta fito ace ta canxa,tunowa da abinda yamata jiya,gabanta ya fara faduwa,bude qofar tayi ta fita,ba dadewa ta dawo sanye da hijabin da bai wuce gwiwarta ba ta shiga motar suka tafi

School din suka je rukhy ta tapi klas ita kuma suka wuce office din principal,kasancewar ya san abdul yasa ba wani time suka dauka ba,anyi mata interview kuma ba laifi ta dan yi qoqari,hakan ne yasa sukace a mai da ita ss 2 din,abdul ne yai musu bayanin cewar matar aure ce,saboda haka su jawa students dinsu maza kunne don baya son wani abun ya faru,sun tabbatar mishi da cewar basu da matsala da students dinsu,sai kuma hijab din dayace yana son nata ya danfi girma saboda hakan,sun amince sannan sukai sallama,da zummar sai nxt wk monday zata fara zuwa.

"Tare suka fito suka shiga mota,itadai bata ce komai ba,suna hanya ne ya tsaya a wani shopping mall yai parking,fitowa yayi baice mata komai ba ya shiga ciki,bai dade ba ya fito riqe da leda guda biyu a hannunsa,bayan motar ya bude ya sa kayan sannan ya zagaya ya shiga motar suka tafi.suna shiga gida ta bude motar taji a rufe ya sa lock,bata ce komai ba haka nan kuma bata ce ya budeta ba ta dawo ta kwantar da kanta a jikin seat din,duk abinda takeyi akan idonshi

"Fadeelah" ya kira sunanta,ji tayi kamar bata taba jin sunan bama,saboda ji tayi ba wanda ya iya fadar sunan nata kamar shi.

Dagowa tayi ta kalleshi,ba tare da tace komai ba

"Zaki fara zuwa school next week,ina son ki kular min da kanki,kinsan cewar ba kamar kowa kike a makrantar ba don ke matar aure ce" Gyada kai kawai tayi ya ci gaba

"Bana son jin wani abu mara dadi pls"

"Za'a kiyaye,na gode"

"Na fada mki ki daina min godiya,ni mijinki ne kuma haqqinki ne a kaina" Ji tayi maganar tayi mata nauyi kawai ta qara sunkuyar da kanta

"Wannan kunyar taki ta min yawa fadeelah,magana ma baxaki iya tsayawa muyi ba,sai kiyi ta sunkuyar da kai" bata dai ce komai ba kuma ganin bata da niyyar yin magana yasa ya juya ya dauko leda daya a cikin ledojin daya shigo dasu ya bude motar ya fito ya zagayo ya bude mata ta fito suka shiga cikin gidan tare,ba kowa a parlon ta wuce daki,dakin shima ya bita,tana shiga ta juyo ta kalleshi,ledar ya ajiye a gefen gado sannan ya qaraso inda take yayi pecking goshinta ya fita,mutuwar tsaye tayi tana kallonsa har ya fita daga dakin.

Marriam mayshanu 👌🏻

GAMON JINIWhere stories live. Discover now