Babi na 8

1.9K 69 0
                                    

               *****************
Satin Manal daya a Galadanci gidansu Mukhtar, ranar zamu tafi kaita dukanmu, zamuyi sati biyu mu dawo, dama su yaya dukansu basu koma Abuja ba dan hutu suka dauka a wurin aiki, Nasar ma ya tabbatar zeje saboda shima hutun yakeyi.

Mun shirya tsaf dukanmu kowa da yaranshi muka rufe gida aka bar masu gadi kawai.

Su Saratu ma Baba sallamarsu yayi da kudi masu tsoka da kayan abinci yace suje gida suyi sati biyu in ana i gobe zamu dawo se su dawo suyi share share da goge goge.

Yaya Mahmoud da Yusra da su Aida daga can zasu wuce Qatar zasu raka Yusra ganin gida.
Su kuma su Yaya Ahmad da matansu da yaransu zasu wuce Saudi Arabia. Nida Baba ne da Nasar da yara na kawai zamu dawo gida.

'Yan uwan Mukhtar sun raka su Manal, mu kuma Audu ne ya kaimu a jeep din Baba, su Yaya kuma mota daya suma suka shiga za'a barta a airport har mu dawo.

Na hadawa Manal duka kayanta wanda zata tafi dasu tsaf na tafi mata dasu.
Haka muka shiga jirgi muka doshi Canada.

Audu ya maida mota gida shima gobe ze tafi ganin gida, se murna yake Baba ya mishi sallama me tsoka. Masu gadi kawai aka bari aka bar musu kudin abincinsu na sati biyu.

              
                  **************
Mun sauka a Ottawa/MacDonald Cartier international airport, Mukhtar ya samo mana cab muka hau, Baba yace a fara zuwa hotel mu samu masauki, shi ya wuce da matarshi inda zasu zauna. Se da safe in Allah ya kaimu.
Lokacin mun huta se yazo ya daukemu muje muga wuri a san kuma yadda za'a fara mata gyaran gida. Kowa yai na'am da hakan.

Muka sauka a 5star hotel, kowa ya samu dakinshi aka kai kayan mu, Baba ya biya da credit card dinshi, sannan su Mukhtar da Manal sukayi mana sallama suka tafi.

Tun a mota Mukhtar ya fara shafa Manal yana kissing dinta, tana ta nokewa tana jin kunya.
Yace: baby pls allow me. I have been dreaming of hugging this beautiful body and kissing those chubby lips" kar ki hanani dan zaki shiga hakkina dear.
Manal tace: ba hanaka nakeyi ba, naga muna cikin taxi ai ka bari muje gida. And you have to remember am all yours from today till eternity inshaAllah. There are no more limits. Se yace: I love you creamy lips.
Tai smile kawai.

Suna isa gidan suka sauka suka biya me taxi din, ya ajiye musu kayansu sannan Mukhtar ya saka wani card ya bude kofa, suka saka kayansu a lift suka hau 5th floor anan gidansu yake. Ya bude musu kofa suka shiga da kayan na su ciki.
Ta ga gida tsaf kamar da mutum da yake su ba kura ake musu kamar ba mu .
A ranta tace gaskia in hakane Mukhtar nada tsafta. Dakuna uku ne da parlour da kitchen duka manya manya .
Da kujeru da gado a daki daya, sauran dakunan ba kaya a cikinsu. Me gadon suka nufa suka ajiye kayansu, sannan ta nufi toilet dan tayi wanka ko taji dadi.
Shi kuma yace bari nayi mana order abinci a mana home delivery.
Tace toh!

Ta fito daga toilet kenan shi kuma ya rufe kofa ya karbi abincinsu da aka kawo.

Tayi sauri ta rufe kofar ta sa lock wai kar ya ganta da towel, yaita dariya.

Seda ta gama tsaf sannan ta bude ta fito parlour ta zauna akan kujera, lokacin har sallolinta tayi, a wayarta ta duba qibla, saboda tun a airport duk suka sayi layika suka saka a wayoyinsu.
Ya tashi ya wuce ya yi wanka yayi sallolinshi, sannan ya kwala mata kira yace "Manal zo muyi sallah".
Taje ta saka hijabi ta bishi sukayi jam'i sukayi addu'a sosai, ya kama kanta ya dade yana mata addua, bayan ya gama yace Manal kama kaina ki min addua nima ki roki Allah abinda kikeso dani ki kuma nemi kariya daga dukkan fitina ta ko sharrina.
Ta kasa tana jin nauyin taba kanshi dakanshi ya kamo hannunta ya dora akanshi, ita kuma tana ta addu'a a ranta har ta gama, sannan tace na gama. Se yace kafin muci abinci Manal bari mu dan tattauna yadda muke son rayuwar mu ta zama inshaAllah.

❤MAHBUBI❤Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon