Babi na 21

1.4K 67 2
                                    

Da zan shiga gida na goge fuskata saboda kada masu aiki na su gane.

Jamila ta kawo min Aysha, na karbeta muka hau sama. Ina kallon ta ina kuka me karfi ina cewa.
Aysha yanzu zaki dena ganin Babanki.
Zaki dena hawa bayansa kuna wasa.
Watakila ni nayi laifi ya shafeki.
Watakila ma kuma ba laifin nayi ba kawai jarrabawa ce daga ALLAH.
Watakila kuma wani abun nakeyi ba dai dai ba ALLAH ya kamani ta nan.

Na zauna naita tunani ko a halayena akwai wani abun da nakeyi wanda ba dai dai bane, na nutsu na duba sosai na kasa gano wani abun da nake ganin ba daidai nake yinshi ba.
A raina na ce ko na cuci wani ne?
Ko nayi wa wani abinda ba daidai ba?
Nace ko a mutanen da nake mu'amala dasu na sa6a ma wani?

Na dinga rokon ALLAH cikin raina ina cewa YA ALLAH KA dubeni, KA yafe min domin ajizanci irin na dan adam... haka naita addu'a kamar ina hira da wani. Seda naji an turo kofa sannan nayi shiru. Ashe su Hamid ne suka dawo. Sukazo gurina suka zauna. Hamid yace mami me akayi miki? Wataran ya kirani mami wataran kuma maama. Nace ba komai. Habibti ma ta fara tambayata duk idonsu ya ciko da kwalla suna so suyi kuka. Nace musu ku share hawayenku ba komai.

Se Hamid yace mami meyasa aka cire su Ra'is daga islamiyyar mu? Me yasa suka dena zuwa gidanmu su da Babansu? Na rasa me zan ce musu. Se kawai wata dabara ta fado min a raina nace dashi, dama ba anan garin suke ba, wani aiki Baban su yazo amma ya gama aikin ya koma garinsu. Ya so yayi muku sallama kuma yana sauri sanda suka tafi. Amma yace ace kuyi hakuri ze dawo tare dasu Ra'is in sun sake samun dama. Cikin ikon ALLAH se suka yadda da abinda na fada suka hakura. Duk yawan tambayar Hamid se naga ya gamsu.

Nace kuje Jamila ta baku abincin dare kuci, suka tafi da gudu. Na cewa kaina yanzu me mutane zasu daukeni in Adil ya rabu dani? Za'ace ni nake da wani mugun hali shiyasa maza suke min haka.
Za'ace da gaske nice bana son zaman aure, sedai nayi in na haihu kuma na rabu da mijin.
Yanzu in su yaya sukaji me zasu ce?
Na dinga rokar ALLAH ya rufa min sirri na ya kuma daidaita mu inda rabon daidaituwa in kuma Babu ALLAH YA zaba mana mafi alkhairi.
Amma hukuncin da Adil ya yanke a kaina yayi tsari. In laifi nayi masa ya fada min mana akan yayi fushi dani ya dena kula ni haka.

Na ci gaba da zuwa ayyuka na kamar ba abinda yake faruwa. Amma shakuwa da soyayya da kauna sun hanani dena tunanin Adil. Kullum a cikin tunani nake. Inta tunanin good times dinmu ina smiling kamar wata zautacciya.

Rannan nace yanzu duk so da kaunar nan da Adil yake nuna min se ya shareni haka?
Kuma ba ko magana ta rana daya bare na san me nayi?
To ko ni na kashe masa uwa ne?
Naga daga mutuwar maman tashi be kara min magana ba.
Wannan wace irin rayuwa ce?
In naso zuciyata ta manta na shiga harka ta se na kasa. Gaskia so akwai azaba wannan shine 'love sick'
Ace kana ta son mutum shikuma yana can yana sha'aninsa yama manta da kai.

Maza kenan!
Bansan me yasa suke chanzawa a lokaci guda. Kullum se nayi fatan ALLAH ya yaye min wannan masifar dana sami kaina a ciki.

Aysha tayi rashin lafiya har na tsahon sati biyu aka kwantar damu a asibiti saboda bata iya ko shan nono bare ruwa. Ga amai da zawo da takeyi. Se ruwa ake kara mata a kullum. Duk wanda yazo se yace ina Adil se naita yin karya ina cewa yanzu ya fita ko yanzu ze zo. Wasu ma nasan zasu gane karya nake.

Ni kuwa ko fada masa banyi ba ma. Yanzu da ace dashi na laru ya zanyi? In har seya ci dani ko sha dani ko ya min sutura ko kuma ya kaimu asibiti duk ya zanyi? Da tuni se dai inje gida ina roko kenan?

Wannan shine babban rufin asiri. Ni na biya kudin asibitin, nake yin komai base yayi ba ma. Ina ma na ganshi. Shiyasa nake yawan yiwa ubangiji na godiya da ya bani sana'ar yi kuma nake yawan fadawa mata su nemi sana'a ko da basuyi ilimi ba, masu ilimi kuma su nemi aikin yi ko ya yake. Wa'anda basu da ilimi kuma su nemi ilimi inda hali.

❤MAHBUBI❤Where stories live. Discover now