Babi na 30

3K 132 29
                                    

An kawo min kanwar jamila. Maryamu nitsatstsiya me tarbiyya ga haddar qurani a kanta. Naji dadin samunta saboda tana aiki tana karatu ba wasa. Ba wakokin nan da yara 'yan kauye sukeyi in suna aiki. Mun ci gaba da rayuwa tare da ita da A'i.

Manal ta haifi tagwaye maza. Munsha murna. Ta sha dan karen wahala harma su yaya Muhammad da matansu zasuje duba ta. Tana ta kara langwabewa wai karsu fasa.

Haka dai rayuwa taci gaba kullum cikin godiyar ALLAH. Aida ma da Minal sun haihu dukansu sun samu 'yan maza. Aida ce ta fara haihuwa se bayan wata biyu Minal ta haihu. Mijin Minal sunan ya Muhammad yasa shi kuma mijin Aida sunan Babanshi yasa Ahmad amma yayi mana kara yace suna biyu yaron yaci. Kowa yayi ma takwaranshi bajinta iya karfinsa.

Yanzu alhamdulillah dukan mu kowa ya samu madafarsa ya kuma tsaya da kafafunsa. Duk gidajen su na haya suna kawo kudi ana tura musu, ni kuma restaurant dina yana kawo alheri sosai. Wani ina sawa a account din helping hands wani kuma ina kaiwa gidan marayu dan tallafawa da taimako. Se kuma na kara shiga wani kungiya ta taimako, masu zuwa kauyuka suna gina masallatai ana kuma musuluntar da arna da kuma gina boreholes. Amma ni bana binsu. Ina dai tallafawa iyakar iyawa ta.

*****************
BAYAN SHEKARA 15
Yara duk sun girma. Hamid ya gama engeneering a Bayero.
Ra'is da Habibti suna level 3 ita kuma Ra'isa ta shiga level 1.
Aysha ta 'yar lele ta shiga ss1.

Haka muke ta rayuwa cikin kwanciyar hankali.

Ban taba samun matsala da yaran nan a matsayin 'ya'yan miji ba. Ban taba musu iyaka da komai nawa ba. Ban taba nuna musu banbanci ba. Har dakina kan gadona suke shigowa dukansu.
Wataran ma se na bisu na kwakwkwalesu.
Ba inda suke son zuwa. Kullum muna tare in dai ba makaranta.

Duk tafiyar da zamuyi nida babansu tare mukeyi dasu. Ina son yaran, ina jinsu a raina kamar ni na haifesu. Shiyasa kullum Adil shi min albarka yake yana kara kaunata. Duk motsi daya in nayi se Adil ya ce ya akayi tawan? Ina son sunan nan da yake fada min har cikin raina.

Gidan su Adil da ya gada bayan rasuwar Babanshi nasa ya fashe shi an maka wa Ra'is da Ra'isa da Aysha gida. An yima kowa gate dinshi. Kowa kuma sama da kasa ne nashi. Amma na Ra'is yafi girma. Saboda ni a tawa hikimar ina ganin ya kamata kowa inda hali ya mallaki muhalli komin kankantarsa. In Ra'is ze sa mata in yayi aure, su se a sa musu 'yan haya su dinga karbar kudinsu suna hidimar gabansu. Basu dorawa mazajensu nauyin komai ba.

Adil seda ya je ya sai fili a kusa da gidan daga can baya amma da dan tafiya ya ginawa Hamid da Habibti irin gidajen 'ya'yansa sak. Naita fada ina cewa meyasa?
Se yayi min fushi, ya dena min magana kwata kwata.
Kwanan mu biyu a haka, abinda bamu taba yi ba.
In nayi girki ba ya ci, baya rungumeni din daya saba a shekara goma sha da auren mu, baya kulani kwata kwata.
Duk na shiga damuwa.

Rannan ya dawo naje na sameshi a parlour a zaune tare da yara dukansu suna hira suna shewa. Yasa Hamid ya dafa masa tea yana sha. Har wai ya tura su sun siyo masa bread yasa butter yana sha da tea din.
Ina zuwa wurin na zauna yayi shiru ya dena hira.
Adil ya manyanta yanzu, shekararsa 50 ni kuma shekarata 45 yanzu. Shekara biyar ya bani.
Na durkusa a gaban yaran nace Baba(abinda nake kiranshi kenan a gaban yaran mu)kayi hakuri in nayi laifi, ka yafe min dan ALLAH.
se ya kau da kansa gefe, yaki kallona.
Se na fara hawaye, nace dan ALLAH kayi hakuri. Kome na maka ka yafe min, bazan kara ba.
Ra'is ya taso yazo kusa dani yana goge min hawayen sannan shima yace Baba dan ALLAH kayi ma maama hakuri ta dena.
Adil ya bata rai.
Ra'isa ma tayi magana be ce komai ba.
Hamid yace Baba kayi hakuri ka dena fushin dan ALLAH.
Habibti da Aysha ma suka ce Baba kayi hakuri.
Seya kwashe da dariya yace ba ruwanku. Kaji min yara 'yan shishshigi. Me ya kai ku shiga fadan iyayenku?
Suka ce ba zamu iya ganin maman mu kasata tana kuka kaki mata hakuri bane.

Ya tashi ya bisu duka ya kwakwkwade su yace kunci gidanku, 'yan banza.
Duka sukayi dariya.
Ya matso ya kamo hannuna yace zauna akan kujera kiji me zance.
Na zauna duk jikina a sanyaye.
Yace Haba Maama?
Yanzu ace har yanzu bamu zama daya ba?
Duk abinda zan yiwa yaran nan Hamid da Habibti se kin nuna min iyaka ta?
In kuma yarana zan yiwa se ki ta murna kina sani nayi musu ma. Ko ma banga ya dace ba se kin kawo shawarar ayi din. Amma banda su Hamid.
Meyasa?

Bance komai ba amma a zuciyata ina ta tunanin bana son dora masa nauyin da ba nashi ba ne shiyasa. Amma kuma tunda so nake ya dena fushi bani da ikon magana. Ni kuma a ganina ba daidai bane na dora masa nauyin 'ya'yan da bashi ya haifa ba. Kar na kureshi har ya ga haukan yayi yawa.

Yace makarantarsu baki taba bari na biya ba.
Kayansu bakya bari na siya. Kin daukemin harda na yarana.
Asibitinsu da na yarana bama kya bari nasan nawa ne bare na biya.
Kin rike min yarana amana.
Kina kula dasu.
Bakya banbanci tsakaninsu da naki.
Amma ki bari na gina ma yaranki gida se kice bakya so?
Ashe bamu zama daya ba?
Ashe yaranki basu zama nawa ba?

Kawai hawaye suka zubo min. Nace kayi hakuri. InshaAllahu bazan sake ba. Yarana naka ne. Kuma na dena hanaka yi musu abu indai baze wuce kima ba.

Ra'is yana jikina yace haba maama?
Ya zaki banbantamu dasu Hamid?
Mu fa kece uwar mu.
Bamu da 'yan uwan da suka fisu.
Yanda baki ta6a nuna mana banbanci ba haka muma bamu ta6a kallonsu a ba 'yan uwanmu uwa daya uba daya ba.

Nace to duk kuyi hakuri ku yafe min.
Bana so ne na zake da yawa har a fara zagina.

Ra'is yace a zaga mana mu ina ruwanmu da me zagin?
Mutum dai yazo gabanmu ya zageki ne se inda karfinmu ya kare.
Na rungumoshi a jikina. Nace ALLAH ya shiryaka.

Babanshi ya kwadeshi yace tashi min a jikin mata.

Yace kaida kake fushi da ita Baba?
Yana magana yana sosa kai.

Baban ya masa dakuwa yace kaci gidanku.

Adil ya rungumoni jikinsa a gaban yaran, yace musu mamantaku ce ta fiya taurin kai kamar mutanen farko.
Yace sena je can kasar larabawa na auro wata.

Ai kuwa duka suka hada baki sukace wallahi kuwa da mun dauketa mun gudu mun bar maka gidanka.
Ya ce kwaci gidanku kuwa.
Dukanmu mukayi dariya.

Mutumin se kara jana yake jikinsa.
Yace to yanzu kowa zan nuna masa gidansa. Kai Hamid ka nemo mana mata muzo musha biki. Ka gama makaranta inaso ka fara zuwa kasuwa kasan kasuwanci kuma kasan zama da iyali.

Kai kuma Ra'is ga kanwarka nan Habibti da ita zan hada ka.
Ya kwa doka wani tsalle.
Yace kai amma Baba kayi wallahi.
Duk muka zare ido.
Aysha tace dama suna hira a parlour da kitchen in tana dafa masa indomie.
Habibti ta kwadeta.
Nace dena dukar min 'ya kuji da munafircinku.
Baban yace ai na dagosu ne.
Nai ta salati.
Nace ban taba lura ba ai.
Babanshi yace to seka fita da result me kyau. In ba haka ba bazan bata dakiki ba.
Yace a ai dole na dage.
Naji dadin yadda Adil yayi sosai. Saboda ni na reni yaron ni kuma nasan halinshi fiye da kowa. Alhamdulillah ALLAH.

A daki ranar Adil rikice min yayi. Yace haba Amnata? Wai ke ana sonki kina wa mutane fitina.
Naita dariya...
Daya kama lips dina seda naje China.
Adil is the best. I love him so much.
Ranar a harka ko jakhie chan baze nuna mana iya kurda kurda ba. Yanda kasan saurayi da budurwa. Yace ALLAH ya barmin ke Amnata. Nace ALLAH ya barmin kai Adili na.
Na rungumeshi kamar ze gudu ne ya barni shima ya kankameni.
Ji nake kamar na shige cikin jikinsa.
Adil ya ce "i love you baby" acikin kunnena. Kawai wani abu me dadi ya tsirga jikina. Na juya na masa kiss a lips. Nace lips din nan sun cancanci kiss. Yace to a kara min. Na kara masa nace I love you more baby.
Soyayya ta hakika akwai dadi.

Rayuwa muke cikin kwanciyar hankali. Adil ba girman kai. Wataran tare muke cin abinci dukanmu muna hira da yara. In ina kitchen tare suke tayani da babansu. Se yace masu aiki su fita su basu guri duk randa yaso aiki. Yana yi yana dan kissing dina.
In nace yara fa.
Se yace rabu dasu.
Suma se si ta gulmarmu.
In na juya se naga ana nunoni ko ana nuna shi wai gulma suke.

Irin rayuwar da kowa ke fatan samu kenan. Soyaya irin ta Adil, da ita duka maza kema mata da an samu zaman lafiya.
Amma kuma wannan sana'ar da ilimin da hakurin suna taimakawa saboda haka se mun dage. Dan in baka dorawa namiji nauyin abubuwa da yawa se dai ma ka dauke masa wasu duk da kasan yana da karfin yinsu din yana kara ganin girmanka. Kuma muhallin nan yana da amfani. In ma abu ya faru ALLAH ya kiyaye kana iya ce masa kwaahe kayanka kayi gaba.

Mun kawo karshe ❤mahbubi❤ mahbubi na nufin beloved da larabci. Kun ga kuwa ai Adil ya cancanci a kirashi mahbubi.
Duk me miji irin Adilin Amna ta maida masa suna mahbubi.

Taku me kaunar ku a kullum umm khalil❤

❤MAHBUBI❤Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum