Babi na 2

2.9K 95 3
                                    


...da gangar jikina amma za'a rabani dake a lokacin da ban ma gama sanar dake manufar tawa ba. Na shiga daki nayi ihu, nayi kuka, na buga kaina a bango, na kira Allah yafi sau a irga ko ze kawo min dauki. Na je na sami mumma na fada mata tace to Adil me zan ce ai se addu'a. Na kasa fada mata damuwa ta saboda bata bani fuska ba, haka na kara tashi na shiga dakina na rasa me ke min dadi. Se nayi tunanin yanzu baki fara sona ba, baki saba dani ba, baki san ko ni waye ba gara kawai na janye kar na karya miki zuciya kamar yadda tawa ta karye.

Amna, shine na yanke hukuncin dena magana dake na kuma karya sim dina na yar saboda karki nemeni na dauka muzo muyi sabon da zaki tsaneni daga baya. Amma banyi dan rashin so ba. Asali ma son ne ya sa nayi haka a wautata gara nai hurting kaina akan nai hurting zuciyarki not knowing abinda nake tayi kenan. Ki yafe min Amna ta. Ya ci gaba da cewa ban taba zuwa gidan su yarinyar ba, ban taba nemanta ba amma se naga ta fara kirana a waya wai ta gaisheni, se tayo girki ta aiko min harda hotonta. Ban taba cin abincin ba, hoton kuma sena yaga shi saboda bana sonta wallahi bazan iya rayuwar aure da ita ba.
Haka naita rayuwar kunci yau da dadi gobe ba dadi. Sonki kamar ze kashe ni amma bansan ya zan yi ba. Kullum in ina tunanin na hakura se naji tunani ya dawo min sabo inta tuna haduwar mu. Ina ta tuna fararen idanunku, tsayinki madaidaici, cute and pretty face dinki da small and sweet kissable lips dinki. Amna ina sonki ba kadan ba shiyasa na zabi bacin raina akan naki.
Naga baba ya dage shi da gaske yake. Se kawai nake ta tunani ache yarinyar da ko secondary bata gama ba, yarinyar da ko isa batayi na mata kallan kirki ba wai itace  za'a so hadani da ita bama a komai ba se a aure. Na shiga damuwar da ko shigowa gida nayi naji an ambaci sunanta se dai na koma saboda tsananin tsanar da na mata. Haka naita rayuwa ba walwala a tare dani har tsahon wannan shekara guda da 'yan watanni. Har se yanzu da Allah ya sake hadani dake ta tafi.

Se yace dani ya kamata kisan wasu abubuwa a kaina kafin a ci gaba da komai.

Amna ban sanar dake waye ni ba.
Ni sunana Adil sunan babana Alhaji Ibrahim khalil, mutum ne me tsaurin ra'ayi in ya yanke hukunci ba'a isa a tsallaka ba saboda a tsaye yake a gidanshi. Babana mutumin Jigawa ne kuma shahararren dan kasuwa ne. Yana fita kasashen turai ya kawo kaya containers da yawa, yana da shaguna a kwari da sabon gari da wasu garuruwan kamar Abuja, Kaduna da Jigawa. Ya auri mamata anan cikin garin Kano a yakasai ita iyayenta 'yan yakasai ne. Mumma ta sunanta hajia Khadija, tana da mutukar hakuri da kirki, in har kinga fushinta to ta'bata akayi. Ta haifi yara har uku basu zauna ba seda ta haifeni sannan bayan ni tayi har sau biyu auma basu zauna ba amma daga nan bata sake samun ciki ba. Tun tana sha'awa harta hakura ta fauwalawa Allah komai. Ita da Baba sun dauki son duniya sun dora min ba abinda yake tabani, ko qara nayi se sun damu, in banda lafiya kusan dukansu zakiga sun fini chutar ma. Shi kuma babana bame ra'ayin mata biyu bane shiyasa ya zauna da ita har yanzu ba tare da maganar kara aure ba ko sau daya. Ban taba ganin iyayena sunyi sa'insa ba, duk abinda baba yake so mumma ta sani, kuma duk abinda ya fada bata ja ko da ya sa'bawa ra'ayinta shiyasa yake mutukar kaunar ta.

Nayi degree a Bayero university a Comp. Science, naje Egypt nayi mastering degree dina a Al Azhar university, yanzu haka ina PhD dina a Egypt din amma har yanzu ban kai shekara 30 ba da haihuwa. Bana aikin gwamnati sedai ni ne nake kula da dukkan kasuwancin babana a yanzu. Duk wani shigo da kaya da rabasu zuwa inda ya dace ni ne nakeyi. Gidan mu yana nan a Abbas road ta wurin asibitin Nassarawa. Sauran bayanan duk daya kamata ki sani a kaina se a hankali.

A yanzu ina rokarki ki bani dama na shigo rayuwar ki na soki so na hakika Amna, son daba mix, pure love for the sake of Allah. Se na numfasa numfashi har cikin raina amma bansan sanda nace kayi yaya da Kauthar din da kuma maganar iyayenka?
Se yayi dariya yace Amna zancen wannan yarinyar ya gama dan ta sami wani wanda take so har seda akai kacha kacha da ita amma ta dage ita se shi. Maganar da nake miki har an kawo kudinta anyi baiko biki ake jira. Da akayi haka se baba ya kirani yace na fito da duk wadda nakeso ze aura min. Naita nemanki tun last 2 months da abin ya faru ban ganki ba kuma nasha alwashin indai ban ganki ba bazan nemi kowa ba bazan auri kowaba. Shine katsam an gayyaceni dinner ta abokina na ganki. Sanyin idaniyata, masoyiyar zuciyata. Allah ya barmu tare Amna.

❤MAHBUBI❤Where stories live. Discover now