Babi na 7

1.9K 72 2
                                    


Haka muka isa gida muna ta hira na kuma lura yayi missing dinmu sosai amma baze iya fad'a ba.
Muna zuwa gida nayi wanka na sa kayan bacci na sababbi dana siya (na sako a hand bag dita) na shafa turaruka na saboda ina d'an tunanin ko ze nemeni, nayi salloli na sannan naje parlour wurinshi yana zaune.
Na zauna muka ci gaba da hira.
Yace Jamila na gida kamar yadda kika barta kafin ki tafi shiyasa ma ban sa a musu wanka ba har sun yi bacci. Nace ba komai, gobe sena d'akko ta mu gyara gida muyi sauran aikace aikacen mu.

Ina zaune nan ina jiran ko ze rike koda hannuna ne amma yayi biris kamar be damu ba, ko rigar baccin be yaba ba bare insan ko ta masa kyau.

Se na tashi na kai yara daki nace mishi seda safe na tafi na kwanta.
A raina ina ta tunanin in masa magana se naga ma na gaji da yawan yi masa magana akan abu d'aya. Wata zuciyar tace share shi kawai kiyi tafiyarki Allah yana gani ai.

Nayi bacci na isashshe sannan washe gari na tashi da wuri nayi mana breakfast, yara suka tashi na shiryasu tsaf zamu ta fi gida anjima. Seda ya shirya ya fito muka gaisa sannan ya zo muka ci abinci muna ta hira har muka gama ya d'auki yara ya sauka dasu 'kasa ze kaimu gida ni kuma nai sauri na gagygyara na rufe gida na sauka na shiga mota.
Ya kaimu gida, mukayi sallama dashi, yace sena dawo daukanku anjima nace masa to, inma na gama da wuri zansa kawai a kaimu dan ina son yin 'yan gyare gyare na, sannan muka shiga gida shi kuma ya tafi. Na tura su Hamid wurin su Manal ni kuma na wuce wurin aminiyata don nayi missing din hirar mu da fadan mu kwana biyu.

Ina shiga Al'ameen na fara gani yana cin abinci a wurin me aikinsu Hasiya a kitchen kan kujerarshi ita kuma tana zaune akan kujerar kitchen tana bashi yana tayi mata hira. Ya taso da gudu ya rungumeni wai ya ganeni, nace habibi Al'ameen na d'aga shi nayi kissing dinshi a lips da forehead. Ina son yaron, kamar yarana nake jinsa a raina. Nace ina Maaman ka da Abi? Yana gwaranci ya kama hannuna ya ja ni har sama ya kaini har parlourn sama zai jani wurin dakinsu nace a'a, jeka ka kira min su.

Ya shiga da gudu, se gata ta fito tana ta dariya tana cewa ina zuwa, minti d'aya, bari naga waye. Tana 'karasowa ta zo ta rungumeni nima na rungumeta, muka zauna muka fara gaisawa da 'yar hirar mu.

Chan se ya 'kwalo mata kira yace "Maama" tace na'am Abi.. gani nan. Ta tashi ta barni a gurin baki a bude ina kallonta, ta min gwalo ta wuce wurin mijinta.
Seda ya shirya tsaf sannan suka fito tare. Yana zuwa ya talle min kaina yana cewa "kinzo kin janye min mata, ina shiryawa" nace haba yaya? Yau d'aya dai.
Cikin kusan wata biyu ban ganta ba amma yau kawai bazaka iya hakuri ba?

Yana dariya ya mi'ko hannu na mi'ka masa nawa kamar yadda muka saba ya kuwa mtse min hannu har seda nayi ihu sannan ya sake ni. Yayi gaba ya kama hannunta yana cewa muje ki rakani na tafi aiki, ina ta gunguni ya juyo ya kalleni, kafin yai magana nai sauri nace ba dakai na ke ba sannan ya juya tana biye da shi.
Naji tace Abi goyani mu sauka, yace Maama kinyi nauyi fa yanzu.
Se ta fara ta'bara "ni Allah, ni Allah" se ya dur'kusa yace hau to!
Ta hau suka sauka. Tai kissing dinshi tace seka dawo. Sannan ta 'kwalawa Al'ameen kira tace zo kayiwa Abi bye bye.
Ya d'aukeshi suka fice ita kuma ta cewa Hasiya ta kawo mana abin ci da sha. Saboda ita Yusra bata iya karyawa da safe seya fita wai bata son shiga lokacinsa kuma cin abincinta na daukar lokaci.
Amma kuma bata iya cin na rana dana dare se yana nan.

Ta hawo sama ta nemi wuri ta zauna. Ta fara cewa
"Hajia Amna 'yar Babanta, matar Nasar ikon Allah"
Nace "ke ban son iskanci, ko in tashi yanzu inyi tafiyata"
Tace "haba 'kawas yi hakuri wasa nake".

Hasiya ta kawo mana abinci nace bazan ci ba bana jin yunwa.

Ranar munyi hira sosai da yusy kawata kuma 'yar uwata har take fad'a min sun kusa tafiya Qatar se murna takeyi.
Nace mata amma dai zaku jira bayan bikin Manal ko?
Tace aah zamu jira mana. Wane mu mu'ki jira muyi laifi a wurin Baba.

❤MAHBUBI❤Where stories live. Discover now