Babi na 23

1.3K 67 2
                                    

Ranar da kyar na iya samun bacci. Rabin jikina duka ciwo yakeyi. Na rasa me ke min dadi. Baccin da na samu gaf da asuba naita mafarke mafarke marassa dadi. Na tashi a firgice na tsorata sosai. Se kawai na shiga toilet na dauro alwala na zo na dauki Qurani na fara karantawa har akayi kiran sallah. Na tashi nayi nafila sannan nayi sallar asubar.

Ranar banje aiki ba saboda jikina ba dadi yake min ba. Ji na nake kamar marar lafiya. A daddafe nake komai saboda bana so a gane har a san damuwa ta.

Minal ta shirya zata tafi aiki ta zo dakina ta sameni a kwance. Nace mata ta tafi kawai ni yau bana dan jin dadi.

Duk rashin maganar Minal seda tace "yaya Amna dan ALLAH ki rage damuwa. Wallahi duk kin rame kin zuge kamar marar lafiya. Mu muna sonki kuma ba zamu taba barinki ba inshaAllahu. Ki manta komai ki koma rayuwarki ta da".

Ta ce yanzu bani da kowa a garin nan da muke hira ko tattaunawa ko shawara se ke. Ba Yaya Manal ba Aida amma kuma ke bakya ma kulani kuma ke kanki bakya kula kanki bare yaranki, kina sa damuwa a ranki da yawa.

Nayi matukar mamakin yadda Minal tayi hankali haka. Ni har yanzu ban dena mata kallon yarinya ba, ashe ta girma har tayi hankali haka. Se tausayinta ya kama ni. Na tuna bata da uwa se ni amma kullum bana bata lokacin daya kamata na inji ma in ita tana da wata damuwar. Nama manta abinda ya kamata na dinga mata se itace ke kula dani.

Ina kwalla tana share min nace Minal kiyi hakuri kinji? Damuwa ce ta min yawa.
Nace minal Adil.... seda na bata labarin komai sannan na tsaya.

Ta tausayin sosai dan na gani a fuskarta. Amma se tace min,
Ki de dena kuka yaya Amna kiyi hakuri watarana se labari.

Na rungumeta sosai a jikina. Se da aka dade na saketa mukayi sallama ta tafi.

Na fada mata duk damuwata ne saboda kar ta ga kamar son kaina nake da yawa yasa bana damuwa da tata rayuwar. Kuma saboda naga ta girma. Ya kamata su dinga jin irin wadannan abubuwan dan su san akwai babban challenge a gabansu.

Ina nan a kwance ina ta tunani a raina kuma ina ta kallon wayata ina jira tayi ringing amma shiru. Seda na maida hankali wani wajen sannan naji ringing din wayar. Ina dakkota yayana ne yake kira.

Ina dagawa yace Amna gani a gidan su Adil ki maza ki shirya ki sameni nan ba da dadewa ba kinji?

Nace toh. Na kashe wayar. Na shiga wanka, na fito na sa abaya, na sauka kasa na ce dasu Jamila na fita. Aysha na kuka naki daukarta. Saboda bansan me zan tarar ba.

A sanyaye nake tukin motar saboda zuciyata tana ta raya min abubuwa da dama. Ina ta cewa me zanje na tarar?
Ko saki na zeyi?
Ko fada ake da yayana?
Saboda na san yayana bashi da hakuri kwata kwata. Indai an taba ni ko an fadi wani abu da be masa ba ze iya yin fadan dasu.
Nace ALLAH kasa dai lafiya.

Ina isa gidan aka bude min gate na shiga. Jikina duk a sanyaye dan ban ma san inda zan nufa ba. Na fito daga mota kenan naga Ra'is da Ra'isa suna wasa, sukazo da gudu suka rungumeni suna murna suna tsalle. Hawaye yaita gangaro min a kunci ina goge shi sannan na tsugunna a gabansu ina tambayarsu.
Ya kuke?
Suka ce lafiya.
Ya gida?
Sukace lafiya.
Suka fara cewa ina su Hamid?
Nace za'a kaiku gurinsu.
Sukace yau zamu biki.
Nace musu toh.

Na mike na rasa inda zan dosa kuma banga yaya a waje ba. Se na bisu suka kaini parlourn mamansu na zauna. Suna ta min shirme ina basu ansa sama sama ina kuma kallon gidan.

Se a lokacin na lura da kazantar dake jikin 'ya'yan ma. Komai kacha kacha ga wani wari yana fitowa daga wani guri da ban san ina ne ba. Ga shara anyi an tara a wani gefe. Yaran sunci abinci duk an bar plates din anan. Kujerun duk sun yage sunyi yaga yaga.

Ina wani tunani a raina naji wayata ta fara ringing kuma har a lokacin Ummi bata fito ba dama gabana nata faduwa kar inje ta fito ta min wulakanci.

Ina dagawa yaya ne ya ce min wai kina ina ne muna ta jiranki shiru. Nace ina cikin gidan ai parlorn Ummi. Yaya yace yi maza ki fito ki zo parlourn Alhajin su Adil din ga mu nan dukanmu ke ake jira.

Na kira Ra'is na sa ya rakani saboda ba zan gane hanyar ba. Ya ja hannuna ya rakani har kofar parlourn sannan ya sake ni ya koma wasan sa.

Na shiga parlourn suna nan dukansu amma banga Adil ba. Daga Ummi se Babansu Adil se yayana.

Na durkusa na gaishe da baban nasu ya amsa ni.
Nace Ummi ina kwana ta dauke kai ta juya gefe sannan ta ansa ni kasa kasa.

Yayana yace Amna nazo na fadawa Alhaji duk abinda ake ciki da ke da Adil Alhaji yace shi be yadda da haka ba dan shi a gabanshi Adil yake magana dake a waya.

Alhaji ya karba daga nan yace kuma kullum bayan yayi kwana biyu a nan gidan yana zuwa yayi min sallama yace dani ya tafi wajen ki. Kuma ni ban san abinda yake faruwa ba gaskia. Na dai lura itama Ummi duk sanda Adil baya nan a kwana biyun da ba girkin ta ba ne ita ma bata zama. Se na zata wani abun ne suka tsara ni kuma tunda be fada min ba be kuma nemi shawarata ba se ban nemi na sani ba na zuba musu ido.

Saboda naga Adil ba yaro bane da zan ci gaba da bibiyarsa ina sa shi yin abubuwan da baya so. Saboda a da ya min biyayyar ta hakika shiyasa a yanzu bana son takura masa.

Yace a kwanan nan ma seda naga in na shiga harkarsa da Ummi ko yaransa se ta min rashin kunya shi kuma baya ganin laifinta.

Gata nan Ummin tana jin mu. Ya ci gaba da cewa ko Hajia ma kafin ta rasu wallahi ba bakin cikin tsiwa da rashin mutuncin Ummi ta rasu. Shiyasa ma Adil din basa jituwa da ita Ummin amma kuma da yake ita take hanashi daukan mataki se yake hakuri.

To yanzu komai ya canza gaskia. Amma bansan abin ya tabarbare haka ba se yau da Mahmuda yazo yake fada min dukkan abinda yake faruwa.

Yace kiyi hakuri Amna kinji? Bari Adil din ya dawo dan yanzu ze shigo inshaAllahu. Na kirashi a waya yace yana nan tahowa. Mu dan kara yin hakuri mu gani.

Nace to Baba ba komai ALLAH ya dawo dashi lafiya kai kuma ALLAH ya kara maka girma da lafiya da nisan kwana. Yace Amin.

Naita tausayin mutumin. Dan nashi daya amma ace bashi da iko dashi da matar tasa da 'ya'yansa. Gashi ya tsufa sosai yanzu taimako kawai yake nema.

Na dinga cewa ko ya ake bashi abinci ma?
Ko ya ake kula dashi ma?
Naita tunanin kadaicin da ya shiga na rashin matarsa da dansa a lokaci daya. 
Na kuma dinga tunanin to ya akai haka?
Meke faruwa kenan?
Abin ma ya daure min kai na rasa yadda zanyi.

Yayana ma a ransa yana ta tunani ya rasa wannan wane irin bala'i ne.
Ita kuma ummi tana nan ta sunkuyar da kai kasa tana ta wasa da carpet din gurin da yatsunta.

Muna nan a haka a zaune muna jira se yaya yace Alhaji bari na kara kiranshi muji inda yake. Tunda munji shiru har yanzu kuma bamu san ko yana nesa ba ko ya kusa.

Alhaji yace hakan yayi kirashi kaji.
Yayana yana dialing wayar yaji ta tana ringing a cikin parlourn.

Muna jin ringing din dukanmu muka kalli gurin muka ga waya a hannun Ummi.

Bata dago kai ta kallemu ba, yaya yace ina ga a gida ya manta wayar.
Amma kuma ba yanzu Alhaji ya kirashi ba? Se Alhajin yace bari na kara kiranshi. Yana kira Adil din ya dauka yace gani nan yanzu zan karaso.

Se dukanmu mukayi tsuru tsuru muna kallon Ummi. Ni a raina ina tunanin to ya akayi Alhaji ya sameshi yaya kuma da ya kira wayar tayi ringing a hannun ummi?

Alhaji yace wace number ka kira Mahmouda? Yayana yace MTN dinshi. Alhaji yace ai ya dade da dena amfani da ita kwata kwata ya koma Glo nayi nayi ya yi swapping layin nasa amma se ya ce min toh kuma in na kara magana ya kara cewa toh. Nasha ce masa dukkan wadanda suka sanka da layin suka sanka amma se yace ba komai wannan yafi masa dadin amfani.

Gabana ya fadi ra ra ras!!!
Yaya yace ya salam!

Kafin yayi magana Adil ya shigo.
Yana shigowa yace Amna!

Na mike tsaye yadda naga Adil duk ya canza. Nace na'am! Se naga ko kallona beyi ba ya wuce wurin Ummi ya zauna a gefenta ya riko hannunta yana ce mata Amna ta na kama hanyar zuwa gidanki Baba ya kirani ashe kina nan?....

To be continued...
Your votes means a lot❤

❤MAHBUBI❤Where stories live. Discover now