Babi na 13

1.7K 66 0
                                    

A gidan na kwana sunata nan nan dani. Kowa se lallabi yake, amma se nake ta mamakin ba wanda ya min wata maganar. Su Hamid nema suke bawa yara 'yan uwansu labari, munje Dubai da Saudi suna shirmensu na yara.

Ban yiwa kowa tsaraba ba saboda ba tafiyar tsaraba nayi ba, ba kuma a son rai nayi tafiyar ba.

I just needed space to sit quietly and listen to my inner self and that's what I did.

Alhamdulillah!!!

I got all the answers.

Kunsan rashin darajar 'ya mace a al'ummar Bahaushe na maida mu baya sosai, mace na so tayi abubuwa dan jin dadin kanta amma bata isa ba saboda ko ina se ace miji yafi mace, kuma koda yana tauye mata hakki.

Su kuma mazan Hausawa na lura wannan damar ce take saka musu girman kai da mugunta da tauyewa mata hakkinsu. Kuma abin haushin shine ba'a taba gyarawa ko chanzawa.

Ko kasheki yakeyi haka zakiyi hakuri ki ta zama. Haka iyayenmu sukayi, muma haka mukeyi.

Amma ya kamata mu canza kanmu, mu san darajar mu, mu saka so da kauna a gefe mu kwatarwa kanmu 'yancin mu saboda 'ya'yanmu su samu sarari suji dadin rayuwarsu. Haka nake ta yawan tunani a raina.

Allah cikin ikonsa Nasar be ji mun dawo ba har muka kwana uku, su yaya sun gama bikin an kai amarya gidanta.

Washegarin gama bikin da safe wajen 11:30 Yaya Muhammad yasa aka kirani. Ina shiga parlourn Na tarar dasu su uku dukansu a zaune. Muka gaisa, mu ka danyi wasa kadan. Allah sarki 'yan uwa masu dadi. Ina kaunarsu sosai.

Yaya Muhammad yace
"Amna abubuwa da dama sun faru a watanni 7 da suka shude, shine yanzu na kiraki nake son jin abinda yasa kika tafka wannan mummunan kuskuren".
Ya ci gaba Amna kin taba ganin me aure ta bar mijinta be saketa ba tayi tafiyarta da 'ya'yanta?
Kin taba ganin kanwa kuma 'ya da ta ketare iyayenta da yayyanta tai tafiyarta da niyyar kanta saboda wani dalili da ba wanda ta sanarwa?
Ya kike tunanin zamuyi?
Ya kike ganin zamu ji?
Wane tashin hankali kike ganin zamu tsinci kanmu a ciki?
Kinsa mu tunani Amna, mun rasa mutuwa kikayi ko bata kikayi ko kuwa da ranki ne. Wannan aikin shedan ne Amna. Shiyasa ake ce muku mata kuna da karancin tunani. Waya fada miki ita matsala guduwa kake daga gareta dan samin mafita? Ai facing dinta kake, ka nuna mata you are not afraid. Kuma duk abinda mu bamu sama miki mafitarsa ba waye ze sama miki? Mufa ba yayye bane kawai, iyaye ne mu. Kuma koda bani ai akwai Ahmad in kuma ba Ahmad akwai Mahmoud. Karki kara yin irin haka Amna. Da iliminki da saninki.

Ya Ahmad ya dauka daga nan. Shida bashi da yawan magana da hayaniya ma yace "haba kanwata meyasa zakiyi haka?".
Yaci gaba da cewa dan Allah kar ki sake kinji Amna? Wallahi kin samu a tashin hankali.

Yayana ya matso ya dokeni sannan yace 'yar banza. Su yaya sun gama fadan komai yanzu seki fara magana muji me ya sa kika aikata duka wannan shiriritar.

Ina kuka sosai saboda maganar su ta taba min zuciya, sonsu ya karu a raina sosai. Na ce yaya wallahi nasan ban kyauta ba, banyi daidai ba, amma kuyi hakuri, ku yafe min. Bazan kara ba.

Sannan nace yaya tunda mukayi aure da Nasar nake da matsala dashi ban taba fadawa koda mami ba bare Baba amma ina neman alfarma a kirashi sannan muyi dika maganar a gabanshi.

Gajia nai yaya shiyasa na yi wannan tsaurin hukuncin. Amma na gane kuskure na a yafeni. Yaya a min afuwa a kuma yi min alfarmar da na roka.

Yaya yace hakan yayi. Bari zan kira Nasar din da wakilinsa in fada musu se a saka ranar da zata musu, mu hadu anan dukanmu a tattauna.

A washegari an hado kowa, duka an hallara. Mutanen da suka zo wancan meeting din da akayi bana nan din sune dai suka dawo wannan. Kowa yana zaune na shigo na nemi wuri na zauna sannan na gaishesu dukansu.

❤MAHBUBI❤Where stories live. Discover now