Babi na 27

1.4K 63 0
                                    

Bayan yara sun tafi na dawo na kara kwanciya. Aysha taki yadda seda na taho da ita. Ta fara wasa zata hanani bacci na matseta gam na shiga bargo da ita. Taki yadda tana ta mutsul mutsul tana gwalan gwalantunsu na yara. Kawai na kira Jamila a waya nace zoki dauki 'yarki, na fito bakin kofa tazo ta karbeta tana ta dariya. Nace to hutawar da zan danyi ta hanani. Suka sauka kasa ni kuma na koma daki na kwanta.

Bamu muka farka ba se biyun rana. Nayi bacci na gode Allah haka Adil ma yasha bacci ya koshi. Mukayi wanka sannan na fita na nema mana abincin da zamu ci.
A'i nasa ta min su jajjage da yanke yanken duk abubuwan da zanyi amfani.
Na gama hada abinci tsaf, na diba a tray na kai masa sama daki. Yana zaune yana duba wata tsohuwar jarida.

Yace 》 Amna rabon da in karanta jarida na manta.
Nace 》bari na sa a siyo maka seka karanta.
Yace 》toh.

Na zuba masa abinci, yaci da yawa sosai, yasha lemon dana hada masa na kankana da kaninfari da abarba.
Nima na ci nawa, sannan na kira A'i tazo ta sauka da kayan, na mika mata su bakin kofa.

Muna zaune, nace masa Adil ka tashi muje gida ka gaida Baba kuma ku tattauna dan yana son ganinka. Kuma ga yara ma da Ummi sun dade basu ganka ba.
Ban nuna masa akwai wata matsala da Ummi ba, se dai yaji a wani wajen ba ni ba. Ban fada masa bata taba zuwa dubashi ba ko wani abu makamancin haka. Kuma ba na so ya fara min tambayoyi shiyasa na bullo masa ta hakan.

Mun isa gidan a motata ina tukawa, tun daga gate masu gadin suke masa maraba da yake Adil mutumin mutane ne. Muna shiga muka nufi parlourn Alhaji.

Alhaji yana zaune akan kujera yasa gilashi a idonsa yana duba jarida. Muna sallama ya dago ya amsa sannan ya gyara zaman sa sosai. Na gaishe shi, Adil ma ya gaishe shi, ya amsa mu cikin farin ciki da murna. Na tashi zan tafi.

Nace ma Adil 》 ni zan koma gida.
Kafin Adil ya ansa ni se Alhaji yace ba inda zaki, zauna anan. Dake za'ayi dukkan wata maganar da za ayi. Na zauna amma ba dan raina yaso ba. Se nake ga kamar matsalar su ce ni bata shafeni ba. Tunda Adil ya ji sauki suje su karata a can.

Aka kira Ummi ta shigo ta zauna bata gaida kowa ba, bata nuna maraba da ganin mijinta ba, ba kuma ta ce uffan ba, ta zauna ta sunkuyar da kai.

Alhaji ya fara magana, ya yi ma Adil bayanin dukkan abinda ya faru dashi daga farko har karshe wanda ya sani.
Ya kuma ce dani ke Amna fadi naki bangaren labarin. Da na fara jin kunya se kuma kawai na zage na fadi komai da ya faru da yadda akayi yayana yazo gidan. Rashin lafiyar Aysha da wadda nima nayi seda na fada.

Adil banda salati ba abinda yake, ita kuma Ummi sunkuyar da kai kawai take bata dago ta kalli kowa ba.

Alhaji ya kara fada masa dukkan abinda ya sani ya faru a gidan Mal. Junaidu ya kuma fada masa Ummi bata taba zuwa duba shi ba da kuma yadda tun ranar da aka tafi dashi asibitin tasa kafa ta bar gidan se jiya ta dawo.

Alhaji yace ma Ummi banda rashin hankali da shiririta koma me ya faru kya kasa zuwa duba mijinki? Bayan kinaji aka fita dashi a mawuyacin hali. Yace ai kya dawo ki tambayeni ya akayi ko ina yake ma amma da yake baki damu ba se ma kika sa kafa kikai ficewarki.
Ni kuma naga take takenki shiyasa ban ma nemeki ba ban kuma ce miki komai ba. Yace ai wannan rashin tarbiyya ce da rashin hankali. Inma zuga ki ake za kuwa a kaiki a baro ki. Ya kuma ce mata ke baki san wasu masu zuga mutum dan suna masa hassadar rahamar da ALLAH Yayi masa ne yasa suke zuga shi dan ya fita daga cikinta suzo suyi masa dariya.

Adil ya dinga salati ba tsayawa. Abin mamaki kawai yake bashi.
Yace wallahi shi duk be san yayi hakan ba. Yace shi a saninsa be taba kin daga wayata ba ko kuma kin zuwa gidana. Yace kuma ya za ayi ace Aysha bata da lafiya yaki zuwa? Yace wallahi be sani ba. Ya juyo ya kalleni yai ta bani hakuri yana neman gafara ta. Nace masa na yafe maka Adil ba komai. Ya juya gurin mahaifinsa ma ya nemi gafararsa Alhaji ma yace ya yafe mishi.

Alhaji ya fara gindaya masa sharruda. Yace na farko Adil ban yadda ko bayan raina ka cuci yarinyar nan ba.
Na biyu ka riketa rikon amana saboda abinda ta maka ba me iya yi maka shi koma waye. Yace ga uwar gidanka nan ko tunanin neman ba'asin abinda ake ciki bata taba yi ba.
Yace Amna tana sonka so na hakika wanda ba abinda ba zata iya yi maka ba. Ta zauna da kai da aljanunka da kazantarka da rashin lafiyarka bata taba gazawa ba. In ka cuceta daidai da rana daya Allah se ya tambayeka saboda haka ka kula. Kuma addu'a ka dage da yinta. Haka magungunan neman tsarin jiki na ayatush shifa ku dinga yi har 'ya'yanku da Azkar shima safe da yamma.

Adil ya ce inshaAllahu Baba har abada bazan wulakanta Amna ba. Ya kara kallona yace ALLAH yayi miki albarka yasa ki gama da duniya lafiya.

Ya juya kan Ummi yace Ummi bansan me nayi miki dana cancanci irin wannan tsana daga gareki.
Yace nayi zama dake na amana da iya karfina da iya iyawa ta. Duk abinda ya kama daidai gwargwadon iyawa ta ina yi miki, amma da abinda zaki saka min kenan ko?

Yace Amna bata taba sani muzanta miki ba. In ma kika lura tunda tazo na canza mu'amalata dake ta dawo ta tausayawa da kyautatawa, saboda ita take nusar dani take kuma sa ni yin abinda ya kamata. Duk sanda mukai tafiya da ita, ita take sakani koma me kika ga na miki ke da 'ya'yanki kuma tana rike miki 'ya'ya kamar nata, a idona ko bayan idona bata ta6a cutarsu ba dan da tanayi zasu fada ko kuma a ma gane.
Yace yaushe ma take zaman gidan bare ta sami damar cutar yara?
Ya kuma ce mata ni ba wani abun kudi nake mata ba, bata taba tambaya ta ba amma kuma bata taba kyashin sa ni nayi miki ba.
Yace aiki ma take nemar miki a wajen sana'arta kuma bata ma fada min ba saboda a niyyarta sedai an gama komai na sani.
Yace na dawo tana waya bata san naji tana cewa ga a inda take son saki kuma akwai wani course da ake na decoration tana so ta turaki ki koyo amma kika saka mata da haka.
Yace wace iri ce ke?
Me kike nema a duniya?
Yace toh ALLAH yana kallon mu kuma na barki dashi sannan kuma na sake ki Ummi. Saki Uku. Ki tattara kayanki ki tafi amma banda 'ya'yana zan rikesu a gurina. In yaso sa dinga zuwa hutu wurinki inshaAllahu.

Ummi ta fashe da kuka ni kuma jikina duk yayi sanyi ina ta jin ba dadi a gabana ya saki matarsa, uwar gidansa, uwar 'ya'yansa. Alhaji be ce komai ba. Na zata ze masa fadan sakin da yayi mata.
Ummi tana kuka ta fara cewa dan ALLAH ya yafe mata ta san tayi kuskure.
Tace ba zata iya komawa gidansu ta zauna ba.
Ta dinga kuka tana kumawa. Amma ba wanda ya kulata. Duk sun dauke kai kamar ba dasu take magana ba.

Alhaji yace mata ta tashi taje cikin gida. Naita mamaki. Wato in iyaye suka gane baka son 'ya'yansu su ma tsanarka suke. Bare shi Alhaji ma da Adil ne kadai dansa. Yadda naga Alhaji ba ko annuri a fuskarsa in yana kallon ummi se abin ya bani mamaki. Ta fara cewa Alhaji dan ALLAH yayi hakuri ya yafe mata.
Alhaji dan ALLAH yasa Adil ya yafe mata ko dan darajar 'ya'yan data haifa.

Alhaji yace ta tashi ta tafi cikin gida ba ya son jin kuka da magiya a kunnensa. Yace inma an yafe miki ai aure ya kare tunda saki uku akayi miki. Tana kuka ta tashi kafa da jiki duk a sanyaye ta fita.

Alhaji yace ka gani ko?
Mata se su dinga abu ba sa tunanin gaba. Yace ta zata saboda yara za'a hakura a zauna da ita da halinta marar kyau?

A raina nace ni ta ban tausayi amma sanda ta aikata sharrinta batayi tunanin ranar nan zata zo ba. Allah ya shirya mana zuciyar mu.

Alhaji yace ku rike juna amana kunji? Ya kuma ce min ki rike yaran nan da zata bari amana karki banbantasu da naki.

Nace toh, inshaAllahu zanyi iya bakin kokari na.

Yace kai Adil ya kake ji yanzu?
Adil yace na warke bana jin komai.
yace to Alhamdulillah! Mun gode ALLAH da kuma Amna data taimaka maka sosai wajen kulawa da yin magani.

Sukai ta hirarsu wadda suka dade basuyi ba. Suna ta dariya har na gaji ma naji ina son tafiya gida...

Ku biyo mu dan jin ya rayuwa zata kasance a gurin Ummi.
Kuma shin me Ummi ta aikata duk wadan nan abubuwan sukai ta faruwa haka?

❤MAHBUBI❤Where stories live. Discover now