Babi na 17

1.8K 66 0
                                    

Amnan Adil.
Ko ba tashi bace?
Kunya da mamaki a lokaci daya suka hanani magana.
Inata wani smiling dana dade banyi ba a rayuwata.
Nayi wani deep breath da ya shiga har cikin zuciyata.
Nan da nan ta tuno Adil da duka soyayyar da muka sha a baya.

Nace Adil ya kake?

Yace me zaki cemin...

...Bayan na tambayi yaya zan nemeki, ya baki numberta, ya bani taki na kiraki amma kika ki dagawa duk kiran da nake miki.

Na rufe idanuwa na da tafukan hannayena duka biyun.
Nace am sorry love.

Se kuma abinda na fada (love din) ya dawo min a kaina, naji wata masifaffiyar kunya kamar zan nutse.
Yace to lokacin tashi yayi. Tashi ki tafi gida mayi magana a waya.

Nace to. Na tashi nayi gaba ya bini a baya. Nayi ma su Abba sallama na wuce. Seda ya rakani har motata ya bude min kofa na shiga sannan ya rufe min. Na daga masa hannu shima ya dago min, na wuce gida.

ALLAH KARIM
ALLAH RASHID
ALLAH HAKIM
ALLAH AZZA WAJAL
ALLAH WALIY
kalmomin da nai ta fada a raina kenan har na isa gida. Bakina kuwa yaki rufuwa wallahi.
Banda smiling da zancen zuci ba abinda nake.

Hamid yace mami menene naga kina ta jin dadi haka yau?
Nace ba komai zo nan nai kissing dinka.
Na masa kiss a kunchinsa.
Yau ko fadan da nake musu in muna homework banyi ba.
Zuciyata ta cika fam da farin ciki babu gurbin bacin rai a cikinta.

Seda yara sukayi bacci naje kwanciya Adil ya kira ni. Ina dauka yace Tawan?
Naji 'yar kunya, dakyar nace na'am?
Se yace ko ba tawa bace?
Nace ta mami ce gaskia, da Baba da su Manal da su yaya dasu Hamid.
Yayi dariya yace baki canza ba sweetheart. Kina nan yadda na sanki.
Yace na kusa over taking dukansu. Dan dana daukeki se na ga dama ma zan barki ki gansu. Nace tabdi jam.
ALLAH baka isa ba.
Yace haka kika ce ko?
Nace eh!
Yace zamu gani.
Nace naji.

Seda muka gama barkwancinmu da soyayyar mu sannan yace Amna ni fa gaskia da gaske aurenki zanyi. Dan ALLAH ki bani hadin kai. Bana  son wasa, banason bata lokaci. Nida ke ba saurayi da budurwa ne ba. Kin fi kowa sanin hakan. Saboda haka ki bani dama na yima yayanki magana na tura magabatana ayi magana ta sosai asan abin yi.

Nace na amince Adil.

Seda na fada nace karfa ya rainani ko dan jan ajin nan ma banyi ba. Se kuma nace to ni ba yarinya ba, meye na bata lokaci?

Yace nagode Amna sosai ma kuwa.
Mu ka ci gaba da shan hirarmu, mukayi har muka gaji muka yi sallama, muka kwanta.

Ranar bacci yayi matukar yi min dadi.

Na tashi nayi sallar asuba, nayi azhkar na kuma karanta wasu adduo'i'n da Al-Qurani.
Wurin 6:30 na tashi yara muka shiryasu kamar yadda muka saba. Na je na saukesu na dawo na dan kwanta, amma bacci yaki zuwa. Naji son Adil ya cika min zuciyata. Na dinga tunaninshi ina tuno yadda na ganshi kwatsam jiya da ya zo office gurina. Nace Adil be chanza ba ko kadan, da yake jikinshi me kyau ne na fulani. Kawai dai naga ya danyi duhu ne.

Ina kwance inata wannan tunanin ne baccin ya sace ni har seda alarm dina yayi kara na tashi na shiga wanka na shirya, naci abinci na fice.

Ina sauka kafin na shiga mota Yusra ta kirani. Nace "hello yusy".
Tace "Amna kizo akwai labari".
Nace "to mu hadu a restaurant mana".
Tace "a'a gaskia kizo gida".
Nace mata "toh".

Ina isa gida na shige bangarenta. Yaya ya fita. Bamu gaisa ba kama hannuna ta ce muje. Ta nuna min motarta tana tsalle tana murna ya sai mata corolla hadaddiya.

Nai matukar tayata murna. Kuma tace a bata takaddar sallama dan yau zata bude shop dinta na kayan yara. Mukai ta murna muna tsalle.

Sannan tai ta min godiya.

❤MAHBUBI❤Where stories live. Discover now