Babi na 5

2K 79 0
                                    

Baba yace Allah Yai mata albarka Yasa ta gama da duniya lafiya Yasa ku ci gaba dayi mata biyayya Yasa kuma ba zata ga 'bacin rai daga gareku ba har 'karshen rayuwarta.
Ke kuma ki dinga tayata da tarbiyyar su Manal duk da kina da aure amma naga mijinki bame takurawa bane baze hanaki zagayowa akai akai ba. Nace Baba inshaAllahu amma ka dena fadan haka ba inda zakaje ba abinda ze faru.

Haka muka gama hira da baba na koma gurin mami ina bata labarin yadda mukayi tai ta murmushi. Se tabar zancen ma tace min to ke yanzu me kike ganin zamu d'anyi na taryar amarya? Nace mata tunda zakuyi tafiya kuma in kayi tafiya itace da kai dan se yanda Allah yayi ki bar min shirin komai da Verve card dinki a hannu na duk abinda kenan zan shige gaba inshaAllah. Mami tace yauwa Amna Allah Yayi miki albarka nace ameen.

Na tafi da Hamid gida ranar Baban shi na dawowa ya ganshi suka fara tsalle suna murnar ganin juna yana ta yiwa babanshi gwaranci suna dariya. A haka sukaci abinci muka kwanta.

Gashi zamu yi hira, muyi wasa da dariya, zeyi mana komai da muke bu'kata amma ba harkar auratayya a tsakaninmu kuma idan nayi 'korafi se mu fara fad'a. Kawai nace a zuciyata bari in du'kufa addua in barshi da halinshi Allah na kallonmu ai.

Ranar dasu Baba zasu tafi aka daura auren Yayana duk su Yaya Ahmad sunzo.
Naje gida zamuyi sallama na tarar da yayana shima ranar ze tafi Qatar se tsabar zumudi yakeyi.
Nace mami ya naga mutumin haka, Ko airport ze kaiku?
Tace wa? Ai yace shi lallai yau ze tafi tunda an daura aure baze jira ba muka 'kyal'kyale da dariya yana gefe yace min sena talle miki 'keya. Kafin nayi magana Mami tace 'yar tawa zaka daka? Ai baka isa ba. Dukanmu mukayi dariya.

Ranar akayi family pictures da kowa aciki tunda duk muna nan harda Hamid amma ba yaran su ya Muhammad basuzo dasu ba wai se amarya zata tare zasu zo kar zirga zirgar tai yawa.

Dukanmu muka raka su Baba airport da yake jirgin yamma ne mukayi sallama sannan Baba yace ku hada kanku. Muhammadu 'kannenka amana kai kuma Ahmadu dake Amna kusa ido kai kuma Mahmuda ka zauna dasu kamar ni ne acikin gidan. Ka zama babba ka d'au girmanka ka kuma nunawa matarka sonsu in abu ya tsaya maka seka nemi shawarar yayunka da 'kanwarka Amna. Ke kuma Manal yanzu jami'a zaki fara nace a sai miki mota ki dinga zuwa da kanki kina dawowa amma fa ki kula se Minal da Aida ku kula kunji? Allah yayi muku albarka ya hade min kanku. Duk mukace ameen. Mami ta rurrungume mu matan. Baban yai shaking hannu da mazan ya shafa kawunansu suka shiga departures lounge mu kuma muka tafi.
Anan muka bar yayana shima mukayi sallama inata tsokanarsa har seda ya dungurar min cikina nayi 'kara.

Haka muka koma gida mukayi sallama da su yaya Muhammad suka kama hanyar Abuja nima na tafi na barsu Manal su kadai. Wannan karan ba'a dakko kowa ba ance Manal ta kula dasu masu aikin mami su tayata. Na bar mata 'yan kudade a hannunta na tafi.
Da suka isa duk munyi waya sunje lafiya. Yayana ya bani Yusra muka gaisa naita mata tsiya ina jin wani irin dadi a raina sosai da yayana ze auro kawata aminiyata. Can ta bani ya Mahmud din mukayi sallama na kashe waya.

                      ************
Gini ya kankama dan naga kamar jira ake su Baba su tafi a fara shi. Wani yaron Baba ne kuma dan uwanshi mal Habu aka barwa kula da komai da yake yana da amana.
Cikin wata d'aya yadda aka tsara aka kammala gini aka musu gate dinsu akai interlocking wurin 'kasar gaba d'aya. Dama filin bayan kato ne sosai dan har wani karamin garden d'in aka 'kara yi musu akasa kujeru da bukka(rumfa me saman asabari) sannan aka saka 'yan liluna na wasan yara.
An musu gini me sama da 'kasa, 'kasa dika palika ne guda uku amma d'ayan a tsakiya aka yishi wani round shape se abin wanke hannu a cikinshi. Se nata parlourn da nashi shima akwai 'kofa ta baya da za'a iya shigowa nata bayan an d'an hau wasu 'yan benaye guda uku.
Kitchen kuma daga gefen parlours din yake, ta kitchen za'a iya shiga dan circle shape gurin nan, ta parlourn gaba ma za'a iya shiga gurin sannan ta parlourn bayan ma haka se na ce a maida shi dining area kawai.
Parlourn gaba wanda shine na yaya na shima kofa ce me steps din kana shiga corridor ne babba sannan kofa ta glass sannan parlourn nashi.
Se benen daze kai ka sama ta wani corridor da yake tsakanin parlourn baya da parlourn gaba.

❤MAHBUBI❤Where stories live. Discover now